Ticker

6/recent/ticker-posts

Shubuhar 'Yan Shi'a Game Da Aliyu (RA)

Duka karerayin 'Yan Shi'a a kan imamancin Imamansu 12 sun kitsa su ne a kan Hadisin "Muwalati", wanda Annabi (saw) ya fade shi a rana mai kamar ta yau, wato ranar 18 ga Zul-Hijja, a Ghadeer Khum, a kan hanyarsa ta komawa Madina daga Aikin Hajji.

Wannan Hadisin ya tabbata, Imamu Tirmiziy ya fitar da shi, amma sai dai 'Yan Shi'a sun juya ma'anarsa kamar yadda Yahudawa suke juya ma'anonin maganar Allah.

Shi ya sa Imamul Baihaqiy ya ruwaito da Isnadinsa daga Rabee'i Almajirin Imamu Shafi'iy ya ce:

"سمعت الشافعي يقول في معنى قول النبي صلى الله عليه وسلم لعلي بن أبي طالب رضي الله عنه: «من كنت مولاه فعلى مولاه» يعني بذلك ولاء الإسلام. وذلك قول الله تعالى: {ذلك بأن الله مولى الذين آمنوا وأن الكافرين لا مولى لهم}.

وأما قول عمر بن الخطاب لعلي: «أصبحت مولى كل مؤمن» يقول: ولى كل مسلم".

مناقب الشافعي للبيهقي (1/ 337)، الاعتقاد للبيهقي (ص: 355)، تاريخ دمشق لابن عساكر (42/ 238)

"Na ji Shafi'iy yana cewa; ma'anar fadin Annabi (saw) ga Aliyu bn Abi Dalib (ra) {Duk wanda na kasance Maulansa to Aliyu ma Maulansa ne}, yana nufin jibinta ce ta Muslunci. Wannan kuwa shi ne ke cikin fadin Allah Madaukaki:

{ذلك بأن الله مولى الذين آمنوا وأن الكافرين لا مولى لهم}

"Hakan saboda Allah shi ne majibincin wadanda suka yi imani, kafirai kam ba su da majibinci".

Amma fadin Umar bn Khaddab (ra) ga Aliyu: "Ka wayi gari Maulan kowane Mumini", yana nufin Majibincin kowane Mumini, (wato masoyi mai taimako)".

Haka Ibnu Asakir ya ruwaito ma'anar wannar kalma daga babban Malamin Harshen Larabci Ibnul A'arabiy inda ya ce:

"المولى المالك وهو الله والمولى ابن العم والمولى المعتق والمولى المعتق والمولى الجار والمولى الشريك والمولى الحليف والمولى المحب والمولى اللوي والمولى الولي ومنه قول النبي (صلى الله عليه وسلم) (من كنت مولاه فعلي مولاه) معناه من تولاني فليتول عليا.

قال ثعلب: ...ولكنه من باب المحبة والطاعة ويدل على أن المولى والولي المحب".

تاريخ دمشق لابن عساكر (42/ 238)

"Maula shi ne mamallaki, kuma shi ne Allah. Kuma Maula shi ne Dan Baffa, kuma wanda ya 'yanta bawa, kuma bawan da aka 'yanta, kuma makobci, kuma abokin tarayya, kuma halifi, kuma Masoyi, kuma Majibinci, daga haka akwai fadin Annabi (saw): {Duk wanda na kasance Maulansa to Aliyu ma Maulansa ne}, ma'ana; duk wanda ya jibince ni to ya jibinci Aliyu.

Tha'alab ya ce:.... Wannan a babin soyayya da da'a ne, yana nuni ga cewa; Maula da Waliyyi shi ne Masoyi".

Saboda haka, Bidi'ar Rafidha 'Yan Shi'a ta ginu ne a kan juya maganar Allah da Manzonsa (saw) da canza ma'anar abin da suka fada, kamar yadda Yahudawa suke yi. Da ma Malam Bahaushe ya ce: Barewa ba za ta yi gudu danta ya yi rarrafe ba!

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments