Ticker

6/recent/ticker-posts

Binciki Zuciyarka Don Ka Gano Son Ran Da Ke Cikinta

Shaikh Abdurrahman al-Mu'allimiy yana bayani a kan wasu abubuwa da ya kamata mutum yana yawan tunani a kansu, ya sanya su a gaban idonsa, daga cikinsu sai ya ce:

((Mutum ya yi tunanin yadda yake da son rai.

1- Ka gaddara cewa; labari ya same ka cewa: wani mutum ya zagi Annabi Muhammad (saw), wani kuma ya zagi Annabi Dawud (as), wani mutum na uku kuma ya zagi Sayyidina Umar (ra) ko Aliyu (ra). Mutum na hudu kuma ya zagi Malaminka (shugaban Mazhabarka ko jagoran Akidarka ko shugaban Kungiyarka ko shehin Darikarka), Mutum na biyar kuma ya zagi Malamin wani, to shin fushin da za ka yi a kan wadannan mutane, da kokarin da za ka yi na ganin an yi musu ukuba an ladabtar da su ya dace da abin da Shari'a ta hukunta, sai fushinka ga na farko da na biyu su zama kusa da juna, kuma su fi tsanani sosai a kan sauran, haka fushinka a kan na uku ya zama kasa da na daya da na biyu, kuma ya fi tsanani a kan sauran na bayansa, haka fushinka a kan na hudu da na biyar ya yi kusa da juna, kuma ba su kai wadanda suka gabace su ba, kuma a samu tazara tsakaninsu?

2- Ka kaddara cewa; ka karanta wata Ayar Alkur'ani sai ka lura da cewa; Ayar ta dace da ra'ayin Malamin Mazhabarka, da ka karanta wata Ayar kuma sai ka lura cewa; ta saba ma wani ra'ayinsa daban, to shin kallonka ga wannar Ayar zai yi daidai da ta farkon, ta yadda ba za ka damu ba idan ya tabbata ta dace da abin da ka gano, ko kuma ba ta dace ba, bayan ka gama bincike da tadabburi?

3- Ka kaddara cewa; ka samu Hadisai guda biyu, ba ka san inganci ko rauninsu ba, amma daya daga cikinsu ya dace da ra'ayin Malaminka, daya kuma ya saba masa, shin kallonka ga wadannan Hadisai biyu zai yi daidai, ta yadda ba damuwarka ba ce kowanne daya daga cikin Hadisan ya zama ingantacce ko mai rauni?

4- Ka kaddara cewa; ka yi nazari a wata mas'alar da Malaminka yana da ra'ayi a kanta, wani Malamin daban kuma ya saba masa, shin ba ka kasance ka karkata zuwa ga rinjayar da daya ra'ayin a kan daya ba, kawai kai so kake yi ka san wanda ya fi rinjaye a tsakaninsu ka bayyana shi a matsayin mai rinjaye?

5- Ka kaddara cewa; ga nan wani mutumin da kake sonsa, ga can kuma wani da kake kinsa, sai suka yi jayayya a kan wata mas'ala, sai ka yi Fatawa a kanta, alhali ba ka san hukuncin mas'alar ba, kuma kana so ka yi nazari a kanta, shin zuciyarka ba za ta so cewa; wanda kake so a cikin mutanen biyu ya zama shi ne a kan dadai?

6- Ka kaddara cewa; kai da wani Malami da kake sonsa, da kuma wani wanda kake kinsa duka kun ba da fatawa a kan wata mas'ala, sai ka ga fatawowinsu su biyun sai ka ga sun dace da daidai, sai labari ya same ka cewa; akwai wani Malami can daban ya soki daya daga cikin fatawowin naku guda uku, ya kausasa harshe a kanta, shin a wajenka duk daya ne idan ya zama fatawarka ya soka, ko ta masoyinka, ko ta makiyinka?

7- Ka kaddara cewa; ka san wani mutum da yake aikata mummunan aiki, amma ka ji ba za ka iya yi masa inkari ba, sai labari ya same ka cewa; wani Malami ya yi inkari ma wannan mutumi inkari mai tsanani, shin yabawanka ga wannan inkari zai zama daidai idan wanda ya yi inkarin masoyinka ne ko makiyinka, wanda ya aikata mummunan aikin kuma masoyinka ne ko makiyinka?

8- Ka binciki zuciyarka, ka samu cewa; Allah ya jarabe ka da wani aikin sabo ko tawaya a Addini, kuma ka samu Allah ya jarabi wani makiyinka shi ma da wani aikin sabo ko tawaya a Addini, a Shari'a duk dadai kuke, shin kyamatarka ga halin da yake ciki zai yi dadai da kyamatarka ga halin da kai ma kake ciki, har ya zama fushinka ga kanka dadai yake da fushinka gare shi?

A dunkule, hanyoyin son zuciya suna da yawa, ba za a iya iyakance su ba. Hakika na jaraba kaina, ta yiwu na yi nazari a wata mas'ala ina jin cewa; ban yi son zuciya a cikinta ba, har na fahimci wata ma'ana a cikinta na tabbatar da ita tabbatarwan da zai kayatar da ni, sai kuma daga baya na lura da wata matsala mai suka ga wannar ma'ana, sai na ji zan shirya ma wannar matsalar, sai na ji zuciyata tana ingiza ni ga kwakwule-kwakwulen martani a kanta, tare da rufe ido a kan tattauna martanin. Wannan ya faru ne saboda a lokacin da na tabbatar da waccar ma'ana da farko, tabbatarwan ya burge ni, na kasance zuciyata ta karkata ga tabbatar da ingancinta, duk da cewa; babu wanda ya san haka a tare da ni, to yaya kuma idan sai da na watsa ta ne a cikin mutane tukun sai na lura da waccar matsalar?

To yaya kuma lamarin yake idan ba ni na lura da waccar masalar ba, wani mutum ne daban ya ci gyarana?

Yaya kuma idan makiyina ne ya ci gyaran nawa?

Wannan fa ba a tilasta wa Malami cewa; kar a samu nau'i na son rai a zuciyarsa ba, saboda wannan abu ne wanda ya fita daga ikonsa. Kawai abin da yake wajibi a kansa shi ne ya rinka bincikar zuciyar tasa game da son ran da ke cikinta don ya san da shi, sai kuma ya yi kokarin kiyayewa, ya rinka lura da gaskiya matuka, a matsayinta na gaskiya. Idan ya bayyana masa cewa; ya saba ma son ransa to sai ya fifita gaskiya a kan son ran nasa. Wannan shi ne ma'anar Hadisin nan - Allah shi ne mafi sani - wanda al-Nawawiy ya ambace shi a cikin "al-Arba'un", kuma ya ce; Isnadinsa ingantacce ne, Hadisin shi ne: ((Dayanku ba zai yi cikakken imani ba har sai son ransa ya zama mai bin da abin da na zo da shi)).

Malami zai iya gazawa wajen kiyayewa ga son ransa, ya bar ran nasa ta karkata ga barna har ya taimaki barnar, yana zaton bai fita daga gaskiya ba, kuma bai yi gaba da ita ba, wannan kam babu mai tsira daga gare shi sai Ma'asumi. Malamai sun banbanta a cikin haka, a cikinsu akwai wanda yake yawaita sake zuciyarsa ta bi son ransa, ya yi barna har wanda bai san dabi'un mutane ba, bai san girman tasirin son rai a kan zuciya ba ya dauka cewa; mai ganganci ne. A cikinsu akwai wanda yake k'aranta sake zuciyar tasa ga son rai sai ya yi sauki. Duk wanda ya bibiyi littatafan Marubuta wadanda ba su dogaro a Ijtihadinsu a kan Alkur'ani da Sunna zai ga abin mamaki kwarai da gaske, sai dai hakan ba zai bayyana masa ba sai a wuraren da ba shi da son rai a cikinsu, ko ya kasance son ran nasa ya saba ma abin da ke cikin littatafan, saboda ya sake ma son ransa sai ya ga cewa; wadanda suka dace da ra'ayinsa ba su da son rai, wadanda suka saba masa kuma gaba dayansu masu bin son ransu ne.

Hakika a cikin Salaf akwai wanda ya kasance yana kaiwa matuka wajen kiyaye zuciyarsa daga son rai har ya kai ga zaluntar dan'uwansa, misalinsa kamar wanda yake tafiya ne a kan hanya, ya kasance a damansa akwai wajen tuntube, sai ya guje masa, ya nisance shi, sai kuma ya fada wani wajen tuntuben a hanun hagunsa bai sani ba)).

القائد إلى تصحيح العقائد (ص: 30 - 33)

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments