𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Malam ina da tambaya, me ke kawo saurin kawowa ga namiji yayin Saduwa? Mijina baya kai minti biyar ya kawo. Me yake haifar da hakan.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam
warahmatallahi wabarakatuh.
Toh da farko akwai dalilai
da suke haifar da saurin kawowa ga namiji kamar haka:
1. Ciwon sanyi na mutuƙar taka rawa wajen Sanya Namiji saurin
kawowa da bayan ya kawo yakasa katabus jikinsa ya mutu Kuma sha'awarsa ta ɗauke
kamar wutan nefa.
2. Idan mace tana da
tabbatacciya ni'ima wadatacciya to da zarar Namiji ya zura azzakari ba wuya daɗi
zai kwasheshi zai kawo maniyinsa sabida santsi da dankon ni'ima zai saurin Kai
saƙo ga kwakwalwarsa sai kawai maniyyin ya
taho, toh irin wannan sai dai sudinga Tarawa a saduwa ta biyu yadda zai jima
Bai kawo ba har ya gamsar da matarsa.
3. Akwai Kuma maza da
halittarsu haka take Wanda lafiyarsa ƙalau
ba shi da ciwon sanyi Sam Amma Yana zura azzakrinsa zai kawo wani kafin yazura
da anafara wasannin zai kawo.
4. Akwai mazan Kuma da
lafiyarsu ƙalau Suma Amma sabida
tsananin soyayyarsa da matarsa da tsananin sha'awarta da yakeyi Wanda shi Kuma ƙarfin soyyaya kansa sinadaran ma'ikatar
sha'awarsa kan saurin aika saƙo zuwa
kwakwalwarsa Wanda ko jingina ya yi ajikinta sai kaga ya kawo ko Kuma Yana zura
azkarinsa zai kawo, toh duk irin waɗannan
gaskiya sai dai sudinga ƙoƙarin sake saduwa da matansu a karo na
biyu wanda hakan zai kaisu ga gamsar dasu.
5. Ɗaukar lokaci mai tsayi ba tare da
mijinki ya kusance ki ba. Wannan shi ma babban dalilin dake haifar da saurin
kawowa, in ta tabbata kuna ɗaukar dogon lokaci baku sadu
ba to sai kubi shawarwarin da zan baku kamar haka:
1. Ya yi wasa dake sosai har
buƙatarki ta biya don rage miki ɓacin-rai
ta hanyar tabawa, tsotsa, shafawa ko shan wajajen da zasu kaiki ga samun biyan buƙata don ki daina jin haushinsa.
2. Yin Jima'a akai-akai,
wato idan ya sadu dake to yaje ku wanke gabanku da ruwan dumi Sannan ya yi alwala
bayan kun huta sai ki sake yi masa dabara ta hanyar shan azzakarinsa, shafa
kirjinsa da bayansa, tsotsar nononsa har gabansa ya mike sai ku sake saduwa.
3. Idan na biyu bai yiwu ba,
sai kuyi baccinku. Bayan ko kafin sallar asuba ku sake komawa don saduwa shi ma
Wanan lokacin Yana da tasiri wajen saduwa sabida ba gajiya Kuma mutum ya samu
hutu.
4. Kuma Ki tabbatar a sati
kun sadu kamar sau huɗu ko biyar, da haka zaki ga
lokacin da yake kawowa yana dadewa ta yadda zai iya cimma zango mai nisa.
5. Ya dinga shan lemon Zaki,
kankana, Ayaba da dai sauran kayan marmari ko sau ukune a sati, Kuma ya fake
kan Shan Kaya Mara chemical, ya guje Shan Zaki, lemukan gwangwani da na roba.
Aƙatshe ya nemi maganin sanyi ingantacce
yadinga yawan shansa , da kuma motsa jiki Koda minti 30 a kullum ko sau 3 a
sati, In sha Allahu wannan matsalar za ta wuce indai an jaraba. Allah ta'ala ya
tsaremu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.