Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ya Sa Amurka Ta Zabi Sufanci a Matsayin Musluncin Da Ta Yarda Da Shi?

ME YA SA AMERKA TA ZAƁI SUFANCI A MATSAYIN MUSLUNCIN DA TA YARDA DA SHI?

Amerka tana da cibiyoyin bincike a kan ƙungiyoyin Muslunci, musamman tun bayan harin 11 ga Satumba. Waɗannan cibiyoyi su ne suka binciko mata, suka gano cewa; Sufanci shi ne tafarkin da ba ruwansa da maganar Jih*adi, Sufaye ba sa wa’azin umurni da kyakkyawa da hani a kan mummuna. Su ne waɗanda suke da ra’ayin a bar kowa ya yi Addininsa bisa yadda yake so, ba tare da inkari ba. Ba su da Aƙidar ƙ*yamar kaf*irai.

Wannan ya sa suke ganin Sufanci shi za su riƙa a matsayin Muslunci matsakaici, abokin tafiya, wanda za su yi ƙawance da shi, don ba zai taɓa zama musu ƙalu-bale ba.

Irin waɗannan cibiyoyi sun haɗa da:

1- RAND Corporation.

2- Carnegie Endowment for International Peace.

3- Brookings Institute.

4- United States Institute of Peace.

5- Center for Strategic and International Studies.

- Da sauransu..

To lallai wannan ba abin mamaki ba ne, saboda da ma Sufanci Addini ne da yake ganin kowa a kan dadai yake, saboda Aƙidarsu ta Wahdatu al-Wujud (komai Allah ne), wacce ta haifar musu da Aƙidar Wahdatu al-Adyan (Interfaith), maana; dukkan Addinai abu ɗaya ne, dukkan masu bauta wa abubuwa daban-daban wa Allah suke bautawa. Babu banbanci tsakanin mai bautar Allah, da mai bautar mutum, da mai bautar rana, da mai bautar kare, da mai bautar saniya, wai duka wa Allah suke bautawa. Shi ya sa babban Shehinsu ya ce:

وما الكلب والخنزير إلا إلهنا *** وما الله إلا راهب في كنيسة

-Wai- da kare da alade duka abin bautarsu ne, haka “fada” da yake coci, ba kowa ba ne face Allah ne!

Subhanallah!

To, a takaice dai, ai lalacewa ta kai matuƙa, idan Yah*udu da Nas*ara suka yarda da kai a bisa Addininka, saboda Allah ya ce:

{وَلَنْ تَرْضَى عَنْكَ الْيَهُودُ وَلَا النَّصَارَى حَتَّى تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ} [البقرة: 120]

“Yah*udu da Nas*ara ba za su yarda da kai ba, har sai ka bi tafarkinsu”.

Kuma da ma manazarta masu yawa - hatta cikin Sufayen - sun tabbatar da cewa; Sufanci ya samo asali ne daga Addinai mabanbanta, Yah*udanci, da Kir*istanci, da Buda da Hindu, da sabuwar Falsafar Plato.

Don haka, idan ka san wannan, ba za ka yi mamaki idan Amerka ta yarda da Sufanci ba, a matsayin Musluncin da ta yarda da shi, abokin ƙawancenta, wanda za ta ƙarfafe shi, don ya yaƙi Addinin Muslunci na gaskiya.

Wannan ya sa ake ta tilasta wa ƙasashe - musamman na Larabawa - dole su rungumi Sufaye, su ba su damammaki su yi ta yaɗa Sufancinsu, don a shagaltar da Musulmai da kaɗe-kaɗe, da raye-raye, da rawa da waƙa, da bikikuwa, da sharholiya, su bar asalin Addinin da Manzon Allah (saw) ya yi aiki da shi.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments