Abu ne sananne, Kalmar Shahada; "La'ilaha illal lahu" ita ce tushen Addinin Muslunci. Gaba daya Addinin Muslunci ya ginu ne a kan wannan tushe da asali. Don haka babu yadda za ayi mutum ya fahimci Addinin Muslunci bisa ingantacciyar fahimta har sai ya fahimci wannar kalma a bisa ingantacciyar fahimta.
Ma'anar wannar kalma;
"La'ilaha illal lah" ita ce; "Babu abin bauta bisa gaskiya da
cancanta sai Allah". Saboda Kalmar "ILAHU" ma'anarta ita ce;
"ABIN BAUTA". Allah ya ce:
قل يا أهل الكتاب تعالوا إلى كلمة سواء بيننا وبينكم ألا نعبد إلا
الله ولا نشرك به شيئا ولا يتخذ بعضنا بعضا أربابا من دون الله
"Ka ce: ya ku Ahlul Kitabi;
(Yahudawa da Kiristoci), ku zo mu hadu a kan wata kalma da za ta daidaita
tsakaninmu da ku; KADA MU BAUTA MA KOWA SAI ALLAH, KADA MU HADA SHI DA KOMAI A
CIKIN BAUTA, KUMA KADA SAHENMU SU RIKI SASHE A MATSAYIN UBANGIJI KOMA BAYAN
ALLAH".
Ibnu Jarir Al- Dabariy (ra) ya
ruwaito daga wasu daga cikin Salaf cewa; kalmar da ake nufi a nan ita ce:
Kalmar Shahada; "La'ilaha illal lahu". Daga cikinsu Abul Aliyah ya
ce:
"كلمة السواء: لا إله إلا الله"
Akwai ayoyi masu yawa da suke
bayanin ma'anar wannar kalma ta tushen Addini, daga ciki Allah ya ce:
وإذ قال
إبراهيم لأبيه وقومه إنني براء مما تعبدون (26) إلا الذي فطرني فإنه سيهدين (27) وجعلها
كلمة باقية في عقبه لعلهم يرجعون (28)
Ya ce:
فمن يكفر
بالطاغوت ويؤمن بالله فقد استمسك بالعروة الوثقى لا انفصام لها
Ya ce:
وما أرسلنا
من قبلك من رسول إلا نوحي إليه أنه لا إله إلا أنا فاعبدون
Ya ce:
وما لي
لا أعبد الذي فطرني وإليه ترجعون (22) أأتخذ من دونه آلهة
Ya ce:
وما أمروا
إلا ليعبدوا إلها واحدا لا إله إلا هو سبحانه عما يشركون
Duka wadannan ayoyin suna
tabbatar da cewa; ma'anar "ILAHU" ita ce: ABIN BAUTA.
Kai hatta Mushrikan Larabawa sun
fahimci ma'anar Kalmar shahada a bisa ma'ana ta hakika, Allah ya ce:
إنهم
كانوا إذا قيل لهم لا إله إلا الله يستكبرون (35) ويقولون أئنا لتاركوا آلهتنا لشاعر
مجنون (36)
Shi ya sa lokacin da Annabi (saw)
ya nemi su yarda da Kalmar "La'ilaha illal lahu", su bauta ma Allah
shi kadai sai suka ce:
أجعل
الآلهة إلها واحدا إن هذا لشيء عجاب (5) وانطلق الملأ منهم أن امشوا واصبروا على آلهتكم
إن هذا لشيء يراد (6)
Don haka ma'anar wannar kalma;
"La'ilaha illal lahu" ita ce; "Babu abin bauta bisa gaskiya da
cancanta sai Allah". Saboda Allah ya ce:
ذلك بأن
الله هو الحق وأن ما يدعون من دونه هو الباطل
* Amma abin mamaki da yawa daga
cikin musulmai ba su fahimci ma'anar wannar kalma a bisa ma'ana ta hakika ba.
Ga nan kadan daga cikin wadanda suka kuskure ma'ana ta hakika game da Kalmar
Shahada:
1. Sufaye masu Aqidar
"Wahdatul Wujud", wato Aqidar komai Allah ne, su suna fassara Kalmar
Shahadar ce da cewa: Babu wani abin bauta sai Allah. Ma'ana; duk wani abin da
ake bautawa Allah ne. Wanda ya bauta ma gunki ma Allah ya bauta, wanda ya bauta
ma Shehu Inyas shi ma wa Allah ya bauta. Wanda ya bauta wa Annabi Isa (as) shi
ma wa Allah ya bauta, wanda ya je kabarin wani shehi ko waliyyi ya bauta masa
shi ma wa Allah ya bauta, saboda babu wani abin da ake bautawa face Allah ne.
2. Ma'abota "Ilmul
Kalam"; Mu'utazilawa, Asha'ira, Maturidiyya da makamantansu. Suna fassara
Kalmar "ILAHU" da cewa;
القادر
على الاختراع
Wai- mai iko a kan kirkiran
halitta. Don haka ma'anar "La'ilaha illal lahu" a wajensu, ita ce:
"Babu mai iko a kan kirkiran halitta sai Allah".
3. 'Yan Kungiyar Ikhwanul
Muslimuna, su kuma suna fassara Kalmar Shahadar ce da cewa; BABU HUKUMA SAI TA
ALLAH.
Sayyid Qutub a cikin Tafsirinsa
"Fiy Zilalil Qur'an" ya tabbatar da haka a wurare da dama, daga ciki
ya ce:
«لا إله
إلا الله» كما كان يدركها العربي العارف بمدلولات لغته: لا حاكمية إلا لله، ولا شريعة
إلا من الله، ولا سلطان لأحد على أحد، لأن السلطان كله لله.
Kuma du ya ce:
ومعنى:
«لا إله إلا الله» .. كانوا يعرفون أن الألوهية تعني الحاكمية العليا
Ya ce:
كانوا
يعلمون أن: «لا إله إلا الله» ثورة على السلطان الأرضي
Ya ce:
أن الإسلام
هو أولا إقرار عقيدة: لا إله إلا الله بمدلولها الحقيقي وهو رد الحاكمية لله في أمرهم
كله، وطرد المعتدين على سلطان الله بادعاء هذا الحق لأنفسهم.
Ya ce:
وشهادة
أن لا إله إلا الله، أي إفراده بالحاكمية في حياتهم الأرضية
Wannan ya sa suke ganin shirka a
wajensu shi ne shirkan siyasa, saboda Tauhidi shi ne Tauhidin Hukuma. Wannan ya
sa suke mutuwa a kan kokarin kawar da gomnatin zalunci. Tun kafuwarsu har zuwa
yau a kan abin da suke ta gwagwarmaya kenan, alhali Manzannin Allah da Annabawa
sun yi yaki ne a kan tabbatar da Tauhidin Bautar Allah da kawar Shirka ma Allah
a cikin bauta.
** Abin lura shi ne:
Fahimtar hakikanin ma'anar Kalmar
Shahada da riko da ita, da tafiya a kanta, da aiki da ita, tare da abin da take
hukuntawa, shi ne asali da tushen tafiya a kan hanya madaidaiciya, kuskure a
fahimtar ma'anar kalmar kuwa, shi ne asali da tushe na kaucewa ga hanya
madaidaiciya; hanyar Annabawa da Siddiqai da Shahidai da Salihan bayi.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.