Hadisin "Muwalaati", shi ne Hadisin da 'Yan Shi'a suke karyar a cikinsa Annabi (saw) ya nassanta Khalifancin Aliyu (ra) a Ghadir Khum, alhali Hadisin ba Nassi ba ne a kan haka.
Imamul Baihaqiy ya yi bayani a
kan haka inda ya ce:
"وأما حديث الموالاة فليس فيه - إن صح إسناده
- نص على ولاية علي بعده، فقد ذكرنا من طرقه في كتاب الفضائل ما دل على مقصود النبي
صلى الله عليه وسلم من ذلك وهو أنه لما بعثه إلى اليمن كثرت الشكاة عنه وأظهروا بغضه
فأراد النبي صلى الله عليه وسلم أن يذكر اختصاصه به ومحبته إياه ويحثهم بذلك على محبته
وموالاته وترك معاداته فقال: «من كنت وليه فعلي وليه».
وفي بعض
الروايات: "من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه".
والمراد به ولاء الإسلام ومودته، وعلى المسلمين أن يوالي بعضهم بعضا ولا يعادي بعضهم
بعضا وهو في معنى ما ثبت عن علي رضي الله عنه أنه قال: والذي فلق الحبة وبرأ النسمة
إنه لعهد النبي الأمي صلى الله عليه وسلم إلي «أنه لا يحبني إلا مؤمن ولا يبغضني إلا
منافق».
وفي حديث
بريدة شكا عليا فقال النبي صلى الله عليه وسلم أتبغض عليا؟ فقلت: نعم، فقال: لا تبغضه
وأحببه وازدد له حبا، قال بريدة: فما كان من الناس أحد أحب إلي من علي بعد قول رسول
الله صلى الله عليه وسلم".
الاعتقاد
للبيهقي (ص: 354 - 355)
"Amma Hadisin
"Muwalati" -in Isnadinsa ya inganta- babu Nassi a cikinsa a kan
Khalifancin Aliyu (ra) kai tsaye bayan Annabi (saw),,, saboda abin da yake nuni
a kan manufar Annabi (saw) a Hadisin shi ne; lokacin da ya aika Aliyu (ra)
Kasar Yaman koke-koke sun yawaita a kan Aliyu (ra) daga wasu mutane, har suka
bayyana masa kiyayya, sai Annabi (saw) ya so ya ambaci falalarsa da soyayyarsa
gare shi, kuma ya kwadaitar da mutane a kan sonsa da jibintarsa da nisantar
adawa da shi, sai ya ce: {Duk wanda na kasance masoyinsa to Aliyu ma masoyinsa
ne}.
A wasu riwayoyin Hadisin: {Duk
wanda na kasance majibincinsa to Aliyu ma majibincinsa ne, ya Allah ka jibinci
wanda ya jibince shi, ka yi adawa da wanda ya yi adawa da shi}.
Abin nufi da jibinta a nan shi ne
jibinta ta Muslunci da soyayyarsa, saboda wajibi ne a kan Musulmai sashensu ya
jibinci sashe, (ya so dan uwansa Musulmi ya taimake shi), kar sashe ya yi adawa
da sashe, wannan kuwa shi ne ma'anar abin da ya tabbata daga Aliyu (ra) a
fadinsa:
"Na rantse da wanda ya tsaga
kwaya, ya halicci dabba, lallai Annabi (saw) ya yi mini alkawarin cewa:
{Lallai ba mai sona sai Mumini,
kuma babu mai kina sai Munafuki}".
Haka ya zo a Hadisin Buraida
(ra), ya kawo karar Aliyu (ra) sai Annabi (saw) ya ce masa: {Shin kana kin
Aliyu?}. Sai ya ce: Eh. Sai Annabi (saw) ya ce: {To kar ka ki shi, ka so shi,
ka kara sonsa}. Sai Buraida ya ce: Bayan Manzon Allah (saw) ya fada mini haka,
babu wani mutum da na fi so kamar Aliyu".
Saboda haka matsalar Rafidha ita
ce cutuka guda biyu; jahilci da son zuciya.
Da a ce suna da ilimi da sun san
cewa; Hadisin a kan son Aliyu (ra) yake magana ba a kan nada shi Khalifa ba,
kamar yadda shi Aliyun (ra) da kansa ya yi bayani. Kuma da a ce suna son
gaskiya da sun karbi bayani na ilimi da ake musu, ba su doge a kan son zuciya
ba.
Ya Allah ka mana tsari da jahilci
da son zuciya.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.