Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Sufaye Da Asha'ira Da Maturidiyya Ahlus Sunna Ne?

Sunan "Ahlus Sunnati wal Jama'a" suna ne da yake dauke da ma'ana ta Shari'a, ba suna ne fanko maras ma'ana ba. Don haka sunan ba ya dacewa sai da wanda ma'anar sunan ta tabbata a tare da shi.

Ahlus Sunnati wal Jama'a su ne Sahabban Manzon Allah (s.a.w), su ne "Jama'a",  wadanda suke kan tafarkin Qur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w), sai kuma wadanda suka bi tafarkinsu cikin Tabi'ai da mabiyansu har zuwa yau. Don haka duk wanda ba a kan tafarkin Sahabbai yake ba, to ba Ahlus Sunna ba ne, ko da kuwa ya fi kowa ikrarin cewa; shi ne Ahlus Sunnati wal Jama'a kawai.

Sahabban Annabi (s.a.w) sun kasance a bisa tafarkin da Annabi (s.a.w) ya dorasu a kansa, har ya koma ga Ubangijinsa ya barsu suna kan wannan tafarki, ba su canza ba. Haka mabiyansu suka cigaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa yau babu canji.

Tun zamanin Sahabbai aka fara samun wadanda suka rabu da wannar Jama'a, inda aka fara samun Khawarijawa suka fita daga al'ummar Musulmi suka dauki makami a kanta. Haka aka samu 'Yan Shi'a suka ware, bayansu aka samu 'Yan Kadariyya, sai kuma Murji'a. Duka wadannan a zamanin Sahabbai suka bayyana a jere. Sai kuma bayan zamanin Sahabbai aka samu Jahamiyya, Mu'utazila.

To haka 'yan bidi'a mabiya son rai suka cigaba da rabuwa daga tafarkin Sahabbai har zuwa lokacin da aka samu bayyanar "Asha'ira" mabiya Abul Hassan Al- Ash'ariy (324), bayansu kuma aka samu bayyanar "Maturidiyya", mabiya Abu Mansur Al- Maturidiy (333).

Mazhabar "Maturidiyya" ita ce Mazhabin da mafiya yawan 'yan Mazhabar Hanafiyya suke bi a Aqida, kasancewarsa Dan Mazhabar Hanafiyya a Fiqhu.

Wannar Mazhaba ta Maturidiyya ita ce: Mazhabar mafiya yawan wadanda suke gabashin Duniya; Pakistan, India, Rasha da sauransu.

Asha'ira da Maturidiyya duka sun saba wa tafarkin Salaf Ahlus Sunnan farko; Sahabbai da Tabi'ai da A'imma, irinsu Imamu Abu Hanifa, Malik, Shafi'iy da Imamu Ahmad bn Hanbal, amma su suka fi kusa da Ahlus Sunna a kan sauran 'Yan Bidi'a da son rai. Shaikhul Islami ® ya ce:

الأشعرية فلا يرون السيف موافقة لأهل الحديث وهم في الجملة أقرب المتكلمين إلى مذهب أهل السنة والحديث.

مجموع الفتاوى (6/ 55)

"Ash'ariyya ba su da Aqidar yakar al'umma da shugabanni dacewa da Ahlul Hadees, a dunkule su ne mafi kusaci ga Ahlus Sunnati wal Hadees a kan sauran mabiya ilmul kalam".

Dalilai da suke nuna banbanci tsakanin Aqidun Asha'ira da Maturidiyya da Aqidar Ahlus Sunnan farko:

1- Sun saba musu a babin Daukar Aqida, suna daukar Aqida ne daga hankali, shi ya sa suke Tawilin Nassoshin Qur'ani da Hadisai su tankwasasu sai sun yi dadai da hankulansu. Suke cewa:

"Idan Nassi ya yi karo da hankali to wajibi ne a tankwasa Nassin ya bi hankali, in kuma ba zai tankwasu ba, to dole a ajiye Nassin a bi hankali, saboda hankalin shi ne asali akan Nassi, ajiye asalin kuwa suka ne ga Nassin".

Baci da munin wannar magana a fili yake ga dukkan wanda yake ganin girman Qur'ani da Sunna.

2- Sun saba wa Salaf a babin Imani da Allah, saboda:

(a) Suna cewa; farkon wajibi a kan bawa shi ne; Nazari cikin dalilan halitta don sanin Allah, alhali kowa ya san Allah ne da fidirarsa. Kuma farkon wajibi shi ne: "Shaidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne".

(b) A babin Tauhidin Rububiyya, suna ganin ana sanin Allah da tabbatar da samuwarsa ne da hankali (Nazari), ba da fitira da Shari'a ba.

(c) Ba su san Tauhidin Uluhiyya ba, (Tauhidul Ibada), shi ya sa suke fassara shi da Tauhidin Rububiyya, suke fassara kalmar Shahada da cewa: "Babu Mahallici sai Allah", a maimakon "Babu abin bauta da gaskiya sai Allah". Wannan ya sa suke afkawa cikin Shirka a bauta, wajen rokon waliyyai, da dawafi a kabarbura da yanka ma wanin Allah da makamantansu. Alhali wannan Tauhidi shi ne hakikanin Addinin Muslunci da Annabawa suka zo da shi.

(d) Suna kore ma Allah Siffofinsa da ya siffanta kansa da su a cikin Littafinsa, da wadanda Manzonsa (s.a.w) ya siffanta shi da su a cikin Sunnarsa ta hanyar tawilin Nassoshin da Siffofin.

(e) Asha'ira siffofi bakwai kawai suke tabbatarwa, Maturidiyya kuma takwas. Shi ya sa suke kore Daukakar Allah a saman halittarsa, suke cewa: -wai- Allah yana ko'ina, alhali a fili karara Allah ya ce: Ya daukaka a saman Al'Arshinsa.

3- A babin Imani da Littafan Allah kuwa, hakikanin ra'ayinsu shi ne; Al- Qur'ani halitta ne, saboda ra'ayinsu kusa yake da ra'ayin Mu'utazilawa, kawai a lafazi ne suka saba, amma sun dace da su a ma'ana.

4- A babin Imani da Manzanni suna ganin Annabi (s.a.w) ya san gaibi, wanda hakan zai iya kaiwa ga Shirka ma Allah a cikin siffarsa da ya kadaita da ita ta sanin gaibi shi kadai.

5- A babin Imani da Kaddara ra'ayinsu kusa yake da ra'ayin Jabariyya, masu cewa: Mutum ba shi da tasiri wajen aikata aiyukansa, don haka dukkan aiyukan da yake aikatawa na alheri da na sharri -wai- duka Allah ne yake aikatawa, har na zina da shan giya da kafirci, -wai- duka Allah ne yake aikatawa - subhanallah-, saboda shi mutum ba ya aikata komai da kansa, kawai yana nan ne kamar busassshen ganyen bishiya da iska take yawo da shi duk inda take so. Sun saba wa Jabariyya a suna amma sun dace da su a ma'ana. Wato a ra'ayinsu na "Kasab".

6- Sai kuma a babin Hakikanin Imani da Aiki, suna tafiya ne a kan ra'ayin Murji'a, saboda imani a wajen Asha'ira da Maturidiyya shi ne Gaskatawar zuci kawai. Ma'ana daga zarar mutum ya gaskata Allah a zuciya to kawai ya je ya sheke ayarsa yadda yake so. Don haka a wajensu, magana da aiki ba sa cikin hakikanin Imani.

7- Banbancin da ke tsakanin Asha'ira da Maturidiyya dan kadan ne, saboda duka asalinsu daya ne, wato "Kullabiyya".

Su kuma Sufaye, launinsu daban ne, duk da cewa; Asha'ira da Maturidiyya su ne dai Sufayen ta bangaren Suluki.

Banbanci mafi muhimmanci tsakanin Sufaye da Ahlus Sunna, suna daukan Addininsu ne ta hanyar:

(1) Hadisan karya.

(2) Ilhama.

(3) Zauqi da Wajdi.

(4) Kashafi.

Kowanne daga cikin wadannan yana da nau'o'i.

Tauhidinsu shi ne Hululi da Ittihadi da Guluwwi a kan Waliyyai da Shehunnai da tsarkakesu, da kuma rokonsu da neman taimakonsu koma bayan Allah.

Hakikanin matsayin Walittaka ya fi matsayin Annabta da Manzanci a wajensu.

A babin Imani da Kaddara su tsantsan 'Yan Jabariyya ne, haka a babin Hakikanin Imani tsantsar Murji'a ne, shi ya sa suke halasta sheke aya, da alfasha, da aikata dukkan ma~sha'a iya yadda suke so.

Gwanaye ne wajen bautan kabarburan waliyyai, da yin tawassuli na bidi'a, da zikirori na bidi'a da kuma kide-kide da raye – raye da rawa da rangwada duka da sunan Ibada. Da kuma sauran bidi'o'i da aiyuka na Shirka da yake bayyana wa mutane, da ma wadanda babu wanda ya sansu sai Allah.

A dunkule, duka wadannan munanan Aqidu ne da suka saba wa Qur'ani da Sunna, suke warware Aqidar Ahlus Sunnan farko, wato Sahabbai da Tabi'ai da Limaman Muslunci; Imamu Abu Hanifa, Malik, Shafi'iy da Ahmad.

SABODA HAKA, TA YAYA ZA A YI ACE: ASHA'IRA DA MATURIDIYYA DA SUFAYE SU NE AHLUS SUNNAI WAL JAMA'A, -WAI- KUMA MABIYA TAFARKIN SAHABBAI SU BA AHLUS SUNNA BA NE?! 

KAMAR HANKALI BA ZAI YARDA DA WANNAN BA, KUMA WAQI'I YANA KARYATASU!

Saboda haka hanyar jirgi daban da ta mota.

Wallahu A'alam.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments