Ticker

6/recent/ticker-posts

Magudin Zabe a Tarihin Siyasar Jam’iyyu a Arewacin Nijeriya: Nazari Daga Rubutaccen Zuben Hausa

Citation: Yusuf, J. & Bunza, U.A. (2025). Maguɗin Zaɓe a Tarihin Siyasar Jam’iyyu a Arewacin Nijeriya: Nazari Daga Rubutaccen Zuben Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(1), 1-13. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.001.

MAGUƊIN ZAƁE A TARIHIN SIYASAR JAM’IYYU A AREWACIN NIJERIYA: NAZARI DAGA RUBUTACCEN ZUBEN HAUSA

Na

Jibril Yusuf
Department of Nigerian Languages and Linguistics
Kaduna State University, Kaduna.
Phone no: +2347030399995
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng

Da

Umar Aliyu Bunza
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Email: aliyu.bunza@udusok.edu.ng
Phone No: +2347063532532  

Tsakure

Sunan wannan takarda shi ne “Maguɗin Zaɓe a Tarihin Siyasar Jam’iyyu a Arewacin Nijeriya: Nazari daga Rubutaccen Zuben Hausa”. A cikin wannan takarda an duba yadda maguɗin zaɓe ya ginu a cikin tarihin siyasa Arewacin Nijeriya. Manufar wannan bincike shi ne yin nazarin maguɗin zaɓe a cikin tarihin siyasar jam’iyyu daga ayyukan rubutaccen zube. Takardar ta mayar da hankali ne ga siyasar Arewacin Nijeriya, domin ganin yadda maguɗin zaɓe ya ginu a cikinta. Hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan da wannan nazarin ya yi amfani da su sun haɗa da: Karance-karance na ayyukan da aka samu a kan siyasa musamman waɗanda suka shafi maguɗin zaɓe, inda aka samu bayanan da suka taimaka wajen gina wannan maƙalar. An duba jaridu da jawaban siyasa da wasiƙu da kuma ƙagaggun labarai waɗanda suke ɗauke da ruhin siyasar jamiyyu a cikinsu domin samun batutuwan da aka kafa hujja da su. An yi amfani da ra’in Tarihanci wanda aka ɗora binciken a kansa. A ƙarshe takardar ta gano cewa maguɗin zaɓe abu ne da ya ginu a cikin siyasar jam’iyyu tun daga farkonta, kuma har yanzu ana amfani da shi domin fafutukar neman ɗarewa bisa madafun iko a cikin siyasar Arewacin Nijeriya.

Fitilun Kalmomi: Maguɗi, Zaɓe, Tarihi, Siyasa, Maguɗin Zaɓe

1.0    Gabatarwa

Maguɗin zaɓe yana cikin haramtattun hanyoyin neman mulki a dimokuraɗiyyar Nijeriya. Yana ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suke haifar da rashin cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya ga al’umma. Hanya ce da ‘yan siyasa suke bi domin su kai ga ɗarewa a kan madafun iko ta kowane hali. A tsarin dimokuraɗiyya zaɓe shi ne hanya ɗaya da ake bi wajen tabbatar da waɗanda za su shugabanci al’umma ko kuma sauke waɗanda suke kan mulki tun daga matakin mazaɓa har zuwa mataƙin ƙasa baki ɗaya (Bello da Bappi, 2015: 3). Muhimmancin wannan al’amari na zaɓe ya sanya ‘yan siyasa tsayawa kai da fata wajen ganin sun yi duk yadda za su yi domin aiwatar da shi da kuma neman samun nasara a kan abokin hamayya ta kowane hali. Duk da cewa, zaɓe a kowane mataki yana ɗauke da wasu dokoki da ƙaidojin gudanar da shi wanda hukuma takan sanya domin tabbatar da adalci ga yan takara, amma a wasu lokuta akan samu waɗanda sukan bi wasu hanyoyi da suka saɓa wa dokokin hukuma domin tabbatar da sun kai ga nasara ko ta halin ƙaƙa. Amfani da waɗannan haramtattun hanyoyin tare da saɓa ƙaidojin gudanar da zaɓe, musamman a lokacin da ake gab da fara jefa ƙuria ko kuma aka fara jefa ƙuriar shi ne yake haifar da maguɗin zaɓe.

2.0 Waiwaye

Dangane da batun maguɗin zaɓe a cikin siyasar jam’iyyu, masana da manazarta sun tofa albarkacin bakinsu. Daga cikinsu akwai Bello da Bappi (2015) da suka dubi yadda al’amuran maguɗin zaɓe suka wakana daga 1999 zuwa 2015. Sun kawo wasu abubuwa da ake ganin sun taimaka wajen aiwatar da maguɗi a wannan lokacin kamar amfani da ‘yan bangar siyasa wajen tayar da yamutsi domin yin maguɗi. Aikin Bunza (2018) ya taɓo maguɗin zaɓe a cikin waƙoƙin Kyaftin Umaru Ɗa Suru. Ya kafa hujja da wasu baitukan waƙoƙinsa tare da sharhinsu waɗanda suka nuna samuwar maguɗin zaɓe a siyasar jam’iyyu. Takardar Micheal da Ogunrotimi da Roland (2023) ta kawo bayanai kan ginuwar maguɗin zaɓe a cikin tarihi. Takardar ta kawo bayanai kan zaɓuɓɓukan da aka gudanar a shekarar 1959 da 1964 da 1965 da kuma 1983. Duka waɗannan ayyukan sun ƙunshi muhimman bayanai a kan maguɗin zaɓe, sai dai ba su kafa hujjoji daga rubutaccen zuben Hausa ba. Manufar wannan takarda shi ne nazarin tarihin maguɗin zaɓe a cikin rubutaccen zuben Hausa. Takardar ta kawo misalai da bayanai game da masu gudanar da maguɗin zaɓe da kuma wasu dabarun da ake amfani da su domin gudanar da maguɗin zaɓe a cikin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya, kamar yadda takardar ta mayar da hankali kan jaridu da wasiƙu da kuma ƙagaggun labaran Hausa.

3.0  Ma’anar Muhimman Kalmomin Bincike

A nan an kawo ma’anonin fitilun kalmomin taken maƙala. Yin hakan ya ba da haske wajen fahimtar inda maƙalar ta dosa da kuma abubuwa da nazarin ya tattauna a kansu.

3.1 Maguɗi

Kalmar maguɗi tana nufin yin amaja wajen aiki ko haɗin abinci (CNHN, 2006:317). Ma’ana dai yin algus ko coge ko ha’inci a cikin wani aiki ko al’amari da ake gudanarwa musamman wanda aka bai wa mai yin sa aminci ko yarda. A cikin Newman(1997: 231) an bayyana ma’anar maguɗi da cewa yin zalunci a zaɓe.

Dangane da wannan takardar kuwa, maguɗi yana nufin yin amfani da wasu hanyoyi da dabaru wajen sauya abin da yake na gaskiya ko na zahiri da wani akasinsa, domin a cuci wani.

3.2 Zaɓe

Kalmar zaɓe kuwa tana nufin ƙuria da ake jefawa don sanin wanda ya fi rinjaye a takara (CNHN, 2006:486-487). Oni (2016: 23) ya bayyana zaɓe da cewa, kimiyya da fasahar jefa ƙuria ne domin zaɓen jam’iyya ko ɗan takarar da aka fi so a cikin siyasar jam’iyyu ko kuma takara a tsarin dimokuraɗiyya. Shi kuwa Ujo (2000: 249) cewa ya yi, zaɓe hanya ce da ake amfani da ita wajen yin zaɓi tsakanin abubuwa biyu ko fiye ta amfani da wasu karɓaɓɓun hanyoyi.

Dangane da wannan bincike kuwa, zaɓe yana nufin tantancewa da jefa ƙuria ga wani mutum wanda ya tsaya takara ƙarƙashin wata jamiyyar siyasa.

3.3 Tarihi

Kalmar tarihi Balarabiyar kalma ce wato (At-tarikh) kamar yadda ƙamusun harshen Larabci Lisan Al-Arab ya bayyana, wanda yake nufin abubuwan da suka shuɗe. CNHN (2006: 428) ya bayyana kalmar tarihi da cewa labarin abubuwan da suka wuce.

Ta fuskar maana ta ilimi kuwa, Carr (1961: 8) ya nuna cewa, tarihi shi ne bin diddigin abubuwa da suka faru na gaskiya ta hanyar samun tabbas daga masanin tarihi. Ana samun tabbas a kan labarin da ya shuɗe ne ta hanyar wanda ya ga abin da ya faru ko ya ji, ko samun kayayyakin tarihi ko rubutaccen bayani da masana tarihi kan rubuta tare da duba lokaci da bagire da jerantuwar tunani a kan labarin, da dai sauransu.

Shi kuwa Mohammed (2013: 53) ya bayyana cewa tarihi ya samu asali ne daga abin da ya shuɗe, saboda ba za mu iya fahimtar duniyarmu ta yau ba sai da sanin abin da ya gabata. Haka kuma gwargwadon zurfafawarmu cikin abin da ya gabata a tarihi, gwargwadon yadda za mu samu haske a kan rayuwarmu ta gaba. Bunza (2018: 175) ya bayyana ma’anar tarihi da cewa, hanya ce ta adana wani abu da ya shuɗe da ake sanar da matasa labarin magabatansu. Adana tarihi abu ne mai muhimmanci da yake taimakawa wajen sanin asalin abu da mutane suke gani a rayuwarsu.

Lawal (2018: 47) ya ce, kafin tarihi ya amsa sunansa na tarihi sai ya cika wasu sharuɗɗa, kamar bayani daga wanda ya ji ko ya gani (oral tradition) ko samun kayan tarihi (Archaeological source) ko rubutaccen bayani daga masana tarihi (written decument). Haka kuma ana laakari da bagire da lokaci da jerantuwar tunani a labarin.

Ta la’akari da ma’anonin da aka kawo a sama, wannan binciken yana da fahimtar cewa, tarihi yana nufin tabbataccen bayani kan faruwar wani abu a wani ayyanannen lokaci da ya shuɗe. Yana iya kasancewa na baka ko rubutacce.

3.4 Siyasa

An bayyana kalmar siyasa da cewa, Balarabiyar kalma ce wadda asalinta daga kalmar “saasa” ne, amma saboda ƙaidar tasarifi na nahawun Larabci sai kalmar ta koma siyaasa, wadda take nufin juyawa a kan wani lamari ko kuma yarda da wani ko jiɓintar al’amarin al’umma tare da saninsu ko ba tare da saninsu ba (Idris, 2016:49).

A cikin Ƙamusun CNHN (2006:397) an kawo maanoni huɗu da suke bayyana siyasa kamar haka:

a.      Tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su.

b.      Rangwame, musamman a ciniki.

c.       Dabara ko wayo.

d.     Iya hulɗa da jama’a.

A ma’ana ta ilimi kuwa, masana da dama sun bayyana fahimtarsu dangane da ma’anar siyasa, inda suka dubi kalmar ta fuskoki mabambanta. Daga cikinsu akwai:

A ra’ayin Mashi (1986:16) ya bayyana siyasa ne ta fuskoki uku: Hanya ta farko ya bayyana ta da ma’anar salo. Sauran hanyoyin kuwa wato ta biyu da ta uku, ya bayyana siyasa da cewa sulhu ko sauƙi. Waɗannan ma’anoni da ya bai wa siyasa ba za su rasa nasaba da yadda siyasa ta kasance hanyar lallashi ko lallaɓa mutane domin neman goyon bayansu ba. Haka kuma ya kalli siyasa a matsayin yaudara ko ƙarya, saboda yadda yan siyasa kan tsara wani lamari na yaudara domin neman biyan buƙata.

Blackburn (1994: 281) ya bayyana siyasa da cewa, tsarin rayuwar alumma ce tare da hukuma, da kuma yadda dangantakar alumma yake da ɗaiɗaikun mutane, inda hakan yake ƙunshe da tsarin nauoin hukumomi kamar samar da doka da oda da dai sauransu.

A ra’ayin Funtua, (2003:19-20) ya nuna siyasa da cewa, ararriyar kalma ce ta Larabci wadda take nufin sauƙi ko rangwame ko jin ƙai. A da, da zarar an ce wa mutum ɗan siyasa to ana nufin mutum mai jin ƙai, kuma mai rangwame, wato dai mutum mai jin tausayin alumma.

Shi kuwa Idris (2016:49) ya bayyana siyasa da cewa hanya ce ta tafiyar da mulkin jama’a a zamanance ko a gargajiyance. Haka kuma dabara ce ta jawo hankalin mutane ta hanyar karkata ta inda suka sa gaba a kowane fage. Misali idan ɗan siyasa ya lura da abin da mutane suka fi so, to shi ma sai ya karkata ta can ko da kuwa da gaske har cikin zuciyarsa ba yana nufin hakan ne ba.

A taƙaice dai, idan aka dubi waɗannan ma’anoni da aka bai wa siyasa za a iya cewa, siyasa tana nufin neman ra’ayin jama’a ta hanyar amfani da lafuzza masu daɗi da suka ƙunshi tausasawa da nuna jin ƙai da rangwame da amfani da hanyar ƙarya da gaskiya, domin samun biyan wata buƙata wadda kan iya kasancewa ta neman shugabancin alumma ko cimma wani buri na rayuwa.

