Ticker

6/recent/ticker-posts

Zunguro Sama Da Kara: Asalin Haruffan Da Hausawa Suke Amfani Da Su Kafin Zuwan Rubutun Abajada





Zunguro sama da kara.

Ashe dai al'ummar Hausawa suna da asalin baƙaƙen da suke amfani da su tun kafin zuwan rubutun A,B,C,D da aka samo daga harshen Latin da Girkawa da Yahudawa da kuma Larabawa?

Waɗannan alamomi sun samo asali ne daga masu bayar da magungunan gargajiya ta hanyar taskace duk wani sassaƙe da saiwoyi da ganyaye da kauci da kuma ɓawo.

Wani masani daga Jami'ar Ƙasar Jamhuriyar Nijar, ya gabatar da waɗannan alamomi a gaban manyan malaman harshen Hausa na duniya yau a jami'ar Bayero Kano. Ya kuma kafa hujja da cewa, irin waɗannan alamomi su ne na farko a wajen samar da rubutu a duniya. Haka kuma Masanin ya bayyana cewa "Ba iya kwanciya aka fi Kare ba, zanen rufa kawai aka fi shi". Inda ya kawo sunayen manyan litattafan tarihi da na addinin Musulunci da su ke nuna cewa lallai Hausawa ne suka fara samar da wani abin rubutawa da irin waɗannan alamomi.

Zunguro sama da kara.

Haka kuma, ya ƙara da cewa, nan duniya babu mai iya ja da waɗannan alamomi da Hausawa suka ƙirƙira tun zamani mai tsawo. Ya kuma kafa hujja da cewa, hatta waɗancan kabilu na Girka da Latinawa da Yahudawa da Larabawa, suna kwafin juna ne, wajen samar ba baƙaƙe da wasulan da ake amfani da su yau da kullum. Amma waɗannan alamomi, Hausawa ne suka ƙirƙire su, ba tare da sun kwaikwayi kowa ba.

Manyan malaman harshen Hausa da na Tarihi sun yi tsokaci mai gamsarwa a kan waɗannan alamomi. Kuma nan gaba, za a yi gangamin taron masana ilimin kimiyyar harshe da masana tarihi da al'adu, waɗanda da su ne, harshe ya ke iya yaɗuwa har ya bunƙasa, domin samar da matsaya a kan waɗannan alamomi, domin a amince da su, su maye gurbin waɗannan baƙaƙen da mu ke rubutu da su yau da kullum.

Manufar taron ita ce, a sauka daga kan duk wata bautarwa da Turawa su ke yi wa Hausawa ta fuskar amfani da baƙaƙen A,B,C,D, a maye gurbinsu da waɗannan alamomin da za su zama su ne na asalin Hausawa.

Idan hakan ta tabbata, akwai yiwuwar sai an sake koyar da mu ilimin waɗannan alamomi, da nufin yin amfani da su a rubutun yau da kullum.

Allah ya taimaki Harshen Hausa,

Allah ya taimaki Hausawa,

Allah ya taimaki ƙasar Hausa. Amin.

Zunguro sama da kara.

Adamu Yunusa Ibrahim,
Cibiyar Nazarin Hausa,
Jam'iar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato, Nijeriya.
talk2abusultan@gmail.com
danzabuwagrk@gmail.com

Zunguro sama da kara.

Post a Comment

0 Comments