Ticker

6/recent/ticker-posts

Barkwanci Ga Wanzamai: Kwatancin Wakar “Idi Wanzam” Da Labarin Azrael The Barber Na Tawfiq Al-Hakim

Citation: Shu’aibu Hassan (2017). Barkwanci Ga Wanzamai: Kwatancin Waƙar Idi Wanzam Da Labarin Azrael The Barber Na Tawfiƙ Al-Hakim. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 5. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

BARKWANCI GA WANZAMAI: KWATANCIN WAƘAR IDI WANZAM DA LABARIN AZRAEL THE BARBER NA TAWFIƘ AL-HAKIM

Na

Shu’aibu Hassan, PhD

ABSTRACT

Barbers are people who use sharp knives and other tools to cut low or completely shave the hair of their clients. This paper is an attempt to compare barkwanci associated with barbers from two different cultures: Sa’in Makafin Zazzau of Hausa and Azarel the Barber of Arabic Egypt. The paper suggests that why barbers are associated with barkwanci is because of two things: i. the working tools are very sharp hence pose danger to the clients; ii. considering the nature of the tools, the clients are not so safe if the barber happened to be insane and not psychologically balanced. So the society applies barkwanci to some barbers and portrays them as psychos and poses a threat to the clients. The paper compares the nature of the barkwanci done to ‘Idi Wanzam’ of Hausa and that of Azaerel by Tawfiƙ al-Hakim in Egyptian society.

1.0 GABATARWA

Wani lokaci akan ga wasu abubuwa da suka danganci adabi suna kasancewa game-duniya ta yadda za a ga ƃurƃushinsu cikin adabi na alummu daban-daban, da irin kama guda, ko kuma a ga bambancin da bai taka-kara-ya-karya ba. Wannan maƙalar ta ƙyallo wani ɓurɓushi ne na adabi da ya danganci barkwanci da aka yi wa wanzamai a Hausa da kuma wanda aka tsinta daga rubutaccen adabi na Tawfiƙ al-Hakim, adibi daga ƙasar Masar.

Irin barkwanci da aka ga an yi wa wanzamai cikin adabin Hausa da na Tawfiƙ (Larabci) ne yake da ɗaure kai. Misali, me ya sa Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya yi wa Idi Wanzam waƙa ta barkwanci? Me kuma ya sa aka ga wani labari na barkwanci ga Wanzam Azrael da Tawfiƙ al-Hakim ya kawo a rubuce-rubucensa? Amsa waɗannan tambayoyi ya haifar da wannan kwatanci na adabin Larabci da Hausa a kan barkwancin da ake yi wa wanzamai.

Abin mamaki game da waɗannan nau’o’in adabi guda biyu daga mabambanta al’adu, shi ne yadda aka danganta wanzamai da cutar ƙwaƙwalwa, wato motsuwa ko hauka ko dai wani hali na rashin lafiya ta yadda za su kasance barazana ga wanda suke yi wa aski ko gyaran fuska. Sannan in an lura, za a ga barkwanci ne ake yi wa wanzaman domin nishaɗi: a yi raha. Ta fuskar ma’ana, masana suka ce barkwanci wasa ne a cikin zance, wanda zai iya haifar da raha. Barkwanci yakan ɗauki salon ba’a, domin a nuna fifiko ko wata gazawa ta wani ko wasu ko kuma wata ƙabila, domin a yi nishaɗi. An karkasa barkwanci da cewa akwai wadda yake aukuwa tsakanin mutum da ɗan’uwansa, la’alla ta fuskar dangantaka, ko tsakanin masu sana’a, ko tsakanin ƙabilu daban-daban. Duk ana aiwatar da irin wannan barkwanci ne domin a yi wa mutum iya-shege da nufin ƙara danƙon zumunci a tsakani (Zarruƙ, R.M. da wasu, 1987:41).

2.0 SANA’AR WANZANCI

Manazarta sun yi rubuce-rubuce da yawa a kan sana’ar wanzanci da irin gudummuwar da wanzamai suke bayarwa ga al’umma, musamman al’ummar Hausawa. Alal misali, Habib, A. da Musa, U.I. da Zarruƙ, R.M. (1988:58) sun bayyana wanzanci da cewa, Sanaa ce ta yin amfani da aska don aske gashi, da yanke loƃa, da yin tsaga ko ƙaho, saboda rage ƙazanta da neman lafiya da tsare alada. Shi kuwa Sallau (2010) cewa ya yi:

Sana’ar wanzanci tana nufin amfani da askar aski don yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya don cire belun wuya. ana amfani da yar tsaga don yin ƙaho da cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. ana yin hujen kunne da yanke yatsan cindo da yanke linzami a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma, masu yin sanaar wanzanci na bayar da magungunan gargajiya ga waɗanda ke buƙata (Sallau, 2010: 33).

