Ticker

6/recent/ticker-posts

Abin Da Mata Suke Nufi Da Namiji A Cikin Maza

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ni mace ce wacce Allah ya sa zamana ina yinsa yawanci da matan Aure, Abin tambaya a nan shi ne naji kullim suna magana wannan namji ne wanan ba namji ba ne, toh dan Allah mai suke nufi da namiji a cikin maza dan Allah a banbantamin.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Kalmar Namiji a yaren malam bahaushe shi ne Kishiyar jinsin mace. Amma a wajen mata, idan kaji ance Namiji, to shi ne Wanda yake iya Sarrafa Matarsa kuma ya gamsar da ita a wajen Sirrinsu na Aure.

Mace an halicceta da buƙatar da Namiji Babu Makawa kowacce mace tana buƙatar taji komi ya yi mata daidai. Sai dai idan Bata samu ba.

Matsalar dai guda ɗaya ce, idan kaji ance Matar Aure tana yawan yiwa mijinta Fushi ko Bata Damu dashi ba irin yadda ya Damu da ita ba ko dan ya yi Tafiya bata damu da ya dawo ko kar ya dawo ba, kai wani lokacin ma tafi son ya yi tafiya ko kaji ance an kama matar Aure da Wani Namijin daban wanda ba nata ba suna Aikata Zina, ko Ana musu Mummunan zato ko Matar Aure ta kai mijinta kotu a raba Aurensu, Matsalar Bata wuce Wata Matsala guda ɗaya. Domin tatsuniyar gizo bata wuce ta koki.

Ya Kamata Mu sani cewar Ba Aure yana Nufin ciyar da mace abinci Sau ukku a rana bane. Sabida haka wani Namijin yana iya yin Alfahari cewar yana ciyar da iyalinsa abinci a rana sama da sau biyu ko sama da sau ukku. Kuma Sai kaga yana Alfahari da yin hakan. Amma a wajen mace hakan ba burgewa bane. Kai Asalima wannan ba shi ne gwarzontaka ba a wajenta ba. Gwarzontaka shi ne, ta jika daidai yadda take So!!!

Wani Namijin Kuma yana Alfahari ne idan ya dawo daga kasuwa zaizo da Kayan morewa Rayuwa, hakan yana ganin yana birge iyalinsa. Wallahi a Banza indai a wajen kebancewa baka iya komi. Sai kaji mace ta ce, "ban rasa ci ba, ban rasa sha ba, ban rasa sutura ba, Amma ke dai bari, Sai Abu ɗaya tak. ko da wasa idan kaji mace ta ambata haka Akanka! To wallahi ka gaggauta ka nemi mafita, Domin ka zama Sorry.

Wani Namijin kuma yana ganin shi Ɗan Gayu ne. Zaisa sutura kala-kala, Amma kuma Idan ya keɓance da iyalinsa Sai a hankali, domin kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba, Sabida kana da matsala guda ɗaya Tak. Sai taga cewar idan wani ne yasa wannan tufafin da kasa, zaifi kyawun gani ba kai ba, Sabida bashi da wata Nakasa a jikinsa.

Lallai maza ya kamata ku tashi tsaye ku nimi magani domin mata suna sa muku suna iri-iri badan komai ba sabida baku iya gamsar dasu a shimfida. Allah ta'ala yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

🕌 Amsar da ta dace – ba tare da wuce gona da iri ba

A harshen Hausa, namiji shi ne kishiyar mace.

Amma a bakin mata, idan sun ce:

“Wancan namiji ne a cikin maza”

to sukan nufi wasu halaye guda biyu:

1. Namiji mai kamala (mazaunin hankali da iko)

Wato halaye ba jiki ba.

Shi ne namiji:

Mai kula

— Yana da tausayi, kulawa, fahimtar zuciyar mace, ya san yadda ake mu’amala da taushi.

Mai ɗaukar nauyi

— Ba ya gudu daga alhaki, ba ya zubar da nauyin gida.

Mai gaskiya

— Ba ya yaudara, ba ya cin amanar matarsa.

Mai hakuri

— Ba mai tsawa ko zagi, ba mai fushi hanzari.

Wannan ita ce ma’anar farko. Mata suna girmama irin wannan namiji fiye da dukiya ko kaya.

2. Namiji mai kyawawan halaye a sirrin aure (ba fadar ɓatanci ba)

A nan ba ana nufin ƙarfin jiki ko tsiraici kai tsaye ba.

A ma’anar mata:

Namiji wanda ya san muhimmancin gamsar da mata

Ba dole ya zama jarumi ba, amma ya san:

• Muhimmancin wasa kafin saduwa

• Hakuri

• Kar ya yi gaggawa

• Kar ya maida kanta baya a hankali

• Ya saurareta

• Ya kula da bukatunta

Wannan ladabi ne, ba alfasha ba.

Namiji mai tsafta

Tsaftar jiki, baki, kamshi, takun hankali.

Namiji wanda bai raina mace ba

Ya san mace ta fi karfi da kalma mai dadi fiye da karfin hannu.

Saboda haka “namiji a cikin maza” baya magana ne akan girma ko tsawo ko wani abu makamancin haka: yana magana ne akan hankali + kulawa + ladabi + jin kai + tsafta + biyayya ga ka'idojin lafiya da aure.

Me ya sa mata ke kirga wasu maza “ba namiji ba”?

Su kan faɗi haka idan:

• Namiji ba ya kula da nauyin gida

• Ba ya da tausayi

• Ba ya sauraren matar tasa

• Mai fushi

• Mai zagi

• Mara tsafta

• Ko bai san muhimmancin jin daɗin matar aure ba

• Ko babu zumunci a tsakaninsu

Wannan ba nufin zagi bane. Nufin shi ne ba cikakken kamala ga matar tasa ba.

🕌 A shari’a kuma, namiji nagari shi ne:

قال الله تعالى

﴿ الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ ﴾

“Maza ne masu daukar nauyin mata.”

— An-Nisā’ 4:34

Babu “ƙaulaƙaula”. Shugabanci + tausayi + adalci.

Manzon Allah ya ce:

خَيْرُكُمْ خَيْرُكُمْ لِأَهْلِهِ

“Mafi alkhairinku shi ne mafi alkhairi ga iyalinsa.”

— Tirmidhi

Wannan shi mata ke kira “namiji a cikin maza.”

🧕 Saboda haka, abinda mata ke nufi shi ne:

Ba girman murya ba,

Ba doki ba,

Ba kaya ba,

Ba gidadanci ba.

Suna nufin namiji mai kamala, ladabi, kulawa da fahimtar mace – a rayuwar aure gaba ɗaya. 

Post a Comment

0 Comments