Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka'idar Sanin Bidi'a Ta Aiki

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya ya ce:

((ومعلوم أن كل ما لم يسنه ولا استحبه رسول الله صلى الله عليه وسلم ولا أحد من هؤلاء الذين يقتدي بهم المسلمون في دينهم فإنه يكون من البدع المنكرات ولا يقول أحد في مثل هذا إنه بدعة حسنة؛ إذا البدعة الحسنة - عند من يقسم البدع إلى حسنة وسيئة - لا بد أن يستحبها أحد من أهل العلم الذين يقتدى بهم ويقوم دليل شرعي على استحبابها وكذلك من يقول: البدعة الشرعية كلها مذمومة لقوله صلى الله عليه وسلم في الحديث الصحيح: {كل بدعة ضلالة} ويقول قول عمر في التراويح: " نعمت البدعة هذه " إنما أسماها بدعة: باعتبار وضع اللغة. فالبدعة في الشرع عند هؤلاء ما لم يقم دليل شرعي على استحبابه. ومآل القولين واحد؛ إذ هم متفقون على أن ما لم يستحب أو يجب من الشرع فليس بواجب ولا مستحب؛ فمن اتخذ عملا من الأعمال عبادة ودينا وليس ذلك في الشريعة واجبا ولا مستحبا فهو ضال باتفاق المسلمين. وقصد القبور لأجل الدعاء عندها رجاء الإجابة: هو من هذا الباب فإنه ليس من الشريعة: لا واجبا ولا مستحبا؛ فلا يكون دينا ولا حسنا ولا طاعة لله ولا مما يحبه الله ويرضاه ولا يكون عملا صالحا ولا قربة ومن جعله من هذا الباب فهو ضال باتفاق المسلمين)).

مجموع الفتاوى (27/ 152)

Abu ne sananne cewa; duk abin da Manzon Allah (saw) bai sunnanta shi ko kyautata shi ba, kuma babu wanda ya kyautata shi cikin wadanda Musulmai suke koyi da su cikin addininsu, to lallai wannan abu zai kasance cikin bidi'o'i abin ƙyama. Babu wanda zai ce irin wannan yana cikin bidi'a mai kyau. Saboda ita bidi'a mai kyau - a wajen mai kasa bidi'a zuwa mai kyau da mummuna - kafin a ce mata mai kyau ce dole sai an samu wani Malami cikin wadanda ake koyi da su ya ce mai kyau ce, bayan an samu dalili na Shari'a da ya yi nuni a kan Mustahabbancinta.

Haka mai cewa: kowace bidi'a a Shari'a abin zargi ce, saboda fadin Annabi (saw): "Kowace bidi'a ɓata ce", da faɗin Umar (ra) a game da Sallar Tarawihi: "Madalla da wannar bidi'a", ya kira ta da sunan bidi'a ce bisa ma'anarta ta Luga ba bisa ma'ana ta Shari'a ba. Saboda bidi'a bisa ma'ana ta Shari'a a wajen wadannan Malamai ita ce; duk abin da ba a samu dalili na Shari'a ya zo da Mustahabbancinsa ba. Amma duka maganganun biyu suna komawa ne ga abu daya, saboda dukkansu sun yi ittifaki a kan cewa; duk abin da Shari'a ba ta zo da Mustahabbancinsa ko wajabcinsa ba to ba wajibi ba ne ba kuma ba Mustahabbi ba. Don haka duk wanda ya riƙi wani aiki daga cikin aiyuka a matsayin ibada, alhali a Shari'a shi ba wajibi ba ne ko Mustahabbi to ɓatacce ne bisa ittifakin al'ummar Musulmi.

Saboda haka, tashin mutum takanas ya tafi kabarbura don yin addu'a a wajensu, da fatan yin addu'ar a wajen nasu abin amsawa ne, yana daga wannan babi na bidi'a, saboda hakan ba ya cikin Shari'a, a matsayin Mustahabbi ko wajibi. Don haka ba zai taɓa zama Addini ba, ko ya zama wani abu mai kyau ko ya zama aikin da'a ma Allah, ko ya zama cikin abin da Allah yake so ya yarda da shi. Kuma ba zai taɓa kasancewa aiki na kwarai ba, ko aikin ibada. Duk wanda ya sanya shi cikin aikin ibada to shi ɓatacce ne bisa ittafaƙin al'ummar Musulmi)).

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments