Waƙar "RANAR HAUSA" an gina jigonta ne bisa kishin harshen Hausa, da nuna tumbatsar harshen da kira i zuwa Hausawa da sui riƙo da shi kuma sui ƙoƙarin haɓaka shi.
Waƙar ƙwar-biyar ce (muhammasa), tana ɗauke da amsa-amon ciki (ƙafiya) da na waje.
Babban amsa-amonta shi ne harafin (K), wanda Sha'irin yai ishara a waƙar da cewa:
"Ƙafiyar na yi ne da K—K—K"
Waƙar tana da tsarin "mabuɗi" da "marufi" irin na asali—ma'ana musulmar waƙa ce.
WAƘAR RANAR HAUSA
Fa bismillahi na fara,
Alhamdulillahi nai shukura,
Da Attahiyatu zan ƙara,
Ga Manzo nawa babu jira,
Wannan wanda kai ka mai aike.
Allah Buwayi ka ji roƙona,
Ka ban ilimi in zazzana,
In jirga ɗango
in a'auna,
Jama'a su ji ta har su amfana,
Harshena ka warware tarke.
Mun san Hausa na da Zaurance,
Lugude har da ma Adon zance,
Da Ƙarangiya
Karuruwan zance,
Har Tatsuniya Zuben zance,
Ni na fi ƙarfi a gun Waƙe.
Jama'a ku yo gudu na fanfalaƙe,
Bikin gidanku kar ku dai zuƙe,
Ko da jan ciki fa ko dunduƙe,
Ba sarefa gami da zuƙalaƙe,
Ku biyo lawali ku zo miƙe.
Yau Hausarmu ta fi Sha—kundum,
Ƙarar
aradu ta wuce "dum dum"!
Daga Sin har zuwa ga nan Kindim,
Wane Amintah mun wuce Bandam,
Zaƙwai—zaƙwai a dangana ga rake.
Cakwai—cakwai fa ɗanɗanon zaƙi,
Garai—garai ruwan cikin tafki,
Kwasai—kwasai fa kwalliya ta jiki,
Mulai—mulai fa ƙurmusun baki,
Harsuna Hausa ta fa doddoke.
Adabinmu har gami da al'ada,
Adabinmu yai ladab kamar fada,
Al'adarmu tai cikar idda,
Dawa da daddawar dawar Wada,
Ga malamanmu na ta yin tarke.
Hausarmu yanzu za mu inganta,
Harshen su Talle Lantana Atta,
Harshen Narambaɗa
da ma Shata,
Harshen Sipikin da Ɗantata,
Ga Sha'iri na ta yin koke.
Hausarmu yau ta zaro zuga,
Sudan Masar da Sin ta zazzaga,
Turai da Rasha babu ko jinga,
Ta haura dangali da ma danga,
Ararraɓi Garahunu Marke.
Kaya na maƙulashe ga cima,
Ɗanbagalaje
ɓaga tsala ma,
Hoci daho muna ta didima,
Caccanga masa gurasa ma,
Burabusko ake tuƙe.
Ɗanwake
Alkubus gudun-ƙurna,
Alkaki zuma wayyo raina,
Funkasau miya ta taushe ma,
Kuka da zogale fa ba rama,
Da rama karkashi ka yayyauƙe.
Riga da wando mu sa sutura,
Girke ɓarage
gami shakwara,
Zanna damanga me fa za ka ara,
"Kayan aro fa bai rufe katara"
Da Allah kar mu ɗauki ko tsinke.
Juju da iska da ƙwanƙwamai,
Jam'i na gwamma ka ce gwammai,
Jam'in dami sai ka ce dammai,
Sai an yi fari ake maimai,
Fatan kun ɗauki dai haske?
Nuƙu—nuƙu gami da kuskunda,
Ga ƙaura
muna da ma tsada,
Ganda ka rabe da ragadada,
Banɗashe ka
rabe da ma banda,
Kar ka zam tilo baƙin
wake.
Ga tambaya ina yi ma lam—Ma,
Jam'in hatsi da jam'in garma,
Jam'in kurciya faɗan
shi ma,
Jam'in ruwa kaza na ɓauna
ma,
Bahaushe kake fa ba canke.
Ƙyale
dimamisau ta hau dusa,
Doki shi ake yi wa cusa,
Nai kira a gunku ɗaliban
Hausa,
Ku rabe matsattsaku da kwarkwasa,
Nauyi na ni fa na sauke.
Yau ƙwai
da ƙwarƙwatarmu
mun taru,
Har ma kafa ta watsa labaru,
Tururuwa da dandazon faru,
Ba gun sanya ko da tsingaru,
A mota wasunmu ko keke.
Ina abin ya ɓuya
yau ga shi,
Me bacci ku ce da shi tashi,
Ɗan
karauka tsaya ji shi,
Yau kam Hausa ta yi yo nishi,
Sauran harsuna ta babbanke.
Nijar ta riga mu tai ƙunshi,
Farko mu ya kyautu mui kishi,
Farkon zubi a ba Uwar dashi,
Mui sammako mu bar batun fashi,
Shi... Shuna kare ya je aike.
ZAUREN HAUSA sun yi yo ƙwazo,
Muma SAƘAFA KULOB mun zo,
Dandazon Sha'iran Gwani Manzo,
A ƙasan
takarkari akwai zozo,
Ga ma Zage—zagi a can a fake.
Murna muke mun shige jaura,
Ƙaura
a lamho yake kora,
Kere za ya hau fa kan kora,
Turmi yanzu ya buge kura,
Hausar mu yanzu ta biyo yanke.
Ba kotso ku bar batun ganga,
Na ƙare
aikatau na waƙarga,
Nai safiya da yammaci kun ga,
Na samu ƴan kuɗi
na sa riga,
Na dai kusan na dakata na fake.
Zabo yana kiran ƙurƙet—ƙurƙet,
Ba gargada taho kawai sambet,
Ka kakare ka ce affafet,
Mai yin wuƙi—wuƙi ku
ce mai ket!
Zai hattara ƙwarai
anan take.
FA'ALUN FA'ILUN MUFA'ALATUN,
Dan Ranar Hausa nai sukutum,
Ramzin Hijira ku ce ZAMTASHUN,
Rabi—Auwal yana BA'UN,
Ƙafiyar na yi ne da K—K—K.
Tammat na gama a daddafe,
Baiti Tiwente—Two a lissafe,
Da daɗin Three
da Two da sassafe,
Kafin ai daka ake sirfe,
Afwan wurinku na fa babbake.
Af! to wasunku zasu so su shina,
Sunan muwallafinku dan ku tuna,
Almajirinku ne fa rarrauna,
Usman Nagado da zan zauna,
Wannan na Gwale ɗan uwan Zurƙe.
Rabbi ƙara daɗo
salatinka,
Gun Manzan ƙwarai da kai aika,
Har Alan Rasulu tsarkaka,
Da Sahabbai da ba su yin shirka,
Bakina da haka zan tsuke.
(m)Usman Nagado (II)
25 ga Agusta, 2025.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.