Ticker

6/recent/ticker-posts

Karin Magana da Salon Magana Kan Masu Nakasa

Karin magana salo ne na yin magana taƙaitacciya kuma dunƙulalliya wacce ke ɗauke da ma’ana mai faɗi, domin isar da saƙo cikin hikima. Akan yi amfani da wannan salo wajen yin nuni, gargaɗi, yabo, ƙarfafa guiwa, da sauransu duk a hikimance, ta yadda kusan in ba cikakken Bahaushe ba, fahimar wannan zance yana da wahala. Daga cikin irin waɗannan maganganu akwai waɗanda suka shafi masu nakasa, wadanda ke ɗauke da darasi da tunatarwa game da halin ɗan adam da mu’amalarsa. 

Karin Maganar Masu Nakasa

Wannan rubutu ya tattaro wasu daga cikin irin waɗannan maganganu na masu nakasa. Ga misalansu kamar haka:

1.      Haushin rashi, makaho ya ce ido da wari.

2.      Daidai, mai ido ɗaya ya leƙa buta.

3.      Daidai, mai ido ɗaya ya leƙa buta.

4.      Na nawa kuma? An ce da kuturu "Allah ya tsine maka" (a wata ruwayar "Allah ya debe maka albarka).

5.      Ta nan muka fara/Da haka muka fara, kuturu ya ga mau kyasbi.

6.      Abin da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

7.      A garin makafi, mai ido daya sarki ne..

8.      Duk ɗaya, makafi sun yi dare.

9.      Naci, damben kuturu.

10.  Ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa.

11.  Haka tara, inji kishiyar mai mageduwa.

12. Me na iya da abin da ya fi ƙarfin wuta, inji kishiyar ƙonanniya (Idan an ɗauki ƙonewa a matsayin nakasa).

13.  Abin faɗa na mai baki ne, bebe sai ka dangana.

14.  Abin da wuya, gurguwa da aure nesa.

15.  Aikin banza, makaho da waiwaye.

16.  Aje mahaukaci gidanka, don mahaukacin gidan wani.

17.  Allah ke gyara tuwon makauniya ba don tana ganinsa ba.

18.  An ce da kuturu ga yatsu ya ce “me zan yi da yatsu”.

19.  An ce makafo, ga ido, ya ce da wari.

20.  An ci gari da shi, amma ya kama kuturun bawa.

21.  A ja mu, a ba mu kashi, in ji uwar makaho.

22.  Babu ruwan kuturu da zobe ko ya kashe na dinari.

23.  Babu ruwan makafo da madubi ko an sawo daga turabulus.

24.  Ba mu rarrabe ba, ‘yan kura sun ga mai wufifi, sun ce ko kuturu ne.

25.  Daga nan muka far, kuturu, da ya ga mai kyasfi.

26.  Damben kuturu ba a naɗi.

27.  Dokin “da na sani” gurgu ne.

28.  Don tsoron Allah ba, kashin makafo da dare ba wuya.

29.  Gara kowa da ni, in ji matar bebe.

30.  In ka kori kuturu, zai tafi dud da kuda.

31.  Kariyar arziki, kuturu da jan allura.

32.  Kauri da daɗewa, ba'azbine ya sayi kuturu ya ce ko yatsa bai fito.

33.  Kowa ya ci ldar kuturu, shi ke yi masa aski.

34.  Kowa ya rena dundumi bai ga makanta ba.

35.  Ku tattaro, ku gani kuturu ya bai uwar makaho kashi.

36.  Kurma da bebe hankalinsu kaɗan shi ke, su ba su aiki, sai da ganin zairi.

37.  Kuturu mugun bako.

38.  Kuturu ya so dambe babu yatsu.

39.  Kuturu da kuɗinsa, alkaki sai na ƙasan kwano.

40.  Ƙaramin kuturu ka dajine, manya sai gwalo.

41.  Ƙwace goriba hannun kuturu wani abu ne.

42.  Mai ido ɗaya ba ya gode Allah sai ya ga makaho.

43.  Maƙetaci miji gurguwa, sai da ya bari ranar tafiya ta zo ya saida jaki ya saya mata kijera.

44.  Muwa gamu a ka, jakin kuturu ya bi tofa.

45.  Sabo da dalili kuturu ya kama trwaɗa.

46.  Wanda ya saurari aikin wani, shi na zama kurma lahira.

47.  Taka ta same ka, am bai kuturu kwantar akuya.

48.  Yau ar! Gobe tir!, sarki bebe, ɗan galadima kurma.

49.  Yau da kallo, an sa kuturu murzab barkono.

50.  Yau da kallo, an sa kuturu saƙar akauje.

51.  Zama ya yi zama an sa mahaukaci tsaron gawa, ya ce tashinki tashi na.

      Salon Magana

1. Hannun kuturu da makaho

2. Ban hannun makafi

3. Ɓarin makauniya

      Waɗannan karin magana na nuna yadda al’ummar Hausawa ke kallon nakasa da darussan da ake ɗauka daga rayuwar juna. Tattara su a wuri guda yana ba mai karatu damar samun su cikin sauƙi kuma ya yi amfani da su yadda ya dace.

Post a Comment

0 Comments