Ticker

6/recent/ticker-posts

Jerin Kare-Karen Magana Da Salon Magana Masu Nuna Nakasa Da Nakasassu

Waɗannan jerin kare-karen magana ne da kuma wasu salon magana na Hausawa waɗanda suke magana dangane da nakasa da kuma nakasassu. Sun shafi nau’ukan nakasa da nakasassu irin su kuturu da kuturta, makaho da makanta, gurgu da gurgunta, bebe da bebanta/bebantaka, da dai sauransu.

1. A bar ta makaho a kama mai ido

2. A ja mu a kai mu an ba uwar makaho kashi

3. A kai Ladan gidan maza kurma ya ci sarauta

4. A kawo ɗauki ɗaki ya faɗa wa gurguwa

5. A saɓa a rufe dambun mahaukaciya

6. A taru a kashe mahaukacin kare

7. A yi abin da za a yi mahaukaci ya ɗauki rigar kurma

8. A zo dai, a zo dai ɗaki ya danne gurguwa

9. Abin ba daɗi, wai mahaukaci ya ci kashi

10. Abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa

11. Abin faɗa na mai baki ne bebe sai ka dangana

12. Abin wani abu ne, faɗan makaho da daddare

13. Abu ɗaya na mutum ɗaya ne, goriba da kuturu

14. Aikin banza makaho da waiwaye

15. Aku kuturu

16. Allah ba ya tauye banza

17. Allah ka gyara tuwon makauniya ba don tana ganinsa ba

18. Allah na gani ake cutar makaho

19. Allah shi ya san karatun bebe

20. An ci gari da shi ya kama kuturun Bawa

21. An ci yaƙi an bar shi da kuturun bawa

22. Ana hauka ya ƙare kana saran turu

23. Aradu mai ɗima kurma

24. Ba a rarrabewa da barcin makaho

25. Ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara da yatsu

26. Ba don tsoron Allah ba, kashin makaho da dare ba wuya

27. Ba ji ba gani auren kurma da makaho

28. Ba ka iya cin ƙawan makauniya

29. Ba kanta ɗan sanda ba ido

30. Ba nakasasshe sai kasasshe

31. Ba shigar ba fitar an bai mahaukaci riƙon gari

32. Bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne

33. Ban ga alamu ba, an ce kuturu Allah ya sa ka wanye lafiya

34. Ban san zancen ba an kai bebe ƙara

35. Banza a banza an sa kuturu ɓallar jaki

36. Banza girman mahaukaci ƙaramin mai hankali ya fi shi.

37. Bari mu ji ɗumi wai mahaukaciya ta yi gobara

38. Cikar mahaukaci duka

39. Cin makauniyar kasuwa

40. Da babban mahaukaci gara ƙaramin mai hankali

41. Da haka muka fara wai kuturu ya ga mai ƙyasfi

42. Da kamar wuya gurguwa da auren nesa

43. Da wari an ce da makaho ga ido

44. Damben kuturu ba a naɗi

45. Dan ma kai ne, mahaukaci ya kashe ubansa.

46. Dare mahutar bawa, makaho ya ce tufkar fa

47. Dariyar darara kuturu dara makaho

48. Dashen makauniya

49. Don gaskiyar makaho ka cacar dare don in ya ci a ba shi

50. Duk abin ɗaya ne mai ido ɗaya ya leƙa shantu.

51. Duk kuturun da ya riƙa ai ba ya jin magani

52. Duk wanda aka gan shi da madubi a kama shi, wai makaho ya zama gwamna.

53. Duk wanda ba ya gane haukan mahaukaci shi ma mahaukaci ne

54. Duk ɗaya makafi sun yi dare

55. Fara’a kamar an ba kurma riga

56. Faɗa da kurma ba ya ƙarewa

57. Ga wani bawan Allah damo ya ga makaho

58. Gane min hanya wai makaho ya so tsegumi

59. Gayyar makaho mai nishi ka sha gari

60. Gida mahaukacin kare mai cizo

61. Gobe juma’a kuturu dariya yake

62. Gudu a kunya ba na gwami ba ne

63. Gudu, yaro gudu, wasa na mahaukaci

64. Gurgu ba shi koya gurgu tafiya

65. Gurgu ka fi mai ƙafa ban haushi

66. Gurgu ka fi mai ƙafa iya rakace/iya shege

67. Gurgun mage tashin ɗangalau

68. Gurguwar dabara

69. Gurguwar shawara

70. Gurguwar tsanya da wuri take fara rami

71. Gurguwar tsanya da wuri take fara rarrafe

72. Gurrgu yana zaune ake sarar sandar dukan sa.

73. Gwami na yi wa mai cassa gori

74. Hannu da hannu cinikin makaho

75. Hannunka mai sanda

76. Har ka tuna min an ce da mahaukaci ba ya duka

77. Hauka da naɗe-naɗe ɗan wake ya ga tubani

78. Hauka maganinka Allah

79. Hauka maganinka Allah

80. Haukan kaza auran muzuru

81. Idan ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka dutse ne

82. Idan zuciya ta makance to gani ido bai yi fa’ida ba

83. In ka ga kurma na gudu, ka fi shi gudu don shi gani ya yi ba ji ba

84. In ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa to ya taka dutse.

85. Ina ruwan makaho da kunya

86. Ina ruwan wani da wani mahaukaci ya ga ubansa da kaya.

87. Kadafkara shiga akurki, ya ce hauka ko bori?

88. Kadan ba ƙarya ba kuturu ya yi dambe da mai yatsu

89. Kadan ba rigimar makaho ba, ya ya kokuwa da mai ido

90. Kadaran-kadahan ka da mai gani ya taka makaho

91. Kan uwa da wabi, makaho ya yi jifa kasuwa

92. Kanku ake ji mahaukaci ya faɗa rijiya

93. Kira kamar sabon makaho

94. Ko in kula zabi sun ga makaho

95. Komai ingancin makauniyar goɗiya, ba ta halarci gasar sukuwa ba

96. Kowa da wurinsa, an ɗaure mai dungu ya sulle

97. Ku ci ku ke aiki an ba mai kurkunu kaɗan

98. Ku kuke gani sgaɗin makaho

99. Kunne kamar makaho

100. Kuturu ake yi wa gayya ba mai yatsu ba

101. Kuturu da kuɗinsa alakaki sai na ƙasan kwano

102. Kuturu mugun baƙo

103. Kuturu ya so dambe babu yatsu

104. Kuturwar uwa ba ki da mamora

105. Leƙa shantu biyu a lokaci guda ba na mai ido ɗaya ba ne

106. Mahaukaci da gata jagorar mai hankali.

107. Mahaukaci da kayan kanwa in ka gaji tsoma a ruwa

108. Mahaukaci da ranarsa

109. Mahaukaciyar kasuwa mayankarki gabas

110. Mai hankali ke gane ɗangyashin kwaɗo

111. Mai ido ɗaya ba ya gode Allah sai ya ga makaho

112. Mai ido ɗaya sarki ne a garin makafi

113. Mai kurman jiki ba ya rama

114. Makaho ba ya shakkar ɓatan madubi.

115. Makaho bai san ana ganinsa ba sai an dungure shi

116. Makahon birni ya fi mai ido wayo

117. Makahon kuda ga cizo

118. Me ya haɗa kuturu da zobe

119. Miskili ka fi mahaukaci ban haushi

120. Mu gamu a ka, jakin kuturu ya yi kaye

121. Mu je zuwa mahaukaci ya hau kura.

122. Mu yi hannun kuturu da makaho.

123. Muƙami bebe da radiyo

124. Muƙami kuturu a Landan

125. Mutanen kirki damo ya ga makaho

126. Na ci damben kuturu ko ba kisa zai tara jini.

127. Na ji wannan inji kurma

128. Na san a rina an saci zanen mahaukaciya.

129. Nadakama ba ka ji kira sai hoge

130. Nadakama manzonka hoge

131. Ni kallonsa nake yi wai makaho yai faɗa da matarsa

132. Ni kaɗai na sani sautin mahaukaciya

133. Ƙafar kuturu mutumcinta takalmi

134. Ƙaramin kuturu ka dajine, manya sai gwalo

135. Ƙarfe shiru da minti kakam agogon kurma

136. Ƙauri da daɗewa ba’auzani ya sayi kuturu ya ce ko yatsa bai fito ba

137. Ƙundumbala shiga makaho kogi

138. Ƙura na kasuwa mahaukaci ya kuɓuta

139. Ƙuruci dangin hauka

140. Ƙwace goriba a hannun kuturu ai ba wuya ba ne

141. Ƙwace goriba a hannun kuturu ba wuya ba ne.

142. Rashin sani ya sa makaho ya taka sarki

143. Riƙon mahaukaci sai sarki

144. Sai inda mai ya ƙare, shiga motar mahaukaciya.

145. Samun gari kuturu gaɗa a rama

146. Santin kurma mai wuyar ganewa

147. Somin taɓi ne mahaukaciya ta mari uwarta

148. Somi-somin hauka zubar da yawu.

149. Tabarmar kunya da hauka akan naɗe.

150. Tana ciki kunamar kurma

151. Uban kuturu ya yi kaɗan

152. Ɓarin makauniya ba ya kwaso

153. Wa zai taɓa ni ya sha adda? Inji kuturu

154. Wawa ba mahaukaci ba ne in ya ci kasuwa gida zai kai

155. Wurƙilili ido ɗaya daɗin leƙa buta

156. Ɗan gurgun mage kana ganin takaicin kaji

157. Ɗan mahaukaciya,mahaukaci ne

158. Ɗan makahon doki, hawansa sai da ɗan jagora

159. Ɗan-ba-ƙara kuturu ya sa hannunsa a tukunyar naɗi

160. Ɗingishin gurgun kwaɗo a ruwa, mai hankali ke ganewa

161. Ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa

162. Ya yi tsayuwar gwamin jaki

163. Yanzu aka fara, mahaukaciya ta shiga rawa

164. Yin ya fi rashin yi, mahaukaciya ta yi wanka da ruwan ɗan wake

165. Zafin zuciya kamar kuturu sabon shiga.

166. Zuciya kamar sabon kuturu

Misalan Karin Magana

Post a Comment

0 Comments