BISMIL LAHIR
RAHAMANUR RAHIM,
WA SALLALLAHU
ALAL NABIYYUL KHARIM
1. Fa
bismillahi na fara,
Bi hamdillahi
nai shukura,
A farko har
zuwa ƙara,
Ya Arrahamanu
na yi bara,
Ka min tanyo in
ko ida.
2. Wa
sallallahu Ya Allah,
Alal Mukhtari
wal Ala,
Ma’al Ashabi ya
Allah,
Ka za ma’a
Auliya’allah,
Madad dahri, bi
la hadda.
3. Yo ga iska
ta na rugi,
Ta yo laftu na
‘yan dangi,
Su na tsumuwa
ta na gangi,
Hamada ba ta
kai wargi,
A gare ta kai a
har abada.
4. Begen iskar
hamada yau,
Ya sa ni na
barkace ha i yau,
In ta taso
kamar ma yau,
In tashi in hau
bisanta ayau,
Ta kai ni Dubai wurin Sanda.
4. Begen iskar
hamada yau,
Ya sa ni na
barkace ha i yau,
In ta taso
kamar ma yau,
In tashi in hau
bisanta ayau,
Ta kai ni Dubai wurin Sanda.
5. Da na ga fa
girgije a sama,
Ya na tafiya da
sawunsa,
Sai in ji kamar
na hau kansa,
Ya kai ni gusun
ga Farfesa,
Mu gaisa can
Dubai abada.
6. Alalo-alalo
taɓakaka,
Zumaina ‘yan
uwa barka,
Yaya bazara da
albarka,
Fatan hairi da
albarka,
A gareku tutur
a har abada.
7. Ina ka ke ne
Professor,
A Sarkinfada
Farfesa,
Fa na leƙo mu ɗan gaisa,
Alla gafarta na
ce ma Sir,
Fatan ka kwan ƙalau Sanda.
8. Ina
tuntuntuni kanka,
A kullum zan yi
hirarka,
A zuci na ɗarsa begenka,
Ƙafa ta
za ta zo gunka,
Ido na yaushe
zai tar da.
9. Nisa ga shi
yai illa,
Zukata ga shi
sun ƙulla,
Alaƙa mai
dubun galla,
Mai dugunzuma
dukka hankulla,
Wayyo Malam Prof. Sanda.
10. Arwahu su
na cikin shauƙi,
Zukata na
hawan-na-ƙi,
Ana ta
ruguntsumin yaƙi,
A fagen fama
jiki yaƙi,
Zumunta za a
dai sada.
11. Jama’a fa
ku daina inkari,
A kan na yo
yabon bahari,
Prof Faruku kui
nazari,
Darajarsa cikin
dubu da ɗari,
Kaɗan ciki ba ni kardada.
12. A farko ga
sani gunsa,
Don yai ilimi
na dininsa,
Balle fa na
zamanin nasa,
Ya danganta ga
Farfesa,
Darajar ƙarshe ya kai Sanda.
13. Malam ya
san Samarƙandi,
Isa Guji da Ɗanwardi,
Ya na raddi ga
mai liddi,
Ya shirya tsaf
da kyankyandi,
Ya san
funfunfuni Sanda.
14. Ya zam
bahari a gun ilmu,
Mu runtuma duk
ya sashe mu,
Fagagen ilmu
zai bamu,
Ƙwararren
duk ƙishirwarmu,
Yau za ta gushe a gun Sanda.
15. Sannan ga
kyan mu’amilla,
Haƙuri
jarinsa ne walla,
Bin dattawa ya
mai galla,
Ga son Manzo ya
na salla,
Ai dole su bar
ka alfanda.
16. Karimi ga
karimanci,
Ba ya jito da
zalunci,
Ba ya sabga ta ƙasƙanci,
Ba ya son mai ƙicen
zuci,
Tilas na yabe
ka ai Sanda.
17. Malam zai
ba ka mamaki,
A sabaucin ƙan da
kai, kirki,
Bai girma kai
da jin mulki,
Kuma ya fa fito
gidan mulki,
Ɗan
sarki danganen fada.
18. Tafi maƙasau
irin kirki,
Ka fanshi dubu
fa jan zaki,
Ina kura ina
shaki,
Ku bar hanya ku
bar tafki,
Ga zaki ya taho
Sanda.
19. Su
‘yartsaddi a ɗau
hanya,
Biri da Dila a
bar hanya,
Su ɗan akuya a ɗau hanya,
Ku ce dirwa ta
sau hanya,
A yau ko ran ta
ta sai da.
20. Lafiya
bango na al’uma,
Lafiya Santo a
gogarma,
Lafiya mai sha
da al’uma,
Lafiya mai
danganen girma,
Ga garnaƙaƙi
bison fada.
21. A min afuwa
fa Farfesa,
Tabbas laifi fa
na yi sa,
Ka na ta kira
mu ɗan gaisa,
Ba ka samun
waya ta Sir,
Ina tuba Prof.
Sanda.
22. Da ga nan
ka ƙudurce
yin niyya,
Ka zo ka ishen
a Zawiyya,
A tirƙashi
ina kunya,
Ka zo ban zo ba
ba kunya,
Ina girmanka na
zubda.
23. Ina ta
kiran waya nan ma,
Ta na kashe ba
ta ko cimma,
Sai nai aniya
na ɗau himma,
Ta zan zo gunka
nai azama,
In sadu da kai
Prof Sanda.
24. Fa na leƙo
gidan na ka,
Mu gaisa dan in
ɗan ganka,
Malam Ahmad ya
ce ba ka,
Nan fa ka na
Dubai hakka,
Sai nai kewar
ka alfanda.
25. To yau na
zo ni har fada,
Mu yo taɗi cikin fada,
In kurɓi dawo furar fada,
Da alkakin
cikin fada,
Da funkason
mutan fada.
26. In tauna ƙashi
in ko tsotse,
In sha madara
da an tatse,
In kwashi tuwo
in ko gyatse,
In lashi zuma
na ma katse,
Garar baƙi fa
sai fada.
27. Da na ƙare na
hau doki,
Fari fat ai
kilin yaƙi,
Na yo sukuwa na
ja burki,
Nai jinjini ga ɗan sarki,
Malam kuma ginshiƙin fada.
28. Bararren ɗa na mai fada,
Karimin ‘yan
cikin fada,
Wata ran kai ne
cikin fada,
Irin ku a ke biɗa fada,
Takawa sannu
alfanda.
29. Tafi
gindigirin icen gamji,
Ana sara ya na
gumji,
Ya na tofo ya
na rauji,
Bahagon gulbi
cike daji,
Ɗan
sarki tarsashin fada.
30. Kasankama
mai shirin yaƙi,
Kai ar ga ɗumfaman yaƙi,
Ya ɗauro janjamin yaƙi,
Ga kansakulan
fita yaƙi,
Ƙi-garaje
jarumin fada.
31. Nagarta ka
ji tsaninsa,
Zumunci ka ji
takensa,
Haƙuri
kuma ka ji jarinsa,
Son Manzo am
muradinsa,
A kullum kai a
har abada.
32. Sannan
Malam fasihi ne,
Ya na waƙa ƙwararre
ne,
Lungu saƙonta
ya gane,
A take yanke
zai aune,
Ya tsara ba
batun ganda.
33. Malam bai
ma tsaya nan ba,
Bai ƙyale
wallafofi ba,
Ba zai kuma
kasa sharhi ba,
Na littafi da
waƙa
ba,
Manzon Adabi da
al’ada.
34. Gogan
harshe a Larabci,
Wata rana sai
yai da Turanci,
In ya so yai da
Hausanci,
Hirarsa gami da
kakaci,
Ga taɗoɗinsa na bada.
35. Fa Farfesa
taƙiyyi
ne,
Yakana ƙana’a hali nai ne,
Tsantseni na sa
mun gane,
A dattako
sananne ne,
Tsabi’u ba ya
alfanda.
36. Ya na son
Annabin Allah,
Da iyalan
Annabin Allah,
Da sahabban
Annabin Allah,
Da sharifai
Auliya’allah,
Bai inkarinsu
alfanda.
37. Bugu-ƙari
Professor,
Ya leƙa ƙasa-ƙasa ai
Sir,
Ya je Landan fa
Farfesa,
Ya je shi Dubai
Professor,
Ya na koyar da
su Sanda.
38.Ɗalibai
nai Larabawa ne,
Da Larabci ya
ke aune,
Ya koyarsu su
na zaune,
Darussan
Ingilishi ne,
Ya ke Tafinta
alfanda.
39. Su na ta
cika da mamaki,
Baƙar
fata da mamaki,
Ya na Arabiyya
ba miki,
Su kumma su na
sakin baki,
Ajaban ajaban
li S.Fada.
40. Ga ‘yar waƙar da
ni nai ta,
Ta ban haƙuri a
dube ta,
Ko ba wazani a
karɓe ta,
Ko ba tsari a
amshe ta,
Manufa haƙuri in
dai bada.
41. Da fatan za
a yafe ni,
A min afuwa a
karɓe ni,
A gafarta a
dube ni,
A ce lale a
tarbe ni,
Ya Farfesanmu
S. Fada.
42. In ka yafe
Professor,
Ina fa jiran ka
ban amsa,
Da waƙa za
ka ban amsa,
Don kai ma
sha’iri ne Sir,
Na gani na faɗa
a har abada.
43. Waƙa wa
ne talalako,
Wa ne banzar
gari soko,
Adabi a cikin
ta lo-loko,
Duba a cikin
Tabarkoko,
Da zugagen
sha’iri ad da.
44. Kyawun waƙa da ‘yan amshi,
Jigo shi ne fa
harsashi,
Sa amsa-amo ta
yo ƙamshi,
Adon harshe fa
ke ƙunshi,
Ga waƙa tai
yi tsaf abada.
45. Cikar waƙa ayo
ramzi,
Adon waƙa kwa
ilgazi,
Mafi sauƙin ta
kan rajazi,
Waƙa fa
ta kan zamo kanzi,
Taskar harshe
da al’ada.
46. Waƙa fa
ta na biɗar haddi,
Lafuzanta ya
zam akwai ƙaidi,
Ɗangwayenta
a kan adadi,
Saƙonta
tsatsaf fa ba liddi,
Ku jiya ku
sha’irai abada.
47. Jigon waƙa ya
zam siddi,
Na hawanta zuwa
fagen rushdi,
Salon sha’ir ya
zam lifidi,
Awo ƙaiminta
kan adadi,
Na ƙafafunta
a har abada.
48. Na kai ga
sukwa fa na ƙare,
Zamiyar ma nai
ta ta ƙare,
Kama-zuru na ja
na tsare,
Na kai muri fa
na ɗaure,
Waƙata
tai cikar idda.
49. Ƙure
doki fa ingarma,
Gano haske na
bantarma,
Ga zirnaƙo da
gwazarma,
Dodo na ruwa fa
dangarma,
Allura ta haƙe
garma,
Kafin haɗiya akwai loma,
Batun nan banda
mai ganda.
50. Salon waƙa na ɗan tsarma,
Ga masu ƙulafucin
nema,
Waƙa
tamkar ya gogarma,
Basiɗine ƙure noma,
Ku zo ku sha’irai ku gwada.
51. Tammat na
kammale waƙa,
Yaumal
Thulatha’a nai waƙa,
A Rabi lauwal
ta kai matuƙa,
Kwana ashirin
biyat liƙa,
Ka samu cikon
fitar adada.
52. Af to saura
batun ramzi,
Fi HAMTASHU (همتش)karɓi ga ramzi,
Hijirar Manzo
Rasulu huzi,
Kai hauzi, sai
ka nem hazzi,
Buga kulkin sai ka sam adada.
53. A hisabin
baitukan nata,
WAISUN (ويص) adadinsu to kwata,
Larabawa kui
iwal nata,
Da Hausa na zo
da waƙenta,
Don tai sauƙi a
gun hadda.
54. Bagagiji ne
fa sunanta,
Babbar laya
kirarinta,
Ga Farfesa na
tsaro ta,
‘Yan Hausa ku ɗau
nazar nata,
Ku rabe ƙaura da kau tsada.
55. A batun
waye ya tsaro ta,
Usman Nagado ya
shiryo ta,
Ɗalibin
Shehu Ƙani
yai ta,
Gusawi gun
zuciya likita,
A Gwale ya yi
ta ba ganda.
56. In ka so
sai ka sa harufa,
Kai babbaƙu
farfaru ka ɗafa,
Inu (ع) da Ca (ث) da Mim (م) ka ɗafa,
Alu-ja (ا) Nun (ن) haɗa ka rufa,
To ce Usman aje
ganda.
57. Ana kwana
ana tashi,
Ana ta ragar mu
numfashi,
Mu na daɗa ƙara alwashi,
Kwatsam rai zai
halin na shi,
Mutuwa ta ishe mu har fada.
58. Mu yo
saunar biɗar tuba,
Gaban mutuwa ta
zo arba,
Mu riski bukin
dakan gumba,
Mu hanzarta
gurin Rabba,
Mu tuba a nan mu bar ganda.
59. Salati zan
a ƙarshenta,
Ga Ɗahe
mai hana ni ɓata,
Da Alayensa sun
kuɓuta,
Da Sahabbai
kunzumi kwata,
Da salami ban
bari abada.
60. Allah na roƙi
fatana,
Nunan Manzo
Ma’aikina,
Shahada ran
fitar raina,
Ta zam furuci
na bakina,
Ka min tanyo in
ko ida.
TAMAT
(M) Usman
Nagado (II)
Bulangu86@gmail.com
Talata, 25-
Rabi al-auwal, 1445 (H).
10
Oktoba, 2023. (M)

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.