Ticker

6/recent/ticker-posts

Sai Dai Wata Ce Can Daban ‘Yar Mammy Market, Ba Matan Annabi (SAW) Ba

Mutane da yawa sun ɗauka Shi'anci shi ne zagin Sahabbai kaɗai, alhali Shi'anci a bisa haƙiƙa, shi ne kishiyantar Addinin Muslunci.

Don haka ba abin mamaki ba ne idan an danganta mutum ga Shi'anci, sai kuma a ji yana ɓatanci ga Hadisan Annabi (saw); Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim, yana cewa; a cikinsu -wai- an ruwaito Matar Annabi (saw) ta fito tumɓur sai bireziya.

Ko kuma ya ce: Matan Annabi (saw) suna yawo kamar ƴan mammy market.

Yanzu miye abin mamaki don ka ji wanda ake cewa; dan shi'a ne, amma yana ƙaryata Azaban Ƙabari?

Aƙidun Mu'utazilawa fa gaba ɗaya Ƴan Shi'a sun ɗiba sun juye a cikin jakarsu ta Aƙida.

Shi Addinin Shi'a, Addini ne da duk wani Zindiƙi mai son rusa Addini yake shiga cikinsa, ya laɓe a bayansa yana ɓarna da sunan Addini. Babban misali a kan haka shi ne Abdullahi ɗan Saba'i. Wannan mutumi Bayahude ne, ya shiga Muslunci a matsayin Munafuki, ya fake da shi'ancin son Aliyu (ra), ya shigo da Aƙidun Yahudanci cikin al'ummar Musulmi.

Bayan haka ka ɗauki Sarakunan Daular Ubaidiyya, daular da aka kafa a arewacin Afirka da ƙasar Misra, suka fake da shi'anci, suka danganta kansu ga Fatima (ra), har ake kiran daular tasu da sunan Daular Faɗimiyya, alhali babu irin zindiƙanci da ilhadi da ɓarnar da ba su yi ba. Har sai da suka ba ma sarakunan nasu matsayin Allah.

Kuma ka bibiyi tarihin waɗanda suka shahara da zindiƙanci, za ka samu galibi sun fake da shi'anci da ƙaryar son Ahlul Baiti.

Saboda haka shi Addinin Shi'a haka yake, tunga ne na mabarnata da miyagu da zindiƙai da mulhidai. Mutum maƙiyin Addini, maƙiyin Allah da Manzonsa, mai nufin lalata Alƙur'ani da Sunna da Shari'ar Allah sai ya zo ya nuna shi Ɗan Shi'a ne, yana son Aliyu (ra) da Ahlul Baiti, sai kuma ya yi ta ɓarna don ya rusa Addini.

To, amma sai dai abin da irin waɗannan zindiƙan ba su sani ba, ƙarya fure take ba ta ƴaƴa. Ba yau aka fara faɗa da Addini ba. Da a ce; zindiƙai za su ci nasara a kansa da bai iso gare mu ba. Amma Allah ya yi alƙawarin zai cika haskensa ko da kafirai sun ƙi.

Don haka karanta Hadisan Bukhari da Muslim da gaskata su yanzu zamu fara, tare da ƙudurta cewa; babu littafi mafi inganci a Muslunci - bayan Alƙur'ani - sai Sahihul Bukhari, sai kuma Sahihu Muslim.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments