Ticker

6/recent/ticker-posts

Abin Da Musulunci Ya Fi Bukata A Yau

A yau babu abin da al'ummar Musulmi take bukata face hadin kai. Sai dai kash! kan ba zai hadu ba, dole sai kowa ya jefar da Akidarsa, ya zo an hadu a kan Akidar Sunna. Don babu abin da zai hada kan Musulmi sai ingantacciyar Akida ta gaskiya, wacce ta zo cikin Alkur'ani da Hadisi, Akidar da Sahabbai da Tabi'ai da A'imma suka rayu a kanta.

In dai da gaske hadin kan ake so, to sai Sufaye sun bar Akidunsu, sun yi watsi da Shehunai da Waliyyansu.

Haka 'Yan Shi'a sai sun bar Akidarsu, sun jefar da Marji'o'i da Mahdinsu.

Su ma Khawarijawa dole sai sun bar Akidarsu, sun ajiye bindigogi da bama-bamansu.

Asha'ira da Aqlaniyyun, su ma wajibi ne su ajiye akidunsu, su yi watsi da dagutun "Majaz" da gurbatattun hankulansu.

Kowa sai ya watsar da tarkacensa, ya zo ya bi Alkur'ani da Hadisi kamar yadda Sahabbai da Tabi'ai suka fahimta.

Duk wanda yake zaton zai hada kan mabanbanta Akida, ya yi siyasa, ya kafa Gomnati ta Muslunci to mafarki yake yi.

Wannan fa ba ina magana ne da Zindikai cikin 'Yan Shi'a da Sufaye ba, a'a, ina magana ne da wadanda da gaske suna son Addinin.

Wajibi ne mu hada kai a kan Akidar Alkur'ani da Sunna, mu tinkari Zindikai da 'Yan Boko Akida, wadanda suka yi damarar rushe Addini, da sauran abokan gaba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments