Ticker

6/recent/ticker-posts

Hujjojin Fajirai

Fajirai suna da wasu hujjoji da suka rike da suke halasta ma kawunansu fasikanci da fajirci, da daure gindi wa karuwanci da sauran miyagun aiyukan ashsha.

A kullum idan an yi musu inkari sai ka ji suna cewa:

"Ai Imani a zuciya yake".

"Ai da zaran mutum ya furta kalmar Shahada shi kenan".

"Ai Ubangiji ya ce: Kar ka shiga tsakanina da bawa".

"Laifin bawa tsakaninsa da Ubangiji ne".

Wadannan su ne irin hujjojin da Fajirai suke kafawa don cigaba da fajircinsu.

Alhali inkarin munkari da hani da mummunan aiki yana daga cikin manyan Siffofin da suka banbance tsakanin Muminai da Munafukai. Allah ya ce:

{وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ} [التوبة: 71]

"Muminai maza da Muminai mata sashensu majibinta sashe ne, suna umurni da kyakkyawa, kuma suna hani ga mummuna".

Su kuma Munafukai bisa kishiyantar Muminai suke, suna hani ga kyakkyawa, suna umurni da mummuna. Allah ya ce:

{الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُمْ مِنْ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمُنْكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمَعْرُوفِ} [التوبة: 67]

"Munafukai maza da Munafukai mata sashensu daga sashe ne, suna umurni da mummuna, kuma suna hani ga kyakkyawa".

Saboda inkarin munkari da hani da mummunan Allah ya fifita al'ummar Annabi (saw) a kan sauran al'umomi, inda ya ce:

{كُنْتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ } [آل عمران: 110]

"Kun kasance mafificiyar al'umma wacce aka fitar da ita wa mutane, kuna umurni da kyakkyawa, kuna hani ga mummuna, kuna yin imani da Allah".

Umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna yana daga cikin manyan aiyukan da Allah ya yabi Muminai cikin Ahlul Kitabi, inda ya ce:

{لَيْسُوا سَوَاءً مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ أُمَّةٌ قَائِمَةٌ يَتْلُونَ آيَاتِ اللَّهِ آنَاءَ اللَّيْلِ وَهُمْ يَسْجُدُونَ (113) يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ} [آل عمران: 113، 114]

"Ba dadai suke ba, a cikin Ahlul Kitabi akwai al'umma tsayayyiya,... suna umurni da kyakkyawa, suna hani ga mummuna".

Kamar yadda hakan yana daga cikin abin da ya sa Allah ya zargi kafiransu, inda ya ce:

{لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَى لِسَانِ دَاوُودَ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ذَلِكَ بِمَا عَصَوْا وَكَانُوا يَعْتَدُونَ (78) كَانُوا لَا يَتَنَاهَوْنَ عَنْ مُنْكَرٍ فَعَلُوهُ} [المائدة: 78، 79]

"Sun kasance ba sa hana junansu a kan mummunan da suka aikata".

Saboda haka umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna yana daga cikin manyan aiyukan da Allah ya yabi Muminai cikin wannar al'umma, inda ya ce:

{التَّائِبُونَ الْعَابِدُونَ الْحَامِدُونَ السَّائِحُونَ الرَّاكِعُونَ السَّاجِدُونَ الْآمِرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَالنَّاهُونَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَالْحَافِظُونَ لِحُدُودِ اللَّهِ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ} [التوبة: 112]

"...masu umurni da kyakkyawa, kuma masu hani ga mummuna..".

Wannan ya sa umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna yana daga cikin manyan aiyukan Muminai idan Allah ya ba su mulki, kamar yadda Allah ya ce:

{الَّذِينَ إِنْ مَكَّنَّاهُمْ فِي الْأَرْضِ أَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ وَأَمَرُوا بِالْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا عَنِ الْمُنْكَرِ } [الحج: 41]

"Wadanda idan mun ba su iko a bayan kasa, za su tsayar da Sallah, za su bayar da Zakka, kuma za su yi umurni da kyakkyawa, su yi hani da mummuna".

A takaice, sifa ce ta Munafukai kin hani ga mummuna. Wannan ya sa Munafukai a wannan zamani, cikin Zindikai da 'Yan dadi Arna da sauran fajirai a kullum suke fada da masu inkarin munkari da hani da mummunan aiki. Abin nasu har ya kai ga fada da hukumar Hisba, hukumar da Gomnati ta kafa don wannan aiki.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments