Daga
A.B.
Yahya
Sashen
Koyar da Harsunan Najeriya
Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Ramzi a nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa yana nufin keɓance tarihi, musamman na lokacin wallafa waƙa, ko adadin baitocin da waƙa ta ƙunsa ta yin amfani da abajadan Larabci. Mawaƙi zai ƙirƙiri wata kalma ko kalmomi, da a wani lokaci akwai ma’ana ga kalmar ko kalmomin. To amma muhimmin abu shi ne bayar da lisafin da haruffan abajada da kalmomin suka bayar. Tun asali wannan fanni daga waƙoƙin Larabci ne marubutan waƙoƙin Hausa suka samo shi. A zamanin Jahiliyya Larabawa sun yi amfani da fannin amma domin su yi ishara ga wani abin tarihi da ya auku a ƙasar Larabawa. Sai bayan zuwan Musulunci ne ilmin ya bazu har ake lissafi da tarihin Hijira cikin ramzi. Hardace waƙoƙi ga Larabawa abu ne da ya kasance al’ada.[1] Har a cikin wannan ƙarni na 21 marubuta waƙoƙin Hausa da Abjadan Larabci ne sukan sa ramzi cikin waƙoƙinsu ko da kuwa da rubutun Boko ne suka rubuta waƙoƙin. Babban dalilin yin haka shi ne kasancewar asalin ramzi daga Larabci ne kuma an ƙirƙira wa haruffan Larabci adadin ta yadda kowane harafi yana da adadi. Abjadan harshen Ingilishi ko Faransanci ba ya da wannan ƙidaya, idan ma yana da ita to marubuta waƙoƙin Hausa ba su san ta ba ko kuma ba su gwada yin amfani da ita ba a iya sanin wannan marubuci.
Haruffan cikin Abajada na Larabci
ishirin da takwas 28 ne. Ko wane harafi kuwa cikin Abajada a matsayin ƙidaya yake, daga ɗaya 1 zuwa dubu 1000. Goma na
farko daga alif sun fara da ɗaya zuwa
goma, goma masu bi musu sun fara daga ishirin zuwa ɗari ɗaya, su kuma masu bin waɗannan daga ɗari biyu zuwa dubu, wato ‘sha’ ne
yake a matsayin dubu. Wannan tsari da ya fara da ‘alif’, ‘ba’, ‘ja’, ‘da’, ya
tsaya a ‘sha’, shi ne ake kira Abajada Maghribi wanda da shi ne wannan muƙala take magana domin da shi ne marubutan waƙoƙin Hausa
suke amfani har zuwa yanzu. Akwai wanda ake kira Hija’i amma ba da shi ne mawaƙan ƙasar
Hausa suke amfani da shi ba.
Abjadan Maghribi shi ne ake fara
koya wa ‘yan makaranta karatu da rubutu na Arabiyya/Larabci domin karanta Alƙur’ani a ƙasar
Hausa. Yanzu da ake da takwarorin makarantun Allo waɗanda ake kira makarantun Islamiyya,
ba lalle ne su karantar da ‘yan makaranta da ABAJADA Maghribi ba. A makarantun
Islamiyya akan karantar da ɗalibai
Abajada da ake kira Hija’i. Duka dai haruffan iri ɗaya ne kuma yawansu 28 ne. Tsari
ne ya bambanta su kurum. Matsalar da za a samu idan mawaƙan ƙasar
Hausa suka kasance masu amfani da duk tsarukan biyu. Tilas a samu kurakurai
wajen fitar da tarihi ko adadi. To amma
har yau marubuta waƙoƙin Hausa suna amfani ne da Maghribi yayin da
za su saka abin da ake kira ramzi.
Koyar da karatun Alƙur’ani a makarantun Allo a ƙasar Hausa akan yi shi ne musamman da harshen
Hausa ko na Fulfulde da yake su ne harsunan da suka fi ƙarfi a ƙasar
Hausa. Sai dai wannan bai hana a koyar da karatun da wani harshe da ba su ba,
kamar Zabarmanci, idan wurin da makaratun suke harshen ne ya fi ƙarfi. Waɗannan
harsuna an ambace su ne don su ne suka fi daɗewa a
wannan ƙasa. Babu matsala idan ‘yan makaranta ba su
iya harshen da ake karantar da su Abajadan ba saboda ƙanana ne. Muhimmin abu shi ne yaro ya fahimci
harafin da ake nufi idan aka ambace shi ko aka rubuta shi, ya kuma iya rubuta
shi.[2]
Ga dai haruffan a tsarin da ake kira Maghribi wanda kuma ake amfani da shi a ƙasar Hausa da ma faɗin Afirka ta Yamma
ب أ
ص ن م ل ك ي ط ح ز و ه د ج ش غ ظ ذ خ ث ت س ر ق ض ف ع
Ga kuma yadda ake rubuta waɗannan
haruffa cikin rubutun Boko:
ṣ n m l k y ṭ ḥ z w/u h d j b a sh gh ẓ dh kh th t s r ƙ ḍ f ʿ
Su kuma waɗannan haruffa, wato Abajada, da
aka rubuta alƙalamin ƙidaya a ƙarƙashin kowane harafi, ana nufin adadin kowane
harafi ne. Misali, alifi adadinsa ɗaya ne, ya
adadinsa goma ne, har dai zuwa sha wadda take da adadin dubu.
Mu ƙara
tantance tsarin haruffan na ramzi maghribi:
ب أ
ص ن م ل ك ي ط ح ز و ه د ج ش غ ظ ذ خ ث ت س ر ق ض ف ع
To ga adadin haruffan idan marubuci ya rubuta kalma ko kalmomi ta amfani da Ramzi cikin rubutun Ajami ko Larabci:
|
ع |
ص |
ن |
م |
ل |
ك |
ي |
ط |
ح |
ز |
و |
ه |
د |
ج |
ب |
أ |
|
70 |
60 |
50 |
40 |
30 |
20 |
10 |
9 |
8 |
7 |
6 |
5 |
4 |
3 |
2 |
1 |
Cigaba:
|
ش |
غ |
ظ |
ذ |
خ |
ث |
ت |
س |
ر |
ق |
ض |
ف |
|
1000 |
900 |
800 |
700 |
600 |
500 |
400 |
300 |
200 |
100 |
90 |
80 |
Wannan kuwa adadin ne idan da
rubutun Boko marubuci ya yi aikinsa:
|
ʿ |
ṣ |
n |
m |
l |
k |
y |
ṭ |
ḥ |
z |
w/u |
h |
d |
J |
b |
A |
|
70 |
60 |
50 |
40 |
30 |
20 |
10 |
9 |
8 |
7 |
6 |
5 |
4 |
3 |
2 |
1 |
Cigaba:
|
sh |
gh |
ẓ |
dh |
kh |
th |
t |
S |
r |
ƙ |
ḍ |
f |
|
1000 |
900 |
800 |
700 |
600 |
500 |
400 |
300 |
200 |
100 |
90 |
80 |
To da wannan adadi ne mawaƙa kan yi amfani su ƙirƙiri abin
da ake kira ramzi. Kada a manta cewa ramzi fannin ilmi ne da ake iya
ambaton tarihi ko yawan abu musamman waƙa ko
yawan baitocinta, har ma da yanayi a wasu lokuta. A cikin waƙar Daliyya wadda Shehu Usmanu ya rubuta ya yi
amfani da ramzi a baitin waƙar na ƙarshe (da Larabci) wato na 63, ya ce, /ƙasshin ba’ada fahhin/
. A rubuce cikin Larabci haruffa ‘ƙ’, da ‘sh’, da ‘fa’, da ‘h’ su za a gani. Idan aka tattara
adadinsu, wato, da 100 da 1000 da 80 da 8, za a samu 1188, wato ke nan lokacin
da Shehu ya rubuta waƙar shi ne
Hijira tana 1188 wadda ta yi daidai da shekara ta 1774 Miladiyya. Wato Shehu
yana ɗan shekara ishirin ya rubuta waƙar domin an haife shi ne a 1754. Ramzi na
tarihi ke nan.
Haka kuma mawaƙa kan yi amfani da ramzi domin su faɗi yawan baitocin da waƙarsu ta ƙunsa.
Misali, Alhaji (Dr.) Aliyu Namangi a baitin waƙarsa,
Tsarabar Madina ya ce,
150. To
adadin baitin kau naƙin
Hamsin ne da
ɗari
tak kwana
Wato da nunu, ‘n’ da ƙa ‘ƙ’ ne ramzin, abin da ke ba da 50 da kuma 100, wato 150. Mai karatu ko saurare ko da ɗangon farko na wannan baiti ya ji zai gane cewa baitocin waƙar 150 ne.
Shi kuwa Haliru
Wurno a waƙarsa ta madahu mai suna ‘Jirgi’, cewa ya yi,
Na yo lisafi
ƙa’imun
adadinta ke nan
Alhaji ƙa’imun na ga begen Annabin
ga
A ɗango na
farko kalmar ‘ƙa’imun’ tana da ‘ƙ’ mai adadin 100, da ‘alif’ mai adadin ɗaya (1) da kuma ‘m’ mai adadin
40. Idan aka tara su sai a samu 141. A ɗango na
biyu kuwa mawaƙin ya yi amfani da kalmar
‘ƙa’imun’ a matsayin kalmar Larabci mai ma’anar
‘tsayayye’, da kuma amfani da salon dibilwa idan aka yi dubi ga kalmar ‘ƙa’imun’ ta cikin ɗangon farko. Wato mawaƙin ya yi yawo da hankalin mai karatun ko
sauraren waƙarsa, ba ma’anar ‘ƙa’imun ta ramzin da ya kawo ba, a’a shi ta
fassarar kalmar Larabci yake nufi.
Ɗangaladiman Wazirin Sakkwato, Alƙali Bello Giɗaɗawa ya yi amfani da tsarin ramzi ya bayyana yawan baitocin da waƙarsa ta ƙunsa:
24. Daɗa waƙag ga ta cika na tsaya nan
Yawan baiti KADA don kak
ka dabke
(Alƙali Bello Giɗaɗawa: A BI GASKIYA AD
DAIDAI)
Kalmar ‘kada’ sunan naman ruwa ce, wato kada, mai harafi biyu, k da d, adadinsu shi ne da 20 da kuma 4, wato 24.
Yanzu bari a sake kawo adadin
haruffan kusa da kusa. Ga na haruffan idan marubuci ya rubuta kalma ko kalmomi
ta amfani da Ramzi cikin rubutun Ajami ko Larabci:
|
ق |
ض |
ف |
ع |
ص |
ن |
م |
ل |
ك |
ي |
ط |
ح |
ز |
و |
ه |
د |
ج |
ب |
أ |
|
100 |
90 |
80 |
70 |
60 |
50 |
40 |
30 |
20 |
10 |
9 |
8 |
7 |
6 |
5 |
4 |
3 |
2 |
1 |
Cigaba
|
ش |
غ |
ظ |
ذ |
خ |
ث |
ت |
س |
ر |
|
1000 |
900 |
800 |
700 |
600 |
500 |
400 |
300 |
200 |
Wannan kuwa adadin ne idan da
rubutun Boko marubuci ya yi aikinsa:
|
f |
ʿ |
ṣ |
N |
m |
l |
k |
y |
ṭ |
ḥ |
Z |
w/u |
h |
d |
J |
b |
a |
|
80 |
70 |
60 |
50 |
40 |
30 |
20 |
10 |
9 |
8 |
7 |
6 |
5 |
4 |
3 |
2 |
1 |
Cigaba
|
sh |
gh |
ẓ |
dh |
kh |
th |
T |
S |
r |
ƙ |
ḍ |
|
1000 |
900 |
800 |
700 |
600 |
500 |
400 |
300 |
200 |
100 |
90 |
Mawaƙa kan ƙirƙiri kalmomi masu ma’ana ko marasa ma’ana
cikin amfani da ramzi. A zamanin Shehu Usmanu ɗan Fodiyo,
har ma a yau, mawaƙa kan ƙirƙiri kalmar
da za ta bayar da ma’ana mai dangantaka da Musulumci. Misalin kalmar da aka fi
amfani da ita a matsayin wani ɓangaren
ramzi ita ce, ‘rushdu’, wadda ke nufin ‘shiryuwa’. Wato ko bayan adana tarihi
da mawaƙi ya yi cikin baitin waƙarsa, ya kuma yi nuni da zamanin hidimar da
suke yi ga Musulumci, domin wannan Kalmar Fannu ce da ke nufin Addinin
Musulunci.
Wani tsari ko salo mai dangantaka
da asalin ramzi shi ne yadda wasu mawaƙa kan
ambaci sunansu ta hanyar tsara harufa ko gaɓoɓin suna. Misali idan sunan mawaƙi shi ne Umaru, sai mawaƙin ya kawo gaɓoɓi ukun da sunan ya ƙunsa, kamar yadda Alhaji Dr. Umaru Wazirin
Gwandu ya yi cikin wannan baiti:
50. Wanda
yay yi waƙa sunanai
‘U’ da ‘Ma’
da ‘Ru’ ga mazamninai
Sai ka zo ka
‘Bi Ke’ birninai
(Wazirin Gwandu: Zaɓaɓɓiya).
Shi kuwa Alƙali Alhaji Haliru Wurno da
zai faɗi sunansa sai ya yi amfani da harufan sunan kamar
yadda ake faɗar su cikin Larabci kamar haka:
49.
Mai biɗat sanin ma’ajin waƙa
‘Ha’u’
‘Dadu’ ‘Ra’ shi yas sarƙa
Wurno ag
garinsu gida haƙƙa
Fassararsa
Alhaji Ishraƙa
Ko da yaushe
bai rasa shiryawa
(Alƙali Alhaji Haliru Wurno:
Tura Ta Kai Bango).
Harafin ض ne Haliru ya kira ‘dadu’ domin idan da ajami za a rubuta Haliru da wannan harafi na ض za a rubuta sunan.
TAMMAT
MANAZARTA
Giɗaɗawa, A. M. B. (2006) Bargon Hikima. Sokoto: Cibiyar Nazarin
Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, sh. 45, bt. 24, ɗg. 2.
Hiskett,
M. (1975), A History of Hausa Islamic Verse,
London.
Namangi,
A. (1978) Waƙar Furan Gero da Tsarabar Madina, Zaria: Northern
Nigerian Publishing Company.
Usman, B.
B. (2006), ‘Hikimar Magabata: Nazarin Ƙwaƙƙwafi a kan Rayuwar Malam (Dr.)
Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916 –2000)’, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Wurno, A.
A. H.Diwanin Waƙoƙin Alƙali
Alhaji Haliru Wurno wanda mai muƙalar nan
ya mallaka.
Yahya, A.
B. (2002), ‘Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani
Shaƙo cikin Nazarin Waƙa’ cikin Studies
in Hausa Language, Literature and Culture 5, Kano: Bayero University.
Yahya, A.
B. (2013), ‘Tsattsafin Raha cikin Waƙoƙin Alƙali
Haliru Wurno’, cikin Zauren Waƙa: Journal of Hausa Poetry Studies 1, Sokoto:
Usmanu Danfodiyo University.
Yahya, A.
B. (2016) Salo Asirin Waƙa (sabon bugu). Sokoto: Guaranty
Printers. https//en.wikipedia.org>wiki>A
[1] Akwai saɓanin ra’ayi tsakanin masana a kan waƙoƙin
da Larabawa suka kira ‘Mu’allaƙaat’,
wato waɗanda aka
rataya. Wasu suna ganin sunan ma’anar kinaya ya ƙunsa, da nufin abin da gama-gari ne ne ga kawunan mutane, ba
wai rataya waƙoƙin aka yi ba ga bangon Ka’aba; wasu masana
kuwa suna ganin ma’anar kalmar ta zahiri ce. Idan ma’anar kinaya ce ‘mu’allaƙaat’ take da to kuwa mai yiwuwa ne domin
kuwa ba dukan shahararrun waƙoƙin Jahiliyya za su kasance a bangon Ka’aba
ba, balle dukkan waƙoƙin zamanin. Haka kuma waƙa ga Larabawa kusan al’ada ce, duk da a
lokacin jahiliyya karatu da rubutu ba su da yawa. A ƙasar Hausa kafin shigowar Musulunci da ma
abayan shigowarsa akwai irin wannan tasiri a kan Adabi kamar waƙoƙin
baka da karin magana da tatsuniya da sauran ɓangarorinsa, har ma da tarihi. Don ƙarin bayani a duba Mu’allaƙat cikin,
https://en.wikipedia.org
[2] Mai wannan muƙala da abajadan Fulatanci aka karantar da
shi a makarantar Allo, duk kuwa da bai jin harshen Fulatanci.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.