Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ya Sa Suke Jin Haushin Ibnu Taimiyya Ne?

Ibnu Taimiyya ya zo ne a lokacin da Falsafa ta cika ta batse.

"Ilmul Kalam" ya tumbatsa ya ɓaci, har ya rikiɗe ya koma Falsafa tsantsa.

Sufanci ya haɓaka har ya koma ilhadi da ittihadi.

Shi'anci ya gawurta har ya canza ya koma shirka da hululi.

A lokacin Ibnu Sina ya gama ɓarna!

Ibnu Arabiy ya gama rusa Addini.

Al-Raziy ma ya zo ya kulle ƙofa, ana ganin babu ya shi.

Ibnul Mudahhar al-Hilliy shi ma ya gama fasadinsa.

Wannan yanayi Ibnu Taimiyya ya zo ya samu, sai kuwa ya hau aiki, ya rinƙa ragargazansu da hujja da ilimi da dalili na Nassi da hankali ɗaya bayan ɗaya. Duk sai da ya gama rushe shubuhohinsu da ɓarnarsu da jahilcinsu da ilhadinsu. Ya raya hanyar Annabawa da Manzanni na riƙo da Wahayi bisa yadda Muminan farko suka fahimta.

To wannar ɓarna da Ibnu Taimiyya ya yi wa Bidi'a, ya jijjiga rukunanta, ya ƙwanƙwashi kawunan jagororinta, shi ne har yau abin ya tsaya musu a wuya.

Shi ya sa a yau, kowa a cikinsu a kan Ibnu Taimiyya haushinsa yake ƙarewa. Duk da cewa Malamai masu hankali a cikinsu, za ka ji suna cewa: Ibnu Taimiyya Malami ne, babu mai shakka a kan faɗin iliminsa da ƙarfin hujjarsa, amma sai dai mun saɓa masa a wasu Ijtihadodinsa...

Amma fa har yau an kasa tinkaran Ijtihadodin nasa a ilmance!

In ka san wannan ba za ka yi mamakin taron dangi a kan Ibnu Taimiyya ba.

Wannan ya sa ƙawancen ƙungiyoyin bidi'a a kan Ƴan Salafiyya ba zai taɓa ƙarewa ba. Saboda suna yaƙi da duk Manhajin da ya saɓa na Annabi da Sahabbansa da mabiyansu.

Ibnu Taimiyya Kai Kaɗai Gayya!

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments