Cite this article as: Umar M. M. (2025). Kalmomin Masu Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai a Garin Sakkwato. Zamfara International Journal of Humanities, 4(1), 91-99. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2025.v04i01.010.
KALMOMIN MASU SAYAR DA MAN FETUR DA
BAƘIN MAI A GARIN SAKKWATO
Dr. Muhammad Mustapha Umar
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Tsakure: Wannan takarda ta yi nazarin kalmomin rukunin masu
sayar da man fetur da baƙin mai a cikin garin Sakkwato. Manufar ita ce, zaƙulo
yadda wannan rukunin ‘yan kasuwa suke sarrafa harshen Hausa, ta hanyar fito da
ma’anonin kalmomin da suke amfani da su a zantukansu na yau da kullum. An
taƙaita wannan bincike a kan nazarin kalmomi ne kawai, ba tare da nazarin
sassan jumla ko jumlolin wannan rukunin ‘yan kasuwa ba. An gabatar da hasashe
guda biyu (2), waɗanda aka gwada su ta hanyar gudanar da lura ta kai-tsaye da
hira ko tattaunawa da masu harkar sayar da man fetur da baƙin mai a wuraren
kasuwancinsu. An tattaro wasu lafuzzan da suke amfani da su domin tabbatar da
samuwar wannan Hausar dalilin zamantakewa da sauran ma’amalolin a wuraren
kasuwancinsu. Binciken ya gano cewa ‘yan kasuwar suna amfani da wasu ma’anoni
na musamman waɗanda suka sha bamban da yadda sauran jama’a suka san su a Hausar
yau da kullum. Binciken kuma ya gano cewa ma’anonin da suke amfani da su sun
samu ne daga faɗaɗa ma’ana da ƙirƙira da kuma sarrafa kalmomin aro.
Fitilun Kalmomi: Kalmomi, Man Fetur, Baƙin Mai.
1.0 Gabatarwa
Fetur[1] mai ne da ake zuba wa
babur ko mota ko wani inji wanda ke ƙonewa
don ya ba inji ƙarfin wuta da zai sa ya motsa.[2] Ana haƙo man fetur daga ƙasa ko daga
teku a tace a matsayin makamashi don amfani a injuna. A hukumance duk wanda zai
yi sana’ar fetur zai nemi lasisi daga gwamnati sannan a ba shi damar ya gina gidan mai[3].
Zai tanadi tankokin ɗauko mai da ma’aikata, da sauran abubuwan buƙata da za su
taimaka tafiyar da wannan kasuwanci mai haɗarin gaske. Sannan mai gidan mai ya
fara saye da sayar da man fetur a ƙarƙashin kulawar hukumar DPR.[4] Daga cikin masu kasuwancin
man fetur akwai manyan dillalai, waɗanda ke sayar da man fetur kan farashin
gwamnati da kuma dillalai masu zaman kansu, waɗanda a wasu lokuta suke sayar da
man fetur fiye da farashin da gwamnati ta ƙayyade. Shi ya sa wasu jama’a ke yi
musu kallon ‘yan kasuwar bayan fage, wato masu sayar da man fetur da tsada da
rashin lita mai kyau.
Baƙin mai[5],
mai ne kore mai kauri da ake zuba wa injuna da zai sa sassansu su motsa kamar
yadda ya dace. Masu sayar da baƙin mai yawanci suna gudanar da sana’arsu ne a
gefen tituna, inda suke aikin zubar da baƙin mai na babur ko mota ko wani inji
idan ya gama aiki, su zuba sabo a biya su kuɗin baƙin mai. Suna sayar da
mataccen baƙin mai da suke tarawa ga jama’a mabuƙata. Wannan baƙin mai shi suke
kira kwandem (condemn), kuma ana shafa shi a jikin katako don kariya
daga ƙwari. Masu ƙaramin ƙarfi ma na amfani da shi wajen juye, musamman kwandem
wanda bai gama aiki sosai ba. A yau masu wannan sana’a suna sayar da wasu
abubuwa bayan baƙin man irin su: Ruwan birki da fulogai da omon wankin mota da wayar kuloci
da giris da man fetur da kalanzir da kayan janareta da kuma sauran sassan abubuwan hawa.
Domin yin wannan nazari an kasa
takardar gida biyar. Daga farko akwai gabatarwa, sai hanyoyin gudanar da
bincike da hasashen bincike. Daga nan sai bayani kan Hausar masu sayar da man
fetur da baƙin mai, tare da misalan kalmomi, kana kuma aka kawo dangantakar
ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana, don tabbatar da kasancewar sauyawar ma’ana
ta hanyar faɗaɗa ma’anar kalmomi. A ƙarshe akwai jawabin kammalawa da sakamakon
bincike.
2.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike
Wannan
takarda sashe ne da ya shafi kundin binciken gaba-ɗaya. Don haka, ne aka
tsakuro wasu hanyoyin gudanar da bincike, da za su sawwaƙa tattaro bayanan
bincike kamar yadda ya dace. An yi amfani da hanyoyin tattaro bayanai guda
biyu, wato hira ko
tattaunawa da kuma lura ta kai-tsaye, waɗanda suka tabbatar da samuwar wannan nau’i na Hausa
kamar yadda masu sayar da man fetur da baƙin mai suke amfani da ita a wuraren da binciken ya shafa. An kasa
waɗanda aka yi hira da su zuwa gida huɗu:
a)
Tattaunawa da masu sayar da man fetur da gas da baƙin mai
a gidajen mai
b) Tattaunawa da masu
sayar da man fetur a gefen tituna, waɗanda ake kira ‘yan cuwa-cuwar man fetur (black market)
c)
Tattaunawa da masu sayar da baƙin mai a gefen tituna
d)
Tattaunawa direbobi masu ɗauko mai da yaransu
A wannan takarda, mai bincike ya zaɓi yin amfani da ra’in Harris (1952) mai suna Discourse
Analysis Theory wanda yake nazarin yadda al’umma suke sarrafa harshe, ta fuskar ma’ana don zaƙulo
dangantakar da ke tsakanin ma’anar da tarihin samuwar kalmomin harshe. Ra’in ya dace
kuma yana da dangantaka da wannan bincike domin ya shafi yadda wasu rukunan
jama’a suke amfani da harshe bamban da sananniyar ma’ana ta fuskar kalmomi a
zamantakewarsu da sauran ma’amalolinsu na yau da kullum. Ga wasu misalai na
wasu ayyuka da aka gabatar ta amfani da ra’in: Isah (2018) da Zailani (2019) da
Sharu (2023) da kuma Mode (2024).
3.0 Hasashen
Bincike
An yi kintacen abubuwa huɗu (4) da ake sa ran za su faru,
waɗanda ake fatar idan aka gwada su, su dace ko su saɓa wa abubuwan da bincike
ya gano a ƙarshe. Ga hasashen:
1. Masu sayar da man fetur
da baƙin mai a garin Sakkwato suna da wata keɓaɓɓiyar Hausa da suke
amfani da ita wajen aiwatar da kasuwancinsu.
2. Hausar waɗannan rukunin ‘yan
kasuwa ta ƙumshi kalmomi masu ɗauke
da sababbin
ma’anoni saɓanin waɗanda aka san su da su.
4.0
Kalmomin Masu
Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai[6]
‘Yan kasuwa sukan yi amfani da harshen Hausa wajen
bayyana wasu abubuwa, waɗanda suka jiɓinci rayuwarsu ta yau da kullum, tare da
samar musu da sababbin ma’anoni, domin sadarwa cikin sauƙi. Kodayaushe
idan wani abu baƙo da babu shi ya shigo a ƙasar Hausa, akan yi ƙoƙarin samar
masa suna ta hanyoyin da suka dace. Misali, yin amfani da wasu fitattun hanyoyi
kamar faɗaɗa ma’ana da ƙirƙira da aro da ɗafi da kuma tsira. Tun da haka ne,
muna iya cewa wasu daga cikin waɗannan hanyoyin sun taimaki Hausar kasuwanci,
musamman sakamakon bayyanar abubuwan zamani. Wani abin sha’awa shi ne, yadda
kowane rukuni na ‘yan kasuwa ke ƙoƙarin ƙirƙira sabbin ma’anoni, don tafiyar da
al’amurransu.
Hausar masu sayar da man fetur tana samuwa ne tun daga
tafiya ɗauko mai, inda direba da yaransa ke amfani da wata Hausa don bayyana
wani hali ko yanayi da suke ciki a lokacin gudanar da sana’arsu. Su ma
ma’aikatan gidan mai suna amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi tsakaninsu domin
sadarwa. Sannan akwai ‘yan cuwa-cuwar[7] man fetur masu sayar da mai a kan tituna. A taƙaice,
akwai alaƙa tsakanin direbobi da yaransu masu ɗauko mai a kurmi da ‘yan kasuwa
masu sayar da mai. Za a fahimci wannan dangantakar a ƙarƙashin misalan Hausar
masu sayar da man fetur da baƙin mai. Fagge (2004: 126-127) ya kawo bayani kan
Hausar ‘yan cuwa-cuwar man fetur kamar haka: Sana’ar sayar da man fetur ta samu
ne daga baya inda matasa kan sayi mai daga hannun manyan dillalai, su kuma su
kasa su sayar a gefen tituna. Sai dai galibi masu gudanar da wannan sana’a
matasa ne kuma yawancinsu ‘yan daba ko ‘yan shaye-shaye.
Kusan da wuya ka ga mai sayar da mai ko mai irin wannan
sana’a[8] ba ya shaye-shaye, musamman wiwi. Su ma suna da wasu kalmomi nasu na daban waɗanda suke
amfani da su a tsakaninsu domin sadarwa. Haka kuma, akwai ‘yan kasuwa masu sayar da baƙin mai a kan titi, waɗanda
suka riƙe ta a matsayin
hanyar sana’arsu da suke yi don gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Masu
wannan sana’ar suna amfani da wata keɓaɓɓiyar Hausa wajen gudanar da sana’arsu,
musamman domin ambaton abubuwan da suke sayarwa da kayayyakin da suke amfani da
su wajen gudanar da sana’arsu.
4.1 Kalmomin da suka Shafi Faɗaɗa Ma’ana
Kalmomin da za a gani a wannan sashe. Kalmomi ne na Hausa
kuma suna da ma’ana ta asali, amma aka ba su wata ma’ana ta musamman saɓanin
wadda aka san su da ita. Waɗannan ma’anoni sabbi, da su ne masu sayar da man
fetur da baƙin mai ke amfani wajen aiwatar da kasuwancinsu.
(A)
Faɗaɗa
Ma’anar Kalmomin Asali
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Méesàa[9] |
Suna
|
Ƙatuwar macijiya mai haɗiye mutum ko
dabba. Ana amfani da fatar ta wajen yin
takarmi da jakunkuna
|
A jikin injin na sayar da mai akwai
wata roba doguwa mai kauri, wadda ta cikinta fetur ke fita, wadda a ƙarshenta
tana da kai ko baki mai mariƙi na musamman, da ake matsawa a zuba mai ko a
tsayar da shi |
|
2 |
Sóoɓòo [10] |
Suna |
Fure ne da ake samu daga sure ko
yakuwa |
Man
fetur mai launin ja-ja-ja |
|
3 |
Jùuyée |
Suna |
Saye
abin da budurwa ke talla, ko wani irin kitso |
Zubar
da baƙin mai na abin hawa ko inji idan ya gama aiki don a zuba sabo |
|
4 |
Hàlàmníyáa |
Suna |
Cin abinci da sauri don haɗama
|
Cuwa-cuwar man fetur inda kowane ɗan
bulakmaket ke sauri ko ƙoƙarin ya ba da roja[11] don ya sayi fetur fiye da sauran jama’a |
|
5 |
Sàndáa |
Suna |
Itace
da aka karya ko aka sara daga jikin bishiya don yin amfani da shi kamar a
makami na dukan wani abu ko don dogarawa |
Dogon
ƙarfe mai zanen mita a jikinsa wanda ake awon man fetur da ke cikin tankin ƙasa |
|
6 |
Náiràa bìyár |
Suna |
Takardar
kuɗin Nijeriya mai ɗauke da hoton marigayi Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa |
Naira
ɗari biyar |
|
7 |
Náiràa góomà |
Suna |
Takardar
kuɗin Nijeriya mai ɗauke da hoton marigayi Alvan Ikoku |
Naira
dubu ɗaya |
|
8 |
Ɗígòo[12] |
Suna |
(i) Ɗison abu ruwa-ruwa
(ii) ruwan baƙaƙe da ake yi wa wasu haruffan Ajami ko na Larabci ko kuma
Ingilishi (iii) aya ta nuna alamar tsayawa a cikin jumla ko wajen karatu |
Lambobi ɗari da ke jujjuyawa, su
bayar da lita guda
|
|
9 |
Bàasáajàa[13] (basaje)
|
Suna |
Fakewa
da wani hali don samun riba |
Karkatar
da man fetur zuwa wani wuri ko wata ƙasa maimakon zubawa a gidan mai a sayar
wa jama’a, musamman don samun riba sosai |
Waɗannan
misalai sun fayyace yadda ‘yan kasuwa suke ba
kalmomin asali sababbin ma’anoni saɓanin waɗanda aka san su da su. Kuma wani
lokaci ba tare da an canja fasalin kalmomin ba, wato kalmomin suna nan zamansu
kamar yadda suke. Kamar yadda aka gani ‘yan kasuwa suna amfani da wannan hanya ta faɗaɗa
ma’anar kalmomi, bayan sun lura da yanayin baƙin abubuwan da suka shigo waɗanda
ba su san su ba, kafin su yi amfani da kalmomi asali da za su dace.
4.2 Kalmomin da suka Shafi Ƙirƙira
A wannan sashe an kawo sabbin ma’anoni da ‘yan kasuwa
suka ƙirƙiro, don sadarwa a tsakaninsu. Waɗannan sabbin ma’anoni sun keɓanta
gare su ne kawai. Akasari duk inda aka zagaya ba za a ji ana aiwatar da su ba,
sai a Hausar rukunin masu sayar da man fetur da baƙin mai.
1.
Ƙirƙira
Daga Kalmomin Asali
|
Lamba |
Kalma |
Ajin
Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jùuyèn náa-ìsáa |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Juye baƙin mai tun bai gama aiki ba |
|
2 |
‘Yán-sâ-káì[14] |
Harɗaɗɗen Suna |
Masu hidimar al’umma kyauta (‘Yan
ganin dama)
|
‘Yan alfarma waɗanda ba su bin layi ko ‘yan cuwa-cuwar
man fetur masu ba da cin hanci a sayar musu mai, ba tare da sun tsaya layi ba
ko kuma masu cin layi, sai dai su tsaya gefe idan an fara shigar da abubuwan
hawa sai su kutsa in sun sami kafa. |
|
3 |
Mân
hánnúu[15] |
Harɗaɗɗen Suna |
Man
gyaɗa |
Man
cuwa-cuwa ko na sata |
|
4 |
Másháaƙár ískàa[16] |
Harɗaɗɗen Suna |
Wuri
ne ko kafa da aka keɓe don wani abu ya riƙa zuƙar iska |
Fayib
da ake haɗawa da tankin mai na cikin ƙasa don tanki ya riƙa numfasawa
musamman idan akwai mai a cikinsa, don gudun kada tanki ya fashe |
2.
Ƙirƙira ta Gamin-gambizar
Kalmomin Asali da na Aro
|
Lamba |
Kalma |
Ajin
Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jákkwátàa (jar kwata) |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Robar maganin ƙwari mai launin ja |
|
2 |
Jùuyèn gáayèe[17] |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Baƙin
mai da wani ya juye wanda bai gama aiki ba |
|
3 |
Gárwár
gáayèe |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Babbar
robar yagot mai mariƙi ko hannu |
3.
Ƙirƙira
Kalma Wadda Sam Babu Ita a Hausa
|
Lamba |
Kalma |
Ajin
Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Róojà |
Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Cin
hanci da ‘yan cuwa-cuwar fetur ke ba ‘yan gidan mai kafin a sayar musu da man
fetur |
Idan aka lura da dukan waɗannan misalan, za a ga sun samu
ne ta hanyar ƙirƙirar daga kalmomin asali, da ƙirƙira ta fasahar gamin gambizar
kalmar asali da ta aro,[18] da kuma ƙirƙira kalma wadda sam babu ita a wani harshe.
Ƙirƙira irin waɗannan kalmomi na bunƙasa rumbun kalmomin harshe. Duba da yadda
ake daɗa samun masu sayar da man fetur da baƙin mai na ƙirƙira sababbin
ma’anoni, musamman waɗanda suka shafi yanayin aiwatar da kasuwancinsu ko
rayuwarsu ta yau da kullum. A wasu lokuta, ‘yan kasuwar sukan cusa
sabbin ma’anonin da suka samar a cikin harshe. Bayan wani ƙanƙanin lokaci, sai
a tarar sun saje da sauran ma’anonin Hausa na asali.[19]
4.3 Kalmomin da suka
Shafi Aro
A
wannan sashe, an ga yadda masu sayar da man fetur da baƙin mai suka ɗauko kalmomi daga harshen
Ingilishi da na Yarbanci. Su mayar da su na Hausa bayan an yi musu
kwaskwarima, don su dace da tsarin Hausa. A taƙaice, sukan Hausantar da
baƙin kalmomin da suka aro ne don samun kafar sadarwa a tsakaninsu.
|
Lamba |
Kalma |
Asalin Kalma |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jóokò (Jooko)[20] |
Kalmar
aro ce daga Yarbanci |
Tsaiko
cikin layin lodin mai ko lalacewar mota kan hanyar dawowa |
|
2 |
Dìríilìn (Drilling) |
Kalmar
aro ce daga Ingilishi |
Sauran
man fetur da ke ragewa bayan an sauke mai a gidan mai. Ana yi masa kirari da ‘dirilin na yaron mota’ |
|
3 |
Míshìn gálàn (Measurement galoon) |
Kalmar
aro ce daga Ingilishi |
Auna mitar bayar da mai ko ta inji na mai |
|
4 |
One-five
(1,500) |
Kalmar
aro ce daga Ingilishi |
Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar |
|
5 |
Áftáasêl (Aftersale)[21] |
Kalmar
aro ce daga Ingilishi |
Sai an sai da mai sannan a biya mai man fetur |
|
6 |
Màanúwâl kóó kwàmfúutàa
(Manual/computer)[22] |
Kalmar
aro ce daga Ingilishi |
Mitar auna abin da aka sayar a injimin sayar da mai,
kuma tana iya lissafin lita miliyan, wato daƙiƙa bakwai na lamba. |
|
7 |
Hâf (half) gáayèe[23] |
Kalmar
aro ce daga Ingilishi |
Robar
yagot mai biye wa garwar gaye |
|
8 |
Ólóojì (awon mai) |
Kalmar
aro ce daga Yarbanci |
Awon
man tanka kafin a zuba a cikin ramin ajiya na ƙasa[24] |
Daga waɗannan misalai an ga yadda ‘yan wannan rukunin suke Hausantar da kalmomin
aro, ta hanyar yi wa kalmomin kwaskwarimar
da za ta sa su dace da tsarin furucin Hausa. Daga nan sai su ba su sababbin ma’anoni da suka bambanta da na
asalinsu. Abin ban sha’awa shi ne, yadda baƙin kalmomin suka saje da na asali
wani lokaci akan kasa bambanta su. Kenan, wannan hanyar sarrafa kalmomin aro
fitatta ce kuma madoga ga harshe, musamman inda aka kasa nemo madadin sabuwar
kalma daga cikin na asali da ake da su a harshe. A ƙarshe, aro hanya ce mafi sauƙi da
harsuna suke faɗaɗa rumbun kalmominsu, bayan an samu hulɗa da cuɗanya
tsakanin harsuna daban-daban. Kamar dai
yadda masu sayar da man fetur da baƙin suke amfani da su a zantukansu na yau da
kullum.
5.0 Kammalawa
Daga abin da ya gabata a fili yake cewa, wannan rukuni na
‘yan kasuwa na amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi da suka shafi yanayin kasuwanci,
musamman don tafiyar da hankulan masu sayen kaya, inda suka al’adanci yin
amfani da kalmomi sanannu wajen samar da sababbin ma’anoni, amma ba lalle ne
ma’anar ta zo daidai da ma’anar asali ba. Da ƙirƙiro sababbin ma’anoni daga
kalmomin asali ko daga na aro ko ta gamin gambiza inda za a haɗa kalmar asali
da ta aro a tashi sabuwar kalma, ko kuma ƙirƙiro ma’anonin da sam babu su a
harshe. Haka kuma, sarrafa harshe cikin aiwatar da kasuwanci a tsakanin ‘yan
kasuwa ta taimaka wajen haifar da ƙirƙire-ƙirƙiren sababbin kalmomi da jumloli,
waɗanda ke daɗa bayyana hali da yanayin ciniki a muhallan kasuwanci.
6.0 Sakamakon
Bincike
A
taƙaice, wannan takarda ta gano abubuwa kamar haka:
1. Wannan takarda ta gano cewa,
Hausar masu sayar da man fetur da baƙin mai (sabuwar Hausar rukunin jama’a) a cikin garin
Sakkwato suna da wata hanyar sadarwa a
tsakaninsu, wadda ta bambanta da Hausar gama-gari ta fuskar kalmomi, domin ba kowa ke iya fahimtar
ma’anarta ba.
2. Binciken ya gano cewa ‘yan wannan
rukuni suna amfani da dabarar faɗaɗa
ma’anar kalmomin Hausa na asali da sarrafa kalmomin aro da kuma ƙirƙira sababbin kalmomi a cikin zantukansu na yau da kullum.
3. Bugu da ƙari, takardar ta gano ‘yan kasuwar suna amfani
da dabarar ɓoye
wasu ma’anoni, domin saye da ɓatad da bami wanda ba ɗan rukuninsu ba.
A taƙaice, sukan sirranta maganganunsu ne domin ƙoƙarin samun riba mai yawa da
sakaya lissafin kuɗi a cinikayyarsu.
MANAZARTA
1.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. (2006). Ƙamusun
Hausa. Kano: Ahmadu Bello University
Press Limited.
2.
Fagge, U.U. (2004). Ire-iren
Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers limited.
3.
Harris, Z.S. (1952). ‘Discourse Analysis’ In Language, V. 28, 1-30.
4.
Isah,
F.H. (2018). A Sociolinguistic Analysis of The Jargons Used by Town Service
Tricyclists (A-daidaita-sahu) in The Kano Metropolis. Unpublished M.A
Dissertation. Department of Liguistics. Bayero University, Kano.
5.
Mode, A. (2024). Nazarin Hausar ‘yan
Koli a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
6.
Sharu,
Y. (2023). Hausar ‘yan Agwagwa-da-buje a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu.
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
7.
Umar,
M.M. (2019). Nazarin Hausar Wasu Rukunan ‘Yankasuwa a Garin Sakkwato. Kundin
Digiri Na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usamanu Xanfodiyo, Sakkwato.
8.
Yusuf M.A. (2002). The Development of Hausa Neologism: The Role of Urban Spaces. In Bichi, A.Y et al (eds). Studies in Hausa Language, Literature
And Culture. The Fifth Hausa International Conference. Kano:
Benchmark Publishers Limited. Page 105-113.
9.
Zailani,
A.A. (2019). A Study of Communication Strategies in Hausa Request Act. Unpublished Ph.D
Thesis. Department of Linguistics and Foreign Languages. Bayero University, Kano.
RATAYE
MUTANEN DA AKA ZANTA DA SU
|
S/N |
Suna |
Shekaru |
Muhallin da aka Tattauna |
Kwanan Wata |
|
1 |
Malami man Ada |
51 |
Gidan man ada
titin Kalambaina, Wamakko, Sakkwato. |
01/10/2024 |
|
2 |
Alh. Basiru Babawo |
40 |
Mai sayar da
baƙin mai a bakin gidan man Man Ada titin Kalambaina, Wamakko, Sakkwato |
05/10/2024 |
|
3 |
Nasiru Malami |
38 |
Mai sayar da man
fetur a hannun-riga da gidan man NNPC mega station kusa da makarantar FGC,
Sakkwato |
06/10/2024 |
|
4 |
Mustapha Dogon-daji |
29 |
Mai sayar da
baƙin mai a gidan dare bakin rawun na gidan ashana western bye-pass,
Sakkwato ta Kudu, Sakkwato |
21/10/2024 |
|
5 |
Ashiru Dabagin Arɗo |
20 |
Mai sayar da baƙin mai da fetur Dange-shuni |
18/11/2024 |
|
6 |
Mal. Ahmad Zaruku |
60 |
Gidan man
Bashariyya Global Resourses, Sakkwato ta Arewa |
25/12/2024 |
|
7 |
Bashar Yusuf (police) |
41 |
Gidan man A.A
Rano Nig. Ltd. Rawun na gidan Man Ada, Sakkwato |
15/01/2025 |
|
8 |
Dogo Mai Gas |
47 |
Gidan man Altine
Muhammad Ƙaura titin Kalambaina, Sakkwato |
16/01/2025 |
|
9 |
Umar Faruk (yellow) |
35 |
Mai sayar da baƙin mai da fetur Wamakko, Sakkwato |
07/02/2025
|
|
10 |
Bashar Ibrahim Maigayya |
30 |
Shiyar Arkilla Federal Low Cost kusa da ofishin
NDLEA |
09/02/2025 |
[1] Masu sayar da man fetur iri biyu ne: akwai ‘yan kasuwa masu sayar da mai
a gidajen mai, akwai kuma masu sayar da mai a gefen tituna a cikin jarka ko
garwa. Fagge (2004:126-127) ya kira su
‘yan cuwa-cuwar man fetur. A wasu wurare ana kiran su da ‘yan bumburutu ko kuma ‘yan bulakmaket. A hukumance, suna sayar da mai
ba bisa ƙa’ida ba. A wasu lokutan baya, har
kamen masu sayar da mai a kan hanya ake yi.
[2] Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, “Ƙamusun Hausa” Ahmadu Bello University Press Limited, Kano, 2006, shafi na 140.
[3] Gidan mai wuri ne na hadahadar mutane masu zuwa don saya wa abubuwa hawa
mai da injunan haska wutar lantarki.
[4] Hukuma ce wadda ke da
alhakin sa ido kan fice
da shigen ma’adinan da ake haƙowa a cikin Nijeriya. Ayyukan da aka ɗora mata sun haɗa da: Sa ido ga yadda
ake gudanar da ha}ar mai da samar da rijiyoyin mai da fitar da ɗanyen mai a ƙasashen waje da wuraren
tace ɗanyen
mai da depot na ajiyar mai da gidajen mai da sauran wuraren da ake ajiye mai ko
sayar da shi, da bututun da ke ɗauko ɗanyen
mai da
gas da sauran ma’adinnan mai. Haka kuma, hukumar na tabbatar da cewa, duk
kamfunnan mai sun mallaki lasisi da gudanar da ayyukansu cikin tsabta da ɗaukar matakan kiyaye
hatsarin gobara da bin doka da oda, musamman abin da ya shafi farashi da cikar
lita da kuma biyan haya ko haraji ga gwamnati kamar yadda ya dace.
[5] Ana ganin sunan baƙin mai ya samo asali ne daga launin da man na juye ke
sauyawa idan ya gama aiki.
[6]
Don ƙarin bayani sai a duba aikin, Umar, Muhammad Mustapha, “Nazarin Hausar
wasu Rukunan ‘Yan Kasuwa a Garin Sakkwato” Kundin Digiri na Uku. Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, 2019, shafi na 38-59.
[7]
Fifiƙewa da ba da himma wajen ƙoƙarin samun wani abu ta hanyar cuta.
[8] Masu sayar da mai a
gefen hanya cikin jarkuna su ne, irin waɗannan matasa.
[9] Wasu suna kiran ta tiyo
ko roba ko hwanho ko kuma nozzle, musamman
ganin irin yadda take aikin zuƙo mai.
[10] Man fetur wanda ake haƙowa a Nijeriya shi
launinsa ke da kama da ja-ja-ja kamar yadda Dogo na gidan man Alh. Altine Muhammad Kaura ya shaida mini.
[11] An bayar da ma’anar roja a sashen 4.2.
[12] Amma a injunan man fetur na shekarun baya masu kama da tuƙa-tuƙa ɗigo goma shi ne lita guda, kafin
bayyanar injunan zamani masu amfani da digital.
[13]Gidajen
mai masu karkatar da man
fetur sukan yi amfani da tankokinsu na ɗaukar
mai waɗanda ba a rubuta musu sunan kamfani
a jikinsu ba, don kar hukuma ta gane su, musamman a lokutan da ake fuskantar ƙarancin man fetur.
[14]
Ƙungiyoyin sa-kai ko kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.
[15]
Sayen man fetur ko gas ta bayan fage daga hannun direba ko yaransa ko wasu
ma’aikatan kamfani ko kuma mutane masu harka da kayan sata (ɗanyun kaya a
Hausar wasu ‘yan kasuwa) ko kayan rashin gaskiya.
[16]
Tankin mai na ajiyar mai a cikin ƙasa yana da marfi, wanda a jikinsa ake haɗa
fayib mai zuƙar mai daga tanki zuwa ga injin na sai da mai, da fayib na
mashaƙar iska wanda ake kafewa a tsaye tare da sunkuyar da kansa don rana ruwa
shi cikinsa, da kuma kusurwar da ake buɗewa a duk lokacin da za a zuba mai ko
awon sa.
[17]
Juyen matashi ɗan gayu.
[18] Wannan rukuni na ‘yan kasuwa ya yi amfani da wannan
hanya ta ƙirƙira wajen bai wa mazubi ko abin awon man fetur suna, kamar yadda
misalan suka nuna. Wani lokaci ma, ana amfani da hanyar fassara kalmar aro (loan
translation). A nan akan yi amfani da kalmomi ne a
fassara ainihin suna, aiki ko ma’ana ta baƙon abu a harshen aro. Ga misali, ana
amfani da dafa-duka (jalaf) domin wakiltar motar nan Peugeot 504 (station
wagon).
[19] Don ƙarin bayani a dubi,
Yusuf (2002) ya bayyana yadda ƙirƙirarrun kalmomi kan rikiɗe su koma karɓaɓɓun kalmomi bayan an
baddala su cikin harshe, kuma sannu a hankali za su yaɗu a riƙa amfani da su kamar
sauran kalmomin harshe.
[20] Ana cewa wane ya yi joko da yawa, wato ya jima bai dawo ba, ko kuma a
ce, direba ya hwaɗa joko.
[21] Ana amfani da wannan
salo ne don a tabbatar da man da aka kawo ya cika kuma mita da difin na gidan
mai na
aiki daidai.
[22] Floor measurement shi ne ainihin sunan mitar a harshen Ingilishi. Ita kuma kalmar kwamfuta wasu na fassara ta da na’ura mai ƙwaƙwalwa.
[23] Akwai masu kiran ta
‘Yákkùnúu.
[24] Ana wannan awon ne idan
ana shakkun tankin mota ko wanda ya kawo mai, ko kuma don tabbatarwa kawai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.