Ticker

6/recent/ticker-posts

Adalci Tsakanin Mace Diyar Talaka Da Diyar Mai Kuɗi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ina da mata biyu, ɗiyar talaka da ɗiyar mai kuɗi, shin ya halatta na yiwa ɗiyar talaka tufafi masu araha, ita kuma ɗiyar mai kuɗi na yi mata masu tsada?

ADALCI TSAKANIN MACE ƊIYAR TALAKA DA ƊIYAR MAI KUƊI

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Akwai hujjoji daga Alƙurani mai girma da Hadisai ingantattu da magan-ganun malamai akan wajabcin Miji yaciyar da Matansa, wannan kuma ya biyo bayan gwar-gwado dama da ikon da yake da ita. Kuma ba ya yiwuwa ya barta ta ciyar da kanta ko da kuwa mawadaciya ce, sai dai idan da yardarta akan za ta ciyar da kanta.

Kuma wannan ciyarwar da za a yiwa mace daga ciki akwai tufatar da ita, lokacin sanyi da zafi, bawai sai kowacce shekara ba, da kowane biki ba, a'a zai yishi ne ko da kuwa tana da tufafin, ba maganar sai ya ga tufafinta sun lalace, sannan ya yi mata ɗinki, A'a tufatarwa na kasancewa ne gwar-gwadon buƙatar matarsa ga tufafin kuma gwargwadon karfi/ikonsa, ba tare da kuma ya yi fifita wata akan wata ba, 'yar Masu kuɗi da 'yar talaka, lura da Alƙur'ani mai girma cewa hakan zai kasance ne da kyautatawa kuma gwar-gwadon Wadatarsa:

 ۚ وَعَلَى الْمَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ لَا تُكَلَّفُ نَفْسٌ إِلَّا وُسْعَهَا ۚ

"Wajibi ne akan wanda ake yiwa haihuwa (miji) ciyarda Matansa da tufatar dasu bisa kyautatawa, Bamu kallafawa rai sai abin da za ta iya" (Suratul Baƙara:233.)

Ibn Kaseer Allah ya yi masa rahma ya ce: "Ana nufin ciyar dasu irin abin da al'adar mutanen gari take cewa shi ne Abin da ake ciyar damata da shi gwar-gwadon arzikinsa garinsu ke tafiya akan shi, ba tare da bannatar da dukiya ko noketa, gwar-gwadon dai samunsa da wadatarsa"Tafseer Ibn Kaseer (1/634)

Anan abin da ya fi zama maslaha shi ne ko wace ya siya mata irin abin da ya siyawa ɗayar gwar-gwadon arzikinsa.

Domin Adalci Allah ya ce Ayi, matsayin su ɗaya awajanka kowacce matarkace, kasonsu ɗaya a cikin gadon dukiyarka ko da kuwa Ubantane ya fi kowa wadata aduniya, inka mutu da ita da wacce Ubanta ya fi kowa talauci aduniya ɗaya suke wajan Allah saboda haka nema yaraba gadonsu dai-dai babu ban-banci idan kamutu.

Bai hlatta ka yi wannan Shaiɗanci tsakanin Matankaba, kuma lallai kasani yin hakan kunna wata gobarar dajice agidanka wanda bakasan iyakacin ɓarnar dazatai a cikin gidanka da zurriyarka baki ɗaya ba.

Maganace Mummuna kuma ko da kaji koka karanta awani waje cewa hakan yahalatta, katabbar kuskurece, ta saɓawa Ayoyin Alƙur'ani da hadisan Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam da tunani mai kyau.

Wajibi ne katsayar da adalci tsakanin matanka, haramunne kafifita wata akan wata, wajan tufafi ko kayan kwalliya ko yana yin irin Abuncin dakake ciyar dasu.

Wajibi ne kadunga yi musu tufafi masu kima ɗaya daraja ɗaya, haka abunci haka wajan kwanciya haka gida dole kabaiwa kowacce dai-dai da ɗayar.

Inka sayawa ɗiyar masu kuɗi tufafin dubu biyar, wajibi ne ɗiyar talakama kasai mata tufafi mai darajar datakai dubu biyar, balalle suzama kala ɗaya ba, amma darajarsu da tsadarsu dolene suzamto dai-dai.

Waccan in kullum kana saimata lemuka da nama da dukkan wani Nau'in Abunci mai kyau kona Sha, ɗayar ma wajibin kane kadunga sai mata irin wannan abunci mai daraja iri ɗaya da kuma karin kuzari da inganta jiki irin wacce kasaiwa ɗiyar masu kuɗin da ka auro.

Haka in kabaiwa ɗaya gida mai dakuna uku da firji da setlight da kayan kawa, itama ɗayar dolene kasai mata gida irin na ɗayar maicike dakayan kawa da more rayuwa irin na ɗayar babu ban-banci.

