Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wasa Da Al'aura (Istimna'i)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko ya halatta idan Mutum ya ji Sha'awa ta kAma shi yabiyawa kansa buƙata ta hanyar wasa da al'aura (Istimna'i)?

​​𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

​​Alal-Haƙiƙa wannan wata Mas'alace da ana iya cewa ta yawaita sosai awannan zamanin, musamman tsakanin Samari da 'Yammata, harma da Matan-Aure da kuma Mazan-Aure, to amma dangane da abin da da ya shafi hukunci akan Istimna'i' (Masturbation) Malamai sunyi Saɓani akai tare da maganganu kamar guda uku:

1. Ƙauli na farko Shi ne,

Mazhabin Malikiyya da Hanabila da kuma mafi yawa daga cikin Malamai duk sun tafine akan cewa haramunne bai halattaba ga Mace ko Namiji su aikata hakan, domin kuwa yin hakan Ta'addancine da ƙetare iyakar Ubangiji, waɗannan Malamai dai sun kafa Hujjarsune da faɗin Aʟʟāн () a cikin wannan aya inda yake cewa:

​وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ.......... إلَخ​

​​MA'ANA:​​

​​ (Muminai) sune waɗanda suke kiyaye farjinsu (basayin zina kuma basa yarda kowa yaga tsiraicinsu)…………har zuwa ƙarshen ayoyin:​​

2. Ƙauli na biyu Shi ne,​​

Mazhabin Hanafiyya da wani sashe na Hanabila suntafi akan cewa asali dai yin Istimna'i haramunne, to amma yana iya zama halal tare da wasu Sharuɗɗa kamar haka;

ya kasance Mutum bashi da aure.

ya kasance in baiyi hakanba to ba makawa dole sai ya je ya yi Zina.

kada ya yi nufin jindaɗi kawai, saidai ya yi nufin yana sone yakarya ƙarfin-Sha'awarne, kokuma ya kasance idan Mutum baiyiba hakan na iya haifar masa da wata cuta ajikinsa, suka ce idan akwai irin waɗannan Sharuɗɗa to ya halatta Mutum ya yi Istimna'i, saboda Ƙa'idar nan ta Usūl da take cewa:

  (إرتكاب أخف الضررين)

3. Ƙauli na uku kuma Shi ne,​​ Akwaii wasu daga cikin Malamai da suke ganin cewa kai tsaye yin Istimna'i ya halatta, Dalilinsu kuwa suka ce babu wani Nassi daga Alƙur'ani ko Hadisi da yafito afili ƙarara abayyane yanuna haramcin Mutum ya yi wasa da al'aurarsa har yafitar da Maniyyi, musamman kuma idan ya kasance Mutum yayi hakanne sakamakon yasamu kansa cikin tsanani, kamar irin Matan da Mazajensu sukanyi doguwar tafiya basu dawoba, ko Matar da aka saketa, ko wacce ma batayi aurenba, ko Namijin da bashida Mace kuma Sha'awa tana damunsa, kokuma yana da Matar amma wani dalili ya sa bazai iya kusan tartaba, dadai sauran abubuwa makamantansu, suka ce irin waɗancan babu laifi suyi, Saidai duk dahaka suka ce yinsa ɗin abin ƙyamane ga wanda Sha'awar ba ta tsananta a gareshiba. Sannan suka ce ai dukkan Malamai sunyi Ittifaƙi akan cewa ya halatta Mace ta yi wasa da Azzakarin-Mijinta haryakai ga fitar da Maniyyi, hakanan shi ma ya halatta ya yi wasa da Farjin-Matarsa harta gamsu, suka ce to inda a ce akwai wata cuta da zata samu Mutum adalilin hakan kamar yadda ake faɗa, to da Shari'a ba ta halatta yin hakan ga Ma'aurata bab.

Sannan suka ce babu wani Hadīsi da ya tabbata daga bakin Mαnzon AAʟʟāh Sallallahu alaihi Wasallam da ya yi magana akan wannan Mas'ala, balle harkaji ana cewa wai duk wanda yamutu yanayi to ranar Alƙiyama za a tasheshi yayiwa hannunsa ciki, babu Hadīsin da ya inganta akanhaka,

Saidai kuma agaskiya maganar da mafi yawan Malamai suka tafi akanta na cewa haramunne, ko shakka babu cewa maganarsu tana da ƙarfi sosai, danhaka dai zaman lafiya anan shi ne, barin aikata Istimna'i shi ya fi zama alkhari, musamman dan Mutum ya kuɓutar da kansa daga cikin Saɓanin-Malamai,

​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαм

 ​​AMSAWA

 Mυѕтαρнα Uѕмαn

 08032531505

​​Doмυп пεмαп ƙaяıп вαчaпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:​​

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments