Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani A Kan Salloli Biyar Na Farilla

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Dan ALLAH ina so a kara mana bayani sossai yadda ake salloli 5 na farillah.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Da farko ba a yin sallah sai da tsarkin jiki da na tufafi da muhallin yin sallah, haka nan ba a yin sallah sai da alwala, ko taimama a inda aka rasa ruwan yin alwala ɗin. Kuma ba a yin sallah sai lokacinta ya shiga, duk wanda ya yi sallah kafin shigar lokacinta sallarsa ba ta yi ba sai inda shari'a ta amince da hakan.

Babu sallah ga wanda bai yi kabbarar harama ba, kuma kabbarar harama a tsaye ake yinta. Sannan kuma babu sallah ga wanda bai yi karatun Fatiha a cikinta ba kamar yadda hadisi ingantacce ya tabbatar, duk raka'ar da mutum ya yi bai karanta Fatiha a cikinta ba, to ba shi da wannan raka'ar sai ya sake yin wata raka'ar a madadinta.

Duk wanda ya mance ya rage wani aiki daga cikin ayyukan sallah, ko ya mance ya ƙara wani aiki daga cikin ayyukan sallah, to ba sallamewa ake a sako farko ba, ana gyarata ta hanyar yin sujjada biyu kafin sallama ga wanda ya rage wata sunnah ko sunnoni, ko a yi sujjada biyu bayan sallama ga wanda ya ƙara wani aiki. Za a sami cikakken bayani idan aka tuntuɓi malamai.

Sallolin farilla guda biyar ne a kowace rana, ga su ɗaya bayan ɗaya:

1. ASUBAHI: Ita kuma tana da raka'o'i biyu ne kacal, kuma ana karanta Fatiha da surah a cikinsu ne a bayyane, har ma an so a ɗan tsawaita karatu a cikin raka'o'inta fiye da na sauran sallolin. Duka wannan dai a taƙaice ne.

2. AZUHUR: Tana da raka'o'i guda huɗu, raka'o'i biyu na farko ana karanta Fatiha da Surah a asirce, sai a zauna a yi zaman tahiya, a miƙe a ciko raka'o'i biyun ƙarshe, su kuma ana karanta Fatiha ne kaɗai ba Surah, idan kuma aka mance aka karanta surah a cikinsu ba komai. Bayan an gama su sai a zauna a sake yin tahiya a yi sallama.

3. LA'ASAR: Ita ma raka'o'i huɗu take da su kamar na Azuhur ɗin can, kuma iri ɗaya ake yinta da yadda ake yin Azuhur ɗin.

4. MAGRIBA: Ita kuma raka'o'i uku take da su, raka'o'i biyun farko ana karanta Fatiha da surah a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, a miƙe a ciko raka'a ta uku, amma ita ana karanta Fatiha ce kaɗai a asirce, sai a sake zaman tahiya a yi sallama.

5. ISHA'I: Ita kuma raka'o'i huɗu take da su kamar na Azuhur da La'asar, sai dai bambancinta da su shi ne; raka'o'inta biyu na farko ana karatu a cikinsu ne a bayyane ba a asirce ba.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐁𝐀𝐘𝐀𝐍𝐈 GAME DA 𝐒𝐀𝐋𝐋𝐎𝐋𝐈 𝐁𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐍𝐀 𝐅𝐀𝐑𝐈𝐋𝐋𝐀

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Dan Allah a kara mana bayani sosai yadda ake salloli biyar na farilla.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaikumus-salam wa rahmatullah.

Akwai abubuwa uku da ake bukata kafin sallah:

1. Tsaftar jiki, tufafi, da wurin sallah

Allah Madaukaki Ya ce:

﴿وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ﴾

Tufafinka ka tsarkake su.” (Al-Muddathir: 4)

2. Yin alwala (ko tayammumi idan babu ruwa)

Nabi ya ce:

«لَا تُقْبَلُ صَلَاةٌ بِغَيْرِ طَهُورٍ»

Ba a karɓar sallah ba tare da tsarki ba.” (Muslim)

3. Shigar lokacin sallah

Allah Ya ce:

﴿إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا﴾

Sallah ta zama wajiba ga muminai bisa lokaci.” (An-Nisā’: 103)

Kuma babu sallah idan ba a yi takbīratul-ihrām a tsaye ba.

𝐌𝐔𝐇𝐈𝐌𝐌𝐀𝐍 𝐅𝐀𝐓𝐈𝐇𝐀

Nabi ya ce:

«لَا صَلَاةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ الْكِتَابِ»

Babu sallah ga wanda bai karanta Fātiha ba.” (Bukhari & Muslim)

Kowane raka’a dole ne a karanta Fatiha.

𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐍𝐂𝐄 𝐀 𝐒𝐀𝐋𝐋𝐀𝐇

Idan mutum ya rage wani aiki ko ya ƙara wani, ana gyara da Sujjadar Sahwi:

Idan an rage sunnah → a yi sujjada kafin sallama.

Idan an ƙara ba da gangan ba → a yi bayan sallama.

𝐒𝐀𝐋𝐋𝐎𝐋𝐈 𝐁𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐍𝐀 𝐘𝐀𝐔𝐌𝐀𝐍𝐂𝐄

1️ SALLAR ASUBAHI

Raka’o’i: 2

Karatu: Fātiha + surah a bayyane

An fi so a tsawaita karatu kaɗan.

2️ SALLAR AZUHUR

Raka’o’i: 4

Raka’o’i biyu na farko:

Fātiha + surah a asirce (ba sauti)

Zama ta farko (tashahhud) → a miƙe

Raka’o’i biyu na ƙarshe:

Fātiha kaɗai

A zauna a ƙarshe a yi sallama.

3️ SALLAR LA’ASAR

Irin tsarin Azuhur ɗaya ne: 4 raka’o’i, duka a asirce.

4️ SALLAR MAGRIBA

Raka’o’i: 3

Raka’o’i biyu na farko:

Fātiha + surah a bayyane

Zama (tashahhud) → a miƙe

Raka’a ta uku:

Fātiha kaɗai, a asirce

Zama ta ƙarshe → sallama.

5️ SALLAR ISHA’I

Raka’o’i: 4

Biyu na farko:

Fātiha + surah a bayyane

Biyu na ƙarshe:

Fātiha kaɗai a asirce

Tashahhud → sallama.

TAQAICE

Salloli biyar:

Asubahi – 2 raka’a, bayyane

Zuhur – 4, asirce

La’asar – 4, asirce

Magriba – 3, bayyane

Isha’i – 4, bayyane a farkon raka’o’i biyu

Post a Comment

0 Comments