Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Hasken Nubuwwa Da Wakar Ciza-Busa

Waƙar farko ita ce ta “Hasken Nubuwwa”. Marubucin Waƙar nan shi ne Usman Nagado (II).

An gina jigonta ne a bisa "Yabon Manzo (S.A.W)"

Waƙar ƙwar-biyar ce, ɗauke da amsa-amon ciki da na waje (babban amsa-amo).

A wannan waƙa an ambaci sunayen wasu daga cikin abubuwan da Ma'aiki ya yi amfani da su (na amfanin yau-da-kullum).

Abubuwan sun haɗa da;

Kansakali, Kwalkwali, Sulke, Muraƙƙa'ah, Jubba, Sambatse, da kuma Barbata.

An yi amfani da abubuwan da suka kewaye ɗabi'a (Nature), domin kusanto da fahimtar mai karatu wajen nuna yadda suka gaza a kwatanta su da hasken Manzo duk da irin haske da amfaninsu. Waɗannan abubuwa sun haɗa da;

—Gamzaki: Alfijir (hasken asuba).

—Bantarma: Hasken da yake wanji da zarar rana ta faɗi.

—Hantsi: Hasken lokacin walaha.

—Garji: Haske na lokacin da rana ta take, ta kai tsakiya (Garjeji).

"WAƘAR HASKEN NUBUWWA"

Ɗan saurayi wai menene,

Fa kake ta murna menene,

Ka washe baki har kunne,

Ko albishir aka yi ma ne,

An baka mata na san ka.

Sai ya kada baki yai sauna,

Malam abinda ya san murna,

Wane a ban aure gu na,

Ai: zagayowar ran suna,

Fa da haihuwar Manzan Makka.

Ko yalla Malam wai ƙaƙa,

Fa kake gani nai ƴar tinƙa,

Tsuntsu ya hango runƙunƙa,

Ga nan fa tafki yai sarƙa,

Daɗi kashe ni ganin harka.

Kura ta yawata kaf daji,

Bata sam abinci ba sai gumji,

Yunwa ta kai ta ƙasan gamji,

Sai ga fa mushen jaki ji,

Ya za ka hango tai gunka.

Yo dubi tasowar iska,

Kai dubi rana ta haska,

Bishiyu suna ta rawa fa haka,

Har ma bisashe sun taka,

Albarkacin Manzon Makka.

Har ma gumaka na murna,

Na bice ƙiran-ƙaryar arna,

Da ka bauta masu kan ɓarna,

Salla bikin ɗaya ce rana,

Kau Maulidi kullum harka.

 

Begen Rasulu abincinmu,

Begen Rasulu abin shanmu,

Begen Rasulu makwancinmu,

Begen Rasulu a barcinmu,

Begen Rasulu da mun farka.

Wane kwatamcin bantarma,

Wa ne gaban gamzaki ma,

Wa ne ya hantsi kai shi ma,

Wa ne ya garjin rana ma,

Hasken Ma'aiki la shakka.

Wa ne ya bantarma fa haka,

Wanda Gantako ke mai duka,

Kullum kaɗa shi ya kai hakka,

Ya shige gidansa yana kuka,

Ƙa za ya kai Manzon Makka.

HaskenSa ya fi na Gamzaki,

Sai assuba yaka yin aiki,

Rana da ta fa fito aiki,

Sai ta kore hasken Gamzaki,

Manzanmu kullum ya haska.

Hantsi da Garji ƴaƴa na,

Su fito suna wasan tirna,

Dare ubansu yai sauna,

Ya fatattake su gida auna,

Ya zasu kai Manzon Makka.

Mun gaskata shi da zancensa,

Dan Rabbana ne ke kimsa,

Masa ko a farke ya furtasa,

Ko ko cikin rurumi yai sa,

Duk dai-wa-daida ba shakka.

Ba ya sarefa a zancensa,

Bai sulmiya ba daɗai amsa,

A faɗin Maƙagin nan nasa,

Bai yada gamgamko ba ƙasa,

Ta Madina dan shi ta haska.

Manzanmu na da bakar yaƙi,

Sannan da kansakalin yaƙi,

Ga kwalkwali hular yaƙi,

Doki gami sulken yaƙi,

Ko yanzu ko yau bai shakka.

Da ruwansa ga shi a barbata,

Ya sanya Sambatsen fata,

Ƙwasai-ƙwasai ga kyan fata,

Da Muraƙƙa'ah Jubbah kwata,

Ga rigunonin mai Makka.

Labbaika babban Limami,

Na Mala'iku sau linzami,

A fage na Allah ba rami,

Duk zuciyoyi da lami,

Da zuwanka kowa ya farka.

Ka kere sammai ba shakka,

Caninka ka ga Masaminka,

Ba shisshigi ga magananka,

Ku ka yo munajati barka,

Da zuwanka sammai sun haska.

Kakan Hassan da Hussaininmu,

Albarkacinku muke samu,

Mai san fura sai yai damu,

Kun bada baya kun bar mu,

Da tunatuninku fa ba shakka.

(m) USMAN NAGADO (II)

      16/10/2024 (M)

*** ***

CIZA-BUSA

01-Wasu na a tudu wasu na kwari

02-Wasu sun taso wasu na shiri

03-Wasu sun yi lamo wasu na ɓari

04-Wasu na ta muzu wasu na ƙiri

05-Wasu sun fara wasu sun bari

06-Wasu sun samu wasu na hari

07-Gururuf gururuf su karab-gari

08-Aka kai gwauro aka kai mari

09-Dan-dan-dan-dan-dan ba ciri

10-Duk cin-diririn-dintsin guri

11-Sa-toka-sa-katsin wuri

12-Haka kakacin sherar sari

13-Kau ragaitar da ka sa fari

14-Ko kana ƙuƙumi ko ko mari

15-Zaburo maza zo kai zabari

16-Baza ƙaimi nemi taro wuri

17-Ka samu halali ba jiri

18-Ka ƙyale shaiɗan makiri

19- Ciza-busa daɗa gurguri

20-Tsarabce-tsarabce iri-iri

21-Tsururutar su wuri-wuri

22-Na zamani nemo tsari

23-A wajen Allahu Mudabbiri

24-Alla kakkaushe mana haɗari.

 (m) USMAN NAGADO (II)

 13 ga Agusta, 2023.

USMAN NAGADO

Post a Comment

0 Comments