2.1 KAYAN AIKIN SANA’AR WANZANCI

Sana’ar wanzanci ba ta gudana sai da kayayyaki irin su aska, da fatar wasa asake, da dutsen washi da almakashi da kofi da sabulu da ruwa da kalaba da ƙoshiya da hantsaki da yar tsaga da ƙaho da jijiya da sauransu. Akasarin waɗannan kayayyaki ana zuba su ne a cikin zabira, wato wata jaka da ake rataya ta a kafaɗa.

3.0 NAU’O’IN WANZAMAI

Idan aka la’akari da yanayin sana’ar wanzanci, musamman a jiya da yau, za a iya kasa ta zuwa waɗannan rukunai:

Wanzaman Кoƙo:

Wanzaman …:

Masu askin Baba (na zamani): Dalilin kiran su masu askin baba kai tsaye shi ne, idan an lura da aikinsu, ba sa yin wani abu da ya wuce aski. Askin nan zai iya kasancewa saisaye ko ƙwaryar molo ko kuma gyaran fuska. Kayan aikinsu kuma su ne kilifa (clipper) da burushi da isga da ƙyalle (na yafawa a wuyan wanda ake yi masa aski don kar gashi ya ƃata masa jiki) da hodar hana ƙuraje da ruwan maganin sifirit (spirit) da sauran mayuka na ƙawa ko hana ƙurajen gashi. Sannan sai uwa uba, wutar lantaki.

3.1 WANZAMI A MAHANGAR AL’ADA

Wamzami mutum ne mai daraja da muhimmanci a cikin al’adar Hausa, da ma sauran al’ummu saboda irin muhimmancin da sana’ar tasa take da shi. Idan dai aka ce al’umma kamila ce wadda ta fita daga cikin duhun kai na wayewar duniya, ta san yadda za ta suturta jikinta da tsaftace shi, to dole kuwa a ce al’adar wannan al’ummar ta tanaji hanyar da za a gyara suma da duk wani gashi da ke jikin ɗan’adam. Suma da gashi kan kasance abin ƙawa, amma rashin gyara su kuma, kan iya zama ƙazanta. Wanzami aka sani da ɗaukar wannan hidima ta gyaran fuska da duk wasu nau’o’i na aski domin kawar da gashin da ba a buƙata a jiki, in dai bai shafi wuraren da alada ba ta yarje wa wani ya gani ba.

La’akari da wannan matsayi na sana’ar wanzanci da matsayin wanzamai, ya sanya manazarta ke ta ƙoƙarin nuni kan muhimmancin sanaar cikin alumma. Habib da wasu (1988) suka ce, cikin masu sanaoin gargajiya na Hausa, wanzami tamfar likita ne na fiɗa.” Lalle kuwa, domin a yau babu wata al’umma da ba ta san muhimmancin likitan fiɗa ba. In mutum bai yi gamo da abin da zai haɗa shi da likitan fiɗa ba, to lalle ya ji labari daga wajen wani ko wasu.

Malaman sun ci gaba da kawo ire-iren ayyukan da wanzami yake yi, inda suka nuna cewa shi ke yin “aski ƙwal- kwabo ko ƙwaryar molo, da jarfa; wanzami shi yake yin ƙaho, don fitar da mummunan jini daga jikin mutum. Suka ƙara da cewa shi yake yi wa yara kaciya. Bayan haka wanzami ne yake fid da hakin wuya, da haƙorin shuwa, da gurya, da sauran abubuwa irin waɗannan.” Ba su tsaya a nan ba sai da suka nuna cewa wanzami “ke yi wa mutane tsaga da ƙyasƙyastu. Wani lokaci sakiya ma wanzami ne yake yin ta.

