Citation: Sani, A.-U. (2025, November 14). Ƙirƙirarriyar basira (AI): Yadda take da yadda ake yi mata ta yi yadda take yi. Paper presented at the Workshop for Participants of the Hausa World Writers’ Day Short Story Competition, via Zoom.
Fasahar AI ta shigo da gagarumin sauyi a duniya kusan ta kowace fuska. Wannan ya shafi ɓangaren kiwon lafiya da ilimi da kimiyya da fasaha har ma da tsaro da tattalin arziki. Duniya ta mayar da hankali sosai a kan wannan fasahar domin ganin yadda za su ci gajiyarta.
Abubuawan Da Za Mu Koya
Wannan tattaunawar za ta mayar da hankali kan:
Tattauna ma’anar AI
Tattauna yadda AI ke aiki (tsarawa, ɗaukar bayanai, koyo)
Tattauna nau’ukan AI
Tattauna misalan amfani da AI a rayuwarmu ta yau da kullum
Tattauna ƙalubale da matsalolin AI
Ma’ana: AI (Ƙirƙirarriyar Basira) fasaha ce da ake tsarawa da ginawa a cikin na’ura wadda take ba wa na’urori damar kwaikwayon tunani da halayen ɗan'adam (kamar koyo da nazari da warware matsala).
Kalmar "Artificial Intelligence": 1956, a wani taro na bincike a Kwalejin Dartmouth, Amurka - shiryawar John McCarthy (masanin kimiyyar kwamfuta). Ana kiransa uban AI (Father of AI).
Ƙunshiya:
Koyo (Learning): Neman ilimi daga bayanai (Data).
Hukunci (Reasoning): Yin amfani da waɗannan bayanai don cimma manufa.
Ƙirƙira (Creation): Samar da sababbin abubuwa (kamar rubutu ko hoto ko bidiyo).
Bambancin AI Da Sauran Manhajoji:
Manhajoji: Suna aikata ayyuka bisa tsarin ginin da aka yi musu (coding).
AI: Suna koyo daga bayanan da suka ci karo da su tare da yin nazari da yanke hukunci.
Matakan Samuwar AI a Taƙaice
Tushe (Gabanin 1940s): Tunane-tunane na falsafa da ke rayawa da kwatanta faruwar abubuwa
Haihuwar AI (1940s–1950s): Bayan samuwar kwamfutar dijital, a 1950 Alan Turing ya gabatar da “Turing Test” (gwajin Turning) don ganin ko na'urori za su iya tunani.
Binciken Farko-Farko (1950s–1970s): AI da za su iya ayyukan lissafi, buga wasan chess, da sauransu. ELIZA (chatbot), SHRDLU (fahimtar harshe)
Ranin AI (AI Winters) (1970s–1990s): An rage saka hannun jari. An fara karaya saboda ƙarancin cigaba a fannin.
Farfaɗowa (1990s–2010s): Bunƙasar koya wa na'urori ilimi, inda na'urori suke koyo daga tarin bayanai a maimakon gina musu komai dalla-dalla (explicit programming). Kwamfutoci masu sauri sun taimaka. Fahimtar hoto, sarrafa magana...
Bunƙasar AI (2010s - Zuwa Yau): Koyo ta "neural networks", tsarin da yake aiki makamancin na ƙwaƙwalwar mutum. Voice assistants (Siri, Alexa), motoci marasa matuƙa, saƙago masu aikatau, mataimaka (GPT, Gemini)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0001.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0002.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0003.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0004.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0005.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0006.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0007.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0008.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0009.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0010.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0011.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0012.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0013.jpg)
%20-%20Yadda%20Take%20Da%20Yadda%20Ake%20Yi%20Mata%20Ta%20Yi%20Yadda%20Take%20Yi_page-0014.jpg)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.