3.5 Maguɗin Zaɓe

Maguɗin zaɓe na nufin dabarun satar ƙuria da ake amfani da su ta kowane hali don ganin abokin ko abokan hamayya ba su samu rinjaye cikin abin da ake yi ba. Yawanci wanda bai yi nasara ba shi ne yake yin koke kan maguɗin zaɓe (Bunza, 2018: 108).  Shi kuwa Awopeju (2024: 7) ya bayyana maguɗin zaɓe da cewa, haramtacciyar hanya ce wadda ta ƙunshi aikata rashin gaskiya domin samun sakamakon da ake buƙata yayin gudanar da zaɓe.

Maguɗin zaɓe tsari ne da yan siyasa da yan takara da kuma jamiyyun siyasa kan yi wa kansu domin samun rinjaye ko damar ɗarewa kan madafun iko ta kowane hali. Ya shafi kowane irin nauin rashin gaskiya a zaɓe kamar cushen ƙuriu da ta da hankalin masu zaɓe ko tayar da hargitsi a lokacin jefa ƙuria domin kawo cikas ga harkar zaɓe (Ejituwu, 1997: 38).

A cikin maƙalar Bello da Bappi (2015: 3) an bayyana cewa, yayin da aka yi maguɗin zaɓe domin kama madafun iko, akan yi ne domin hana abokan hamayya dama. Akan iya ƙwace wannan damar ce ta abokan hamayya idan ya kasance masu zaɓe ba su da iko a kan komai na zaɓen, yayin da waɗanda za su ƙidaya ƙuriu su ne suke da wuƙa da nama a kan ƙuriun da aka jefa. A wannan yanayin akan tuhumi sahihancin zaɓen.

Dangane da wannan nazari, maguɗin zaɓe yana nufin yin amfani da duk wata hanya domin yin ha’inci yayin jefa ƙuria, ko bayan an kammala, ta hanyar ƙara wa wata jamiyya yawan ƙuria ko lalata ƙuriunta domin tauye wanda ya yi nasara da kuma tabbatar da wanda bai samu nasara ba.

4.0 Ra’in Bincike

An ɗora wannan bincike a kan Ra’in Tarihanci (Historicism Theory), wanda masanin falsafa Karl Wilhelm Fredrich Schlegel (1772-1829) ya samar.  Masana da manazarta irin su, Blackburn (1994) da Barry (1995) da Habib (2008) da kuma Lawal (2018) sun ba da ma’anar tarihanci daidai fahimtarsu kamar haka:

A fahimtar Blackburn (1994: 167) ya bayyana ma’anar tarihanci da cewa, hanya ce ta fahimtar abubuwan zahiri na zamantakewa ta yadda za a iya bin diddigin faruwarsu da haɓakarsu, domin ba a iya gane abubuwan zahiri na rayuwa, kamar dimokuraɗiyya ko sassaucin ra’ayi ta la’akari da yadda suke a yanzu, ba tare da kallon tarihinsu ba. Masanin ya nuna cewa sanin tarihin abubuwan da suka faru a cikin al’umma musamman abin da ya shafi salon shugabanci kamar na dimokuraɗiyya ko wasu ra’ayoyi na rayuwa, ba a iya fahimtarsu ta hanyar duban halin da ake ciki a yanzu, dole sai an koma ga tarihi.

Shi kuwa Barry (1995: 170) a tasa fahimtar ya bayyana tarihanci da cewa, wata hanya ce ta ƙulla alaƙa tsakanin matanin adabi da wanda ba na matani ba, sau da yawa masu ɗauke da lokacin tarihi iri ɗaya. Ya nuna cewa, a cikin nazarin adabi ta fuskar tarihanci akan ƙulla alaƙa ne tsakanin matanin adabi wato rubutaccen adabi da wanda ba rubutacce ba. A nan idan aka lura za a ga cewa ta hanyar tarihanci ne ake tabbatar da wani abu da ya faru a cikin tarihi da zamanin da ya faru ta hanyar amfani da matanin adabi.

Habib (2008: 147) a tasa ma’anar ya bayar da wasu siffofi ne da za a iya tantance tarihanci da su, inda ya nuna cewa, dole ne a karanci adabi ta muhallin al’adarsa, da sauran muhallan tattaunawa waɗanda suka kama tun daga siyasa da addini da ƙawa ko kwalliya, da kuma tattalin arziƙi. A nan masanin yana nufin idan har za a yi nazarin adabi ta mahangar tarihanci to wajibi ne a dubi wasu mihimman abubuwa waɗanda akan tattauna a kansu kamar siyasa da addini da tattalin arziƙi da sauransu. A wata ma’ana da Lawal (2018: 34) ya kawo, ya ce, tarihanci yana nufin duba yadda al’amuran tarihi suke a cikin matanin adabi ta hanyar la’akari da rubutaccen tarihi domin samun tabbas.

Ke nan, idan aka dubi waɗannan ma’anonin da aka kawo sama za a iya cewa tarihanci ba wani abu ba ne illa, nazarin wasu al’amuran da suka shafi rayuwa waɗanda suka danganci al’ada da addini da siyasa da tattalin arziƙi da sauran gwagwarmayar rayuwa a cikin matanin adabi ko ba na matani ba ta hanyar duba zuwa ga ingantaccen tarihi.

An fara amfani da ra’in tarihanci ne tun a ƙarni na 18. Rain yana bayani ne a kan yadda tarihi yake bayyana hanyoyi da tsarin rayuwar alumma. Haka kuma, yana bayyana yadda wasu alamurra suka faru a cikin wani zamani, da irin ci gaban da aka samu cikin aladu na can dauri da kuma bayanin wurin zaman wata alumma.

George Hegel (1770- 1831) yana ganin cewa tabbatuwar ‘yancin ɗan Adam shi ne maƙasudin adana tarihi, wanda kuma hakan kan samu ne kaɗai ta hanyar samar da tabbatacciyar ƙasa. A ganin wannan masani, sanin abin da ya faru a baya shi ne yake ba da damar rayuwa cikin yanci da fita daga ƙangin bauta, domin yakan ba da damar fahimtar inda aka fito don a ƙara ɗaura ɗamara zuwa inda aka dosa.

Ƙarƙashin wannan rain an sake samun wani sabon tunani a wuraren shekarun 1980 da aka kira shi da suna Sabon Tarihanci wanda wani Ba’amirke matarki mai suna Stephen Greenblatt ya samar a shekara ta (1980). Greenblatt ya samar da Sabon Ra’in Tarihanci ne a sakamakon wasu nazarce-nazarce da ya gudanar, sai aka buƙaci ya tattara ayyukan ya nazarce su ta fuskar wani rai na musamman, sai ya samar da wannan rai da ya kira Sabon Tarihanci New Historicism a shekarar 1980 (Lawal ,2018:35).

Nazari ta mahangar ra’in tarihanci, shi ne dubi zuwa ga al’amura na tarihi a cikin adabi ta hanyar danganta wannan adabin zuwa ga tarihi na haƙiƙa daga masana tarihi, kuma wannan tarihin ya kasance tabbatace ta sigar rubutu.

Greenblatt (1980:47) ya tabbatar cewa, tarihanci yana ɗauke da manyan ginshiƙai ko tubala guda biyu da ake dubawa a wajen tarken adabi. Ga su kamar haka:

a.     Matsayin Tarihi a Cikin Matani(Historisity of a Text)

b.     Sahihancin Tarihi a Rubutaccen Labari(Textuality of history)

Ke nan, a duk lokacin da ake tarken adabi ta mahangar tarihanci, sai an dubi yadda adabin yake ɗauke da zantuttuka na tarihi a cikinsa, wato yadda aka gina zantuttukan tarihi da nuna su a bisa tarihin na gaskiya. Na biyun kuwa, shi ne a nazarci yadda labarai ko bayanai da aka rubuta suke ɗauke da tarihin da su marubutan suka sarrafa da irin sahihancin wannan tarihin daga tunanin marubutan, wato ya kasance tabbatacce ne ta sigar bayar da labari. A ƙarƙashin waɗannan manyan tubala guda biyu ne ake tarken adabi ta mahangar ra’in tarihanci kamar yadda Greenblatt (1980:47) ya bayyana.

Idan aka dubi ra’in da kyau za a fahimci cewa, da farko an kira shi tarihanci ne kawai, sai bayan tatttara ayyukan da Greenblatt ya yi ne ya sake nazarinsu bisa ra’in na tarihanci sai ya kira su “Sabon Tarihanci”.

Dangane da bambanci tsakanin Tarihanci da Sabon Tarihanci kuwa, Habib (2008: 147) ya ce, mafi yawan abubuwan da suka gabata a ƙarƙashin jagorancin Sabon Tarihanci ba wani sabon abu ba ne, sai dai za a iya cewa yana wakiltar salon nazari da bunƙasar tarihanci na gargajiya da ya gabata ne. Idan aka lura za a fahimci cewa, Sabon Tarihanci ba wani sabon abu ne na daban ba, sai dai za a iya cewa Sabon Tarihanci ci gaban Tsohon Tarihanci ne kawai, domin duk manufarsu ɗaya ce a fagen nazari.

Mabiya wannan mazahaba sun haɗa da: Louiz Montrose da Michael de Montaigne da G. B. Vico da George Hegel. Wasu daga cikin nazarce-nazarce na adabin Hausa da aka gudanar ta mahangar ra’in tarihanci sun haɗa da: Usman (2016) da Bunza (2018) da Yusuf (2018) da Lawal (2018) da Bunza (2018) da kuma Ali (2020)

Wannan ne ya sa aka ga dacewar zaɓen wannan ra’in domin ɗora shi a kan wannan takarda, kasancewar tana bayani ne kan abin da ya shafi maguɗin zaɓe a cikin tarihin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya, wanda ya fito a cikin rubutaccen zube na Hausa.

5.0 Nazarin Tarihin Maguɗin Zaɓe a cikin Rubutaccen Zuben Hausa

A wannan ɓangaren, an yi nazari ne dangane da maguɗin zaɓe a cikin rubutaccen adabin Hausa. An shiga cikin jaridu da wasiƙu da ƙagaggun labaran Hausa inda aka riƙa kafa hujjoji da wasu ɓangarori da suka nuna samuwar maguɗin zaɓe a cikin tarihin siyasar jamiyyu a Arewacin Nijeriya. Dangane da wannan binciken an raba maguɗin zaɓe zuwa manyan kaso guda biyu kamar haka: Hanyoyin gudanar da maguɗin zaɓe da kuma masu gudanar maguɗin zaɓe. Bari mu dubi kowane kaso domin ganin abin da ya ƙunsa.

5.1 Hanyoyin Gudanar da Maguɗin Zaɓe

Maguɗin zaɓe yana cikin abubuwan da suke haifar da tarnaƙi wajen samun cigaban ƙasa, kasancewar akan yi amfani da haramtattun hanyoyi domin daƙile nasarar wanda alumma suke so, ko kuma wanda ya fi cancanta. Maguɗin zaɓe abu ne wanda ya daɗe ana yin sa a cikin tarihin siyasar jamiyyu, duk da cewa akwai hanyoyi daban-daban da ake bi wajen yin maguɗin. Wannan ya danganta da irin yanayi da salon zaɓen da za a gudanar, shi zai ba da damar sanin ko ta wace hanya ce za a bi a yi maguɗi. Alal misali, akan yi zaɓe ta hanyar tsayuwa jere bisa layi, inda akan yi layi daidai da adadin yan takara ko jamiyya, sai a ƙidaya masu zaɓen. Wanda mutane suka fi yawa a layinsa shi ne zai fi samun yawan ƙuriu. Wani salon kuma shi ne, akan fitar da akwati da za a jefa wa ƙuria da alamar jamiyya a jikinsa. Adadin jamiyyun da suka shiga zaɓen shi ne adadin akwatin da za a kawo, kowanne da alamar jam’iyyarsa a jiki. Masu jefa ƙuria kuma idan sun zo sai mutum ya duba alamar jamiyyar da yake goyon baya ya jefa tasa ƙuriar a cikinsa. Haka kuma akan yi amfani da takardun jefa ƙuria wanda suke ɗauke da sunan jamiyya da alamarta da kuma matakin da za a jefa wa ƙuriar, wato ko dai ya kasance na shugaban ƙasa ko gwamna ko kuma na yan majalisu ko shugabannin ƙananan hukumomi kamar dai yadda tsarin yake a jamhuriya ta huɗu.

Ta la’akari da kowane salo na zaɓe ne akan yi amfani da hanyar da akan yi maguɗin da ita. Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen gudanar da maguɗin zaɓe akwai:

5.1.1 Sace Akwatunan Zaɓe

Akwatin zaɓe shi ne mazubin ƙuriu da ake amfani da shi domin jefa dukkan wata ƙuria da aka zaɓa. A cikin wannan akwatin akan sanya ƙuriar da kowane ɗan takara ya samu, wanda kuma su ne za a ƙirga domin a iya gane wanda ya yi nasara da wanda bai yi nasara ba a zaɓen. Akan yi amfani da wannan akwatin wajen gudanar da maguɗi ta hanyar sace shi daga rumfar zaɓe ko kuma ma kafin a kai fa kawo shi rumfar zaɓen. Akan yi haka ne domin a raunana ƙuriun abokan hamayya. Irin wannan batun ya fito a cikin jaridar Aminiya kamar haka:

Haka kuma su ke shirya mutane su sace akwatunan zaɓe, su yi dangwalen ƙarya, kamar kuma yadda suke buga takardun zaɓe na bogi. (Baba-Aminu da Ahemba da Salifu da Bivan da Malumfashi, 2014).

A cikin wannan misalin an bayyana hanyar maguɗin zaɓe wadda akan shirya wasu mutane da sukan je su sace akwatunan zaɓe. Da dama idan aka sace akwatin akan yi amfani da shi ne a yi zuba ƙuriun wanda aka ga dama ko kuma a lalata ƙuriun wanda ba a so ya kai ga nasara maimakona a bari a yi zaɓen don fitar da wanda ya yi nasarar na gaskiya. Akan yi amfani da takardun zaɓe na jabu waɗanda aka buga domin aiwatar da irin wannan maguɗin.

5.1.2 Amfani da Kayayyakin Zaɓe na Bogi

Idan aka yi nufi yin magudin zaɓe, tun kafin lokacin zaɓen ya zo akan tanadi wasu abubuwa daga cikin kayan aikin zaɓe wanda akan yi amfani da su wajen gudanar da maguɗin. Irin waɗannan kayayyakin hukumar zaɓe ne kaɗai take da alhakin samar da su domin gudanar da zaɓe. ‘Yan siyasa sukan tanadi irin waɗannan kayayyakin domin su yi amfani da su hankali kwance. Sukan shirya tare da aiwatar da maguɗin ne idan suka lura sakamakon da jama’a za su samar ba zai masu daɗi ba. Dubi wannan misalin:

Da farko dai mun bi hanyar da za mu bi mun samo samfurin akwatin zaɓe, kuma a yanzu haka a cikin sutona na gidan gonata mun tara namu akwatin irin na hukumar zaɓe, waɗanda sai ranar zaɓe za mu baza su lungu da saƙo na ƙasar nan. (Surajo, 2006: 109).

A nan Shugaban jam’iyyar JHC ne yake bayanin irin shirin maguɗi da suka yi. Ya nuna cewa, sun bi duk hanyar da za su bi sun samu nau’in akwatin da za a yi amfani da shi a zaɓen, suka kuma tanade su. Ya nuna cewa sun tanadi irin akwatunan da hukumar zaɓe za ta yi amfani da su, an ɓoye su, sai ranar zaɓe za su raba akwatunan a ko ina cikin ƙasar. Irin wannan tanadin kayan zaɓe na bogi hanya ce ta maguɗin zaɓe. Da kayan ne akan yi amfani domin yin maguɗi, maimakon amfani da wanda hukumar zaɓe za ta raba ranar zaɓe. Irin waɗannan akwatunan zaɓen ba a kai su filin zaɓe, maimakon haka akan samu wani wuri ne a ɓoye su, inda za a cika su da ƙuriun da aka dangwala wa jamiyyar da ake so ta yi rinjaye. Da zarar an kammala zaɓe za a tafi da akwatin zaɓe, sai a san hanyar da za a bi musanya akwatin da al’umma suka kaɗa ƙuriunsu a ciki da wannan akwatin da aka dangwale ƙuriun maguɗin a cikinsu. Akan musanya idan aka samu ƙarancin masu sanya ido daga jam’iyyar hamayya ko kuma a yi amfani da jami’an tsaro ko ‘yan banga wajen tayar da yamutsi wanda hakan zai ba da damar a sauya akwatin zaɓen da na bogi.

Bugu da ƙari, takardun ƙuriu suna daga cikin kayan aikin zaɓe wanda akan raba, kuma da su ne ake jefa ƙuria. Su ma irin waɗannan takardu akan samar da na bogi wanda akan tanada tun kafin ranar zaɓe, wanda za a dangwale wa jamiyyar da ake so ta yi nasara. Bayan an dangwala wa jamiyyar sai a yi amfani da ƙuriun ta hanyar dabara a kai su rumfar zaɓe tare da zuba su cikin akwatin ɗan takarar da ake so ya samu rinjaye. Irin wannan ya fito a cikin littafin Siyasa Waina Ce kamar haka:

Idan kuka isaTele, kada ku tsaya sai kun kai Tsamiya. Da kun kai Tsamiya, ku ɗau ƙunshi guda daga cikin jakar ku zurara katunan ƙuriu da ke ciki a akwatin YKK na ɗakin zaɓe da ke can bayan gari. In kuka gama wannan, sai ku juyo ku zuba ƙunshin guda a akwatin YKK da ke ƙofar gidan Sakatarenmu na can Tele. Ɗayan da ya rage ku zuba a akwatin zaɓen YKK na ɗan ƙauyen nan Shayi da ke kan hanya. Daga nan sai ku dawo abinku. (Zukogi, 1994: 23).

Wannan misalin da yake sama ya nuna yadda akan yi amfanin da ƙuriun bogi ta hanyar yin cushe a cikin akwatin zaɓe domin yin maguɗin zaɓe. A nan an nuna magoya bayan jamiyyar YKK ne, wato Bogi da Nako waɗanda aka ba su aikin kai ƙuriun bogi domin yin maguɗi da su bayan an haɗa baki da maaikatan zaɓe na rumfunan. An shirya amfani da waɗannan rumfunan ne domin aiwatar da maguɗi kasancewar ba koina ne ake iya shirya irin wannan maguɗin, kuma ya yiwu ba. Yawanci akan duba inda aka san magoya bayan jamiyyar da za ta yi maguɗin ba su da rinjaye, sai a haɗa baki da maaikatan zaɓen domin aiwartarwa ba tare da masu zaɓen sun ankara ba.

5.1.3 Amfani da ‘Yan Bangar Siyasa

An sake nuna irin wannan salon maguɗin a cikin littafin Siyasarmu a Yau, sai dai a ciki marubucin bai kawo batun amfani da hikima da dabara wajen yin cushen ƙuriun ba, maimakon haka sai ya nuna cewa an yi amfani da yan banga ne ta hanyar nuna ƙarfin makami. Dubi abin da marubucin ya ce:

Kowace mota ƙirar Jif ce, akwai kayan aiki a ciki, tare da akwatunan zaɓe da takardun zaɓen a ciki. Idan kun tuna jiya, kun yini kuna cike takardun zaɓe da sunan bogi, amfanin da za ku yi da shi ne, gobe idan kowane ya je gun da na ba shi ya kula da ɓangarensa, kuma akwai wayar sadarwa wanda za mu dinga musayar bayanai da ku. Idan kun tabbatar da cewa zaɓe yana tafiya daidai watau jamiyyata tana kan gabato shi ke nan, amma idan kun ga cewa jam’iyyar adawa ce a kan gaba to ku tashin hankalin jama’a da harbe-harbe. Idan jama’a sun tarwatse to sai ku yi ƙoƙarin ɗauke akwatunan zaɓen ku zuba tawa... (Kabara, 2005: 33).

Salon maguɗin da aka nuna a wannan misalin da yake sama ya bambanta da wanda ya gabace shi. A wannan an nuna cewa ɗan takarar shugaban ƙasar Gashi, Alhaji Naso shi ne ya tara yan bangarsa yake nuna masu hanyar da suka shirya yin maguɗin zaɓe matuƙar aka lura ba jamiyyarsu ce za ta yi nasara ba. An nuna sun tanadi motocin da za su yin amfani da su, waɗanda suke ɗauke da kayan zaɓe da suka ƙunshi akwatunan zaɓe da katunan ƙuriu waɗanda za su yi amfani da su a duk inda suka lura cewa jamiyyarsu ba za ta yi nasara ba. Haka kuma, ɗan takarar ya ba su makamai da za su yi amfani da su wajen tarwatsa masu zaɓe bayan sun lura cewa ba su suke da rinjaye a rumfar ba. Bayan sun kora jamaa sai su sauya akwatunan zaɓen da nasu.

Wannan wata hanyar maguɗi ce da aka riƙa amfani da ita a cikin tarihin ginuwar siyasar Arewacin Nijeriya. An riƙa amfani da yan banga wajen aiwatar da irin wannan salon maguɗin zaɓen, inda sukan tayar da hankali a duk rumfar da suka lura ba su ne suke da rinjaye ba. A wasu lokuta ma ba wani akwatin zaɓen sukan zo da shi ba, amma tun da sun lura ba za su yi nasara a wannan rumfar zaɓen ba, sai su tayar da yamutsi ta yadda za a fasa akwatin, a lalata ƙuriun kowa ya rasa.

5.2 Masu Yin Maguɗin Zaɓe

Maguɗin zaɓe ba ya yiwuwa in ba tare da haɗin bakin masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen ba. ko dai ya kasance maaikatan gwamnati da suke aiki a ƙarƙashinta waɗanda akan tura a matsayin jamian zaɓe, ko kuma a ɗora masu wani aiki da ya shafi aikin zaɓen. Ko waɗanda suke aiki da hukumar da take shiryawa tare da aiwatar da zaɓen, ko kuma maaikatan tsaro da aka ɗora alhakin sanya ido da kula da rayukan alumma a lokacin zaɓe da ma bayan zaɓe. Da dama idan aka rasa haɗin kan waɗannan kason na alumma to maguɗin zaɓe zai samu cikas. Wannan ya sa wannan binciken ya yi amfani da rubutaccen zube domin kafa hujja a kan waɗannan ɓangare na alumma a matsayin masu aiwatar da maguɗin zaɓe.

5.2.2 Ma’aikatan Gwamnati

A cikin tsare-tsaren zaɓe an riƙa amfani da ma’aikatan gwamnati tun daga jamhuriya ta farko domin aiwatar da maguɗin zaɓe. An samu hujjojin da suka fito da waɗannan batutuwa a