Saboda muhimmancin wanzamai ta fuskar al’ada da kuma irin ayyukan da sana’ar tasu ta sanya suke yi, su Habib (1988) sun ci gaba da cewa, “Sarakuna suna kusantar da wanzamai a fadarsu saboda muhimmancin wanzanci. Kuma har suna naɗa musu Sarkin Aska, da Ɗangaladima, daga cikinsu. Ba sarakuna kawai ke ganin ƙimar wanzamai ba, don kuwa jamaa suna ba wanzamai girma, don haka ma duk wani buki da aka yi sai an ware musu nasu rabo ko ba sa nan.

Shi ma ɗan na-gada, wato Sallau (2010), cewa ya yi:

… sana’ar wanzanci ta taƃo aikin likita a ƙasar Hausa kafin zuwan likitan zamani. Dalili kuwa shi ne, wani daga cikin aikin wanzanci shi ne kula da lafiya musamman ta jarirai da ƙananan yara, ta wani fannin ma har da lafiyar manya. Masu yin ire-iren waɗannan ayyuka ana kiransu wanzamai waɗanda dole su kasance masu cikakkiyar lafiya, masu hankali da natsuwa (Sallau, 2010: 34).

Idan aka yi la’akari da yanayin aikin wanzami a tsakanin jama’a, za a iya cewa “ya fi kowa kusanta da jama’a saboda yawan mu’amala da su kuma kasancewarsa tamfar wani maroƙi a tsakaninsu. Har ma ana yi masa kirari da cewa:

Kalakala maganin gizo ɗan wanzam,

Aska na cikin kube tana cin gashi,

Ka wa Sarki rotse ka tashi da girma!

Ɗan wanzam na Sarkin Aski,

Ba ka so ga jikinka. (Habib da wasu, 1988: 59).

3.2 WANZAMI CIKIN ADABI

Idan aka yi dubi da irin kyakkyawan matsayin da wanzami yake da shi cikin al’adu daban-daban na duniya, ciki har da Hausa, sai a ga akasin haka a cikin adabin al’ummu da dama. A cikin adabin, akan ɗan muzanta su ta hanyar yi musu barkwanci, ko nuna su a matsayin masu yawan surutu da shiga sharo ba shanu, cikin harkokin jama’a. Babbar isharar da za mu yi a nan ita ce yadda aka nuna wasu wanzamai guda bakwai cikin shahararren littafin nan mai suna Dare Dubu Da Ɗaya, littafi na ɗaya. Waɗannan wanzamai su ne Wanzamin Bagadaza, wato Shehu Samitu, wanda aka nuna da yawan surutu, da kuma ayyuka irin na motsattsu. Sauran shidan su ne, Baƙaƙu, da Haɗɗaru, da Baƙ-baƙ, da Kuzul Asawati, da Assharu, da kuma Saƙalilu. Waɗannan wanzamai duk an nuna su da wasu halaye na rashin natsuwa, musamman ma shugabansu, wato Samitu (Malumfashi, da Haruna, da Mada, 1, 2015: 287 – 332).

Haka kuma a cikin Magana Jari Ce 2, a labarin “Ba Ruwan Arziki Da Mugun Gashi, Wanda Allah Ya Ba Haƙuri Ya Fi A Zage Shi, mun ga yadda ta kaya da wanzamin Isa Lamiri, wato Shuaibu ɗan wanzam, mai kayan kaifi. A farko dai ba a nuna ɗan wanzam yana da wani taƃin hankali ba, amma daga bisani, sai aka nuna yadda ya birkice, domin ya ga abin da ya faru a kan idonsa, tsakanin Isa Lamiri da Buzu (Imam, 2, 1945: 9 13).  

A littafin Yawon Duniyar Hajji Baba kuwa, ba a taƃa mutuncin wanzami ba, sai ma aka yi ƙoƙarin nuna darajarsa a cikin alumma:

Ubana sunansa Hassan, yana kuwa ɗaya daga cikin wanzamai waɗanda suka shahara a Isfahan. … Amma gwanintarsa ta wanzanci, musamman tsakanin ‘yan kasuwa, ta sa bayan shekara ashirin ya sake auren wata yarinya ‘yar wani mai arziki. Bai sha wata wahala game da auren nan ba, domin ya saba da mai arzikin, kuma shi yake yi masa aski (Tunau, 1966: 1).

A nan, sana’ar wanzancin ta samar wa Hassan Wanzan wata daraja ce, har ya shahara a birnin Isfahan, kuma har ya iya auren ‘yar mai arziki na birnin, kasancewarsa wanzamin mutumin.

Daga cikin rubuce-rubuce na adabi da aka nuna wani hali na barkwanci ga wanzami, akwai na Tawfiƙ al Hakim, wato na Wanzam Azarael, wanda wannan maƙala take aiki a kai.

4.0 BARKWANCI GA WANZAMAI

Sallau (2010: 34) ya tabbatar mana da cewa sana’ar wanzanci ta mutane ne:

… waɗanda dole su kasance masu cikakkiyar lafiya, masu hankali da natsuwa. Makaho ko wanda ba ya gani sosai, ko mai hannu ɗaya, ko kuturu ko mahaukaci ba sa iya yin ayyukan sana’ar wanzanci don tsoron kar a fuskanci matsalar da za ta iya cuta wa waɗanda za a yi wa ayyukan.

Idan aka yi la’akari da abin da Sallau ya faɗi a nan a kan su waye ya dace su yi sana’ar wanzaci, to za a ga babu makaho a ciki. Bisa ala’ada, an san da karin maganar nan da ke cewa, ‘haushin rashi, makaho ya ce ido da ɗoyi.’ In kuwa haka ne, ashe ba abin mamaki ba ne a ji makaho yana yi wa wanzami iya shege domin ya san sana’a ce da ta gagare shi. Wannan hanzari ba gudu ba ake gani ya sanya Sa’in Makafin Zazzau ya yi waƙar Idi Wanzam. Bisa alada, ba a taɓa jin cewa akwai wani dalili da ya haifar da wasan barkwanci tsakanin wanzamai da makafi ba, kamar yadda aka sani tsakanin wasu masu sana’a kamar a ce malami da maharbi, ko ɗan bankwai da barinde, ko maƙeri da wanzami da ire-irensu.

Wani hasashen da ake da shi a kan wannan barkwanci da ake yi wa wanzamai shi ne la’akari da aka yi da irin yanayin kayan aikinsa, da kuma yadda duk mai son ya yi masa aski ko gyaran fuska, yake miƙa masa kansa gaba ɗaya. Mutum ya miƙa kansa ga mutumin da yake ɗauke da makami (aska) mai kaifin tsiya, ya sanya ta a wuyansa da kunnensa da hancinsa da tsakar kansa, ai abin dubawa ne. Wannan dalili ne kuwa ya sanya dole mai irin wannan sana’a ya kasance mai cikakken hankali da natsuwa. Rashin ɗayan waɗannan zai iya zama ɓarna. Waɗannan abubuwa biyu muhimmai, su ne Azarael Wanzam da Idi Wanzam suka rasa daga labarin Tawfiƙ da kuma waƙar Salisu Sai.

5.1 WAƘAR IDI WANZAM

Karofi (1980) ya bayyana cewa Malam Salisu ya shara sosai a ƙasar nan a kan basirar tsara waƙar bara. Salisu ya nuna cewa yana da yara makafi da dama da ya koya wa waƙar bara, musamman sannanun waƙoƙin nan irin su, Waƙar Wulli da Makahon Direba da Waƙar Idi Wanzam. Kaɗan daga cikin yaran da Salisu Makaho ya koya wa waƙa su ne, Malam Ibrahim Kunkunna da Malam Iro Ibrahim Sakkwato da Malam Audu Sakkwato. Wannan ƙwarewa ta Salisu Makaho ne ta kai har ya sami sarautar Sain Makafin Zazzau da Kaduna (Karofi, 1980: 160 162).

Wannan waƙa ta Idi Wanzam, shahararriya ce a bakin makafi, amma an fi danganta ta da Salisu Makaho, Sain Makafin Zazzau, domin shi ne aka tabbatar maƙirƙirin wannan waƙa. Baya ga yadda aka zayyana wanzami cikin rubuce-rubuce daban-daban na adabi, a cikin adabin baka ma, musamman na Hausa, an ga kuma yadda Salisu Makaho ya ƙirƙiri wannan waƙa, ya danganta ta da wani wanzami wai shi Idi Wanzam, na Kwanar Gagawa. Waƙar cike take da barkwanci domin raha ga shi wannan wanzami mai suna Idi Wanzam. Bayan Salisu Sa’i, makafi da dama sun kwaikwaye shi, inda suke rerawa lokacin da suke yawon bara.

Haka ma makaɗan zamani, masu amfani da kayan kiɗa irin su fiyano, ba a bar su a baya ba wajen kwaikwayo, tare da rera wannan shahararriyar waƙa. Fitaccen mawaƙin fiyon nan, wato Sadi Sidi Sharifai, shi ma ya kwaikwayi wannan waƙa, inda ya rera da muryar fitaccen ɗan wasan kwaikwayon nan, wato Rabilu Musa ɗan Ibro.

5.2 LABARIN AZRAEL WANZAM A TAƘAICE

Mutuwa kan iya riskar mutum a kowane lokaci: yana sane ko ba ya sane. Akan yi wasan ƃuya da mutuwa, mutum kan iya kuƃuta, ko ya faɗa tarkonta. Mutuwa kan ce “Na gan ka, na kuma san inda ka ƃoye. Rayuwarmu ta yanadam cike take da barazana, wasu ba mu ma san da su ba: wasu sanadinsu ƙuda, wasu cizon sauro, wasu sanadinsu hatsarin mota, ko jirgin ƙasa ko na sama. Mutum bai sani ba ma, kila sanadin mutuwarsa tana hannun wanzaminsa da ke yi masa aski, ko gyaran fuska, hatsarin da sam mutum ba ya zaton zai iya faruwa.

A farkon bazara na tafi shagon wanzami domin ya yi mini gyaran fuska. Ina cike da buri na rayuwa, har wata ‘yar waƙa na ke yi a zuciyata. Ina tafe ina jin sautin waƙar manoma lokacin da suke kora raƙumansu ɗauke da kayan kankana suna ratsa kyawawan titunan birnin Cairo. Na faɗa cikin kujerar wanzam, na miƙa masa kaina, na lunshe idona, kamar mai mafarkin jin daɗi, ga fanka tana busa ni. Lokacin da wanzamin ya ɗaga haƃata, sai na ji wata natsuwa. Daga nan ya wasa askarsa da fatar wasa asake, har ta fara sheƙi.

Da ya dafa kaina, sai ya yi mini magana cikin wata murya mai ban ta’ajibi, ya ce, “Ina fata ba za ka damu ba in na ce tun ɗazu da ka shigo nake lura da kai, kuma zuciyata ba ta yi mini ƙarya. Ina da wata yar buƙata a gare ka.

Ya ɗaga askar daga goshina, amsa masa da cewa, “Ina sauraronka.”

Ya kama kaina ya fara aski, ya ce, “Maigida, ko ka san wani a asibitin mahaukata?”

Na yi mamaki, amma sai na daure, na ce, “Idan zuciyarka da ba ta ƙarya ita ta raya maka haka bayan ka nazarce ni, to ba ni wata alaƙa da wannan asibitin, na gode.

Sai ya ce, “Ka yi haƙuri, ba haka nake nufi ba. Ina nufin cewa nazarina ya nuna mini kai mutum ne mai daraja da kila ko ka san wani likita a asibitin.

Na ce, “Me ya sa?”

Ya ce, “Ina da wani ɗan’uwa mahaukaci ne a can da nake so a sake shi.”

“Mahaukaci? Ya warke ne?”

“Haukar ba mai tsanani ba ce. Asibitin sun yi masa sharri ne. Haka suke yi a kullum sukan tsare mutune bisa kuskure. Abin dake damunsa daga lokaci zuwa lokaci shi ne yana da wata matsala ce da take sanya wa ya riƙa rayawa a ransa aikata wasu abubuwa marasa hatsari. Amma bai taƃa aikata wata ƃarna ba. Bai taƃa aikata wani abu da mahaukata ke yi da har ta kai a tsare shi a asibitin ba.

Na ce, “Abin mamaki! To me ya sa har aka tsare shi a asibitin?”

“Ba wani dalili, yallaƃai. Matsalar mai sauƙi ce: ɗan’uwan nan nawa shi ma wanzami ne kamar ni. Yana aiki wata rana, lafiyarsa lau, to lokacin zafi ne, ka kuma san cewa yanayin kan sanya mutane jin ƙishi. Yana cikin yi wa wani aski, kamar kai ɗin nan, sai tunaninsa ya raya masa cewa kan wanda yake yi wa askin nan ya yi kama da kankana. Yana riƙe da aska a hannunsa, sai ya ji kamar ya tsaga kan mutumin nan.

Ai sai nan da nan na yi kuwwa, na ce, “Ya tsaga me?”

Cikin tattausan lafazi, ba tare da wata damuwa ba, wanzamin nawa ya ce, “Ya tsaga kankanar ... Ina nufin kan mutumin.”  

Sai na ji lakata ta sake. A lokacin kaina yana hannunsa, yana aske ƙasan haƃata, can wajen wuya, ina ganin sheƙin askar tasa. Sai na ji numfashina ya ɗauke. Nan fa sai na yi ta maza, hankalina ya dawo, cikin natsuwa, na ce “Lalle wannan ɗan’uwa naka ya zama zakka a cikin danginku ...”

Ya karkato da rezar kan maƙoshina, cikin natsuwa, ya ce, Gaskiyar lamari game da danginmu shi ne, duk haka muke. Ni kaina wani lokaci nakan raya wasu abubuwan ban mamaki a zuciyata, musamman lokacin kakar kankana. Ina mai tabbatar maka cewa ɗan’uwan nan nawa ba shi da laifi.”

Sai na ga wani haske kamar na aska ya nufi maƙoshina, har yana haska fuskar wanzamin. Na ce shike nan na mutu, sai na fara addua, na roƙi Allah ya kuƃutar da ni.

Sai na sadaukar kawai, na rufe idona – babu nishaɗi a wannan lokacin – ina jiran mutuwata kawai. Ban sake buɗe idona ba sai da na ji yana yayyafa mini turare a fuskata, yana cewa, “Na yi maka barka.”

Na tashi na karkaɗe jikina, na ji ni kamar wani sabon zuwa duniya. Na biya shi, na yi waje. Na ji yana kira a bayana, yana tunatar da ni batun ɗan’uwan nasa kan yadda za a sake shi. Ban ko kula shi ba. Da na fito kan layi, sai na ja wani dogon numfashi, na rantse cewa in dai lokacin kakar kankana ne, to ni zan yi wa kaina aski, ko kuma dai ba zan sake zuwa aski wurin wannan wanzami ba. (al-Hakim, 2008: 221 – 223).

A wannan labari na Azrael Wanzam, za mu ga cewa an danganta shi wannan wanzamin da ciwon hauka wanda ya sanya mutumin da ya a je aski shagonsa shiga wani matsancin hali. Za mu iya cewa Allah ne kawai ya cece shi daga ciwon haukar Azrael don kaɗan ya rage ya tsaga masa kai, kamar yadda ake tsaga kankana. Wannan ya tabbatar cewa sana’ar wanzanci ta masu cikakken hankali ce, ba ta motsattsu ko mahaukata tuburan ba. Tawfiƙ ya yi wa Azarael barkwanci ne ƙila saboda yanayin kayan aikin sanaar wanzanci, wato asake masu kaifin tsiya waɗanda za su iya cutarwa. Bayan haka kuma, an san yadda mutum kan miƙa kansa baki ɗaya ga wanzami yayin aski, wanda in har rana za ta ƃaci, to fa ba tsimi ba tanadi, sai dai gyaran Allah. A taƙaice dai, sanaar ta masu hankali ce da natsuwa, kamar yadda Sallau (2010) ya nuna, ba ta irin su Azrael da Idi Wanzam ba.

6.0 “IDI WANZAM” DAGA BAKIN SALISU MAKAHO, SA’IN MAKAFIN ZAZZAU

Idi Wanzam, kamar yadda Salisu Sa’i ya nuna mana a waƙe, mahakaci ne tuburan. Za mu iya tabbatar da hakan daga cikin abubuwan da mawaƙin ya faɗi daga cikin ɗiyoyin waƙar tasa da dama. A lokacin da Makaho ya nemi ko akwai wanzami a garin:

Da na sauka garin Gagawa,

Na ce jama’ar Gagawa,

Zan yi tambaya a gare ku,

Tambayata da wanzami a garin nan?

Sai suka ce ‘To Malam,

‘Da wanzami a garin nan’.

Sai na ce ku kai ni wurinsa,

Don kuwa ina son aski,

Sannan ai mini gyaran fuska.

Jin haka, sai jama’ar Gagawa sai suka gargaɗi Malam Makaho da cewa:

Shi wannan wanzamin,

Mu ma da ka gan mu ‘yan garin nan,

Muna tsoronsa.

Wannan tsoro da suke ji na Idi Wanzam ya nuna lallai da walakin: ko dai mafaɗaci ne, ko kuma motsattse ne. ilai kuwa, ta tabbata motsattsen ne.

Dalilai da dama suka tabbatar mana cewa Idi Wanzam motsattse ne. Na farko shi ne sunayen asakensa:

Askarsa guda huɗu, kowace aska ga sunanta:

Ɗaya ‘Kura kya ci da gashi’,

Ɗaya ‘Ladanki na jikinki’,

Akwai wata ‘Wa aka samu?’,

Sannan ga ‘Кare dangi’.

Amma ita ‘Кare dangi’,

Idan ta fito daga sanho,

Rannan mutum dubu sa ƙare.

Sannan amfani da sanho maimakon zabira domin adana asaken:

Wai wanzaman kiriki,

Suna yawo da zabira,

Idi Wanzam, shi sai ya zubo askarsa a sanho.

Sannan shi Idi Wanzam wai yana wasa aska a dutsen niƙa maimakon mawashi na fata ko dutsen ƙanƙara:

Haba ‘yan amshi!

Wanzaman kirki,

Kowa yana da mawashin aska,

Idi Wanzam da dutsen niƙa yake wasawa,

Na Kwanar Gagawa,

Ko kuwa ya sami bulo na siminti.

A tsarin likitanci na gargajiya akan yi ƙaho. Wajen yin ƙaho, akan yi amfani da wani gyararren ƙaho ne na dabba domin a zuƙo mataccen jini. Shi mataccen jini ana samunsa ne a wurin da mutum ya ƙume, ko ya yi targaɗe da ire-irensu. To shi Idi Wanzam maimakon ya yi amfani da ƙaho bisa alada, yana amfani fafaffiyar garwa ce:

Subhanallahi!

Sannan wanzaman kirki,

Suna yawo da ƙaho,

Idi Wanzam, bakin garwa aka fafe,

Majajjawa ita ce ‘yar kamu.

Ire-iren waɗannan halaye duk suna nuni da cewa lallai Idi Wanzam motsattse ne. Yaya za a ce asaken da yake yi wa mutane aski a ce har suna da sunaye na musamman, kuma sunayen ma da ji salonsu ya nuna cewa masu shirin shan jini ne.

Wani tuntuƃe gushin gaba domin a tabbatar wa Malam Makaho cewa lallai Idi Wanzam motsattse ne, shi ne yadda ya ƙi amsa sallamar da ya yi masa. A maimakon ma ya amsa masa sallamar, sai ya daka masa tsawa:

Aka kai ni gidan wanzami,

To da na je gidan,

Na yi sallama na ƙara,

Na sake sallama na ƙara,

Ya yi shiru ya ƙyale.

To Idi Wanzami,

To daga can da ya motsa,

Sai ya daka mini tsawa!

Ran nan da na ruɗe,

Har igiyar wandona ta tsinke,

‘Yan amshi suka tsorata,

Kan a jima sun kai Ɗanbatta,

Suka bar mu muna ta adanja.

Mutumin da za a yi masa sallama, kuma yana ɗan Musulmi ya ƙi amsawa, a maimakon haka ma sai ya daka tsawa ga mai yi masa sallamar, ai an san lallai bai da lafiyar ƙwaƙwalwa sosai.

Haka kuma wata yarinya da ta tarar da Malam Makaho yana jira a azure, ta ƙara tabbatar da motsuwar Idi Wanzam, inda ta shawarci Makaho da ya kama gabansa:

Ka ji ina nan zaune,

Daga nan sai ga yarinya,

Ta ce, ‘Salamu alaikum,

Albishirinka Makaho,

Zan yi tambaya a gare ka.’

Subuhanallahi!

‘Wai me kake nema a gidan nan’?

Na ce, ‘Yarinya ai na zo ne ai mini aski’.

Ta ce, ‘Wa zai maka aski’?

Na ce, ‘Idi Wanzami’.

Sai na ji ta yi salati,

Ta ce ‘La’ilaha Illallahu, kai dai baƙo ne a garin nan!

In kai baƙo ne,

Tashi in sa ka a hanya kan Idi ya fito a gidan nan.’

Wani babban lamari kuma da ya gudana tsakanin Malam Makaho da Idi Wanzam, da yake ƙara tabbatar da nuni a kan motsuwar hankalinsa, shi ne na irin shirin da aka yi domin yin askin:

Ya ce, ‘To, tsaya Makaho, ni askina sai an shirya’.

Na ce, ‘Shirin me za a yi tun da dai na ba ka kirari’?

…………………………………………………….,

Idi Wanzami, sai ya fito a gidansa,

Ya nemi ƙato goma,

Suka je suka samo dirka,

Nan suka zo suka jibge,

Ga igiya a gabansa,

Ita ma kamu saba’in ne,

Ya sa an haƙa rami,

Rami gaba bakwai aka tona,

Na ce, ‘Wanzami, duk wannan ramin mene ne?’

Lallai irin wannan aski na Idi Wanzam sai an shirya. A ce za a yi aski sai an saro dirka, kamar za a kafa rumfa? Sannan ga igiya har kamu saba’in tare da haƙa rami gaba bakwai? Wannan ai ko raƙumi za a yanka iyaka ke nan.

7.0 KWATANCI

Idan aka lura da waɗannan wanzamai guda biyu, za mu ga shi Azrael yana da ciwon hauka ne na gado, amma ba lalle ne a gane hakan ba domin ba koyaushe haukar take tashi ba. Ba domin wannan irin tattaunawa da ta faru tsakaninsa da wannan da ya yi wa aski ba, da ba za a san da haukar tasa ba ma. Amma shi Idi Wanzam haukarsa a bayyane take ga ‘yan garinsu da kuma sauran iyalansa ma. Kowa a garin ya san shi da cewa mahaukaci ne.

Haukar Azrael ba ta tashi sai da kaka ko lokacin bazara, lokacin da ake fama da ƙishi saboda zafi. Kuma a daidai wannan lokacin ne kakar kankana. Saboda haka duk wani mai jin ƙishi yakan so ya sami kankana ya sha. Wannan yanayin yakan sa Azarael ya ji kamar ya tsaga kan wanda yake wa aski da nufin cewa kankana ce. Amma ita haukar Idi Wanzam hauka ce da ta ƙunshi tun daga kayan aikinsa zuwa halayyarsa da muamalarsa. A taƙaice dai Idi Wanzam mahaukaci ne tuburan.

8.0 KAMMALAWA

Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin nuna cewa barkwanci bai tsaya a tsakanin masu sanaa a junasu ko tsakanin wasu ƙabilu ba. Akan ga jamaa suna yi wa wata nauin sanaa ko masu aiwatar da sanaar saboda wani dalili, amma ba domin suna aiwatar da sanaa kishiyar ɗayar ba. Wannan kuwa shi ya faru a kan wanzamai kamar yadda muka gani.

Maƙalar ta nuna cewa kila saboda muamala da wanzami yake yi da kayan kaifi irin su aska da ƙaho, ga shi kuma riƙe da kan mutum da wuyansa da duk dai inda in har rana ta ɓaci, zai iya kai mutum ƙiyama lokaci ƙanƙane, shi ya sa ake yi masa wannan irin barkwanci.

Maƙalar ta nuna cewa irin barkwancin da ake yi wa wanzamai ba a ƙasar Hausa kawai ake yi ba, har da ma ƙasashen Larabawa, kamar Masar da kuma sauran wurare. Wasu suna ganin cewa in kana neman labarin gari, to ka tambayi wanzami. Kila wannan magana ba ta zama sharri ba.

Manazarta

Habib, A, Musa, U.I, da Zarruƙ, R.M. (1988). Zaman Hausawa, bugu na biyu. Lagos: Islamic Publications Bureau.

Ibrahim, U. (2011). “Tasirin Haye a Sana’o’in Hausawa na Gargajiya.” Kundin Digiri na Tsakiya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Johnson-Daɓies, D. (Ed.) (2008). The Essential Tawfiƙ al-Hakim, play, fiction, autobiography. Cairo: the American University in Cairo Press.

Karofi, D.S. (1980). “Mabarata: Nazarinsu da Gudunmuwarsu a kan Adabin Hausa.” Digirin Farko, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

Sallau, B.A.S. (2000). “Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Кasar Hausa.” Kundin Digiri na Tsakiya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B.A.S. (2009). “Sana’ar Wanzanci da Sauye-sauyen Zamani Jiya da Yau.” Kundin Digiri na Кoli. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B.A.S. (2010). Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: M.A. Najiu Professional Printers.

Sallau, B.A.S. (2013). Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Sallau, B.A.S. (2009). Maganai a Sha a Yi Wanka a Buwaya. Kaduna: M.A. Najiu Professional Printers.

Yobe Journal - Volume 5 

Post a Comment

0 Comments