Wannan shi ne zai tseratar dakai agaban Allah rannar Alkiyama daka shiga wuta.

Bayan haka yana daga abin da ya fi zama maslaha yayin da mutum zai yi aure ya dubaMUKAFA'AHwato dai-daito tsakanin miji da mata, domin duk lokacin da ya zamto miji daba ya iya hidimawa matarsa wajen kiyaye mata abincinta, muhallinta uwa-uba bashi da karfin siya mata mai wanda zai gyara mata fatar jikinta kamar yadda take a gidan iyayenta, to dole ne a samu matsala. Don haka yana da kyau idan son samu ne ya auro dai-dai da shi ko kuma wacce yafita.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

ADALCI TSAKANIN MACE ƊIYAR TALAKA DA ƊIYAR MAI KUƊI

Tambaya (Taƙaitacciya)

Ina da mata biyu: ɗiyar talaka da ɗiyar mai kuɗi. Shin ya halatta in yi wa ɗiyar talaka tufafi masu araha, ita kuma ɗiyar mai kuɗi in yi mata masu tsada?

Amsa (Cikakkiya kuma Faɗaɗɗiya)

A Musulunci, wajibi ne miji ya yi adalci tsakanin matansa a abubuwan zahiri kamar:

Abinci

Tufafi

Masauki

Kayan more rayuwa

Asalin iyali ko wadatar iyaye ba hujja ba ce ta fifita mace a kan kishiyarta. Dukansu mataye ne a wajanka, haƙƙinsu ya daidaita gwargwadon ikonka.

1. Wajabcin Ciyarwa da Tufatarwa Bisa Kyautatawa

Dalili daga Al-Qur’ani

﴿وَعَلَى الْمَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ لَا تُكَلَّفُ نَفْسٌ إِلَّا وُسْعَهَا﴾

(Suratul Baqarah: 233)

Hausa:

Wajibi ne a kan wanda aka haifa masa (miji) ya ciyar da matansa kuma ya tufatar da su bisa kyautatawa. Ba a kallafa wa rai sai abin da zai iya.”

👉 “Bil-ma‘rūf” yana nufin abin da al’ada ta yarda da shi, gwargwadon ikon miji, ba bambancin asalinsu ba.

2. Bayanin Malamai (Ibn Kathir)

Maganar Malami

﴿يَعْنِي بِالْمَعْرُوفِ أَيْ بِحَسَبِ عُرْفِ بِلَادِهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ غَيْرِ إِسْرَافٍ وَلَا إِقْتَارٍ﴾

(Tafsīr Ibn Kathīr 1/634)

Hausa:

Ma’ana, a ciyar da su da tufatar da su gwargwadon al’adar mutanen ƙasarsa da ikon arzikinsa, ba tare da ɓarnatarwa ko ƙunci ba.”

👉 Don haka, adalci shi ne a daidaita darajar abin da kake ba kowacce.

3. Haramcin Fifitawa a Abubuwan Zahiri

Gargadin Annabi

﴿مَنْ كَانَتْ لَهُ امْرَأَتَانِ فَمَالَ إِلَى إِحْدَاهُمَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَشِقُّهُ مَائِلٌ﴾

(Sunan Abī Dāwūd: 2133 – Hasan Sahih)

Hausa:

Duk wanda yake da mata biyu sai ya karkata ga ɗayarsu (a zalunci), zai zo ranar Alƙiyama rabin jikinsa yana karkace.”

👉 Karkatawa a nan ya haɗa da tufafi, abinci, masauki, da kayan more rayuwa.

4. Amsa Kai Tsaye ga Tambayar

Ba ya halatta ka sayi wa ɗiyar mai kuɗi tufafi masu tsada, ka bar ɗiyar talaka da masu araha idan ikonka ya kai daidaitawa.

Wajibi ne darajar ta daidaita:

Idan ka saya wa ɗaya tufafi darajar 5,000, wajibi ne ka saya wa ɗayar ma daraja iri ɗaya.

Ba lallai su zama kala ɗaya ba, amma daraja da tsada su yi daidai.

Haka nan a abinci, masauki, da kayan more rayuwa.

5. Hikimar Adalci da Maslaha

Adalci:

Yana kare gidanka daga rikici

Yana tsare ka daga zunubi

Yana sanya albarka a aure da zuriya

Haka kuma, yana da kyau a duba kafā’ah (daidaito) lokacin aure, domin kada a shiga ƙunci da sabani idan ikon miji bai kai bukatun rayuwar da mace ta saba ba.

Kammalawa

Asalin mace—ɗiyar talaka ko ɗiyar mai kuɗi—ba ya canja haƙƙinta a wajanka. Adalci wajibi ne, fifitawa haramun ne a abubuwan zahiri. Wannan ne hanyar tsira a gaban Allah.

Post a Comment

0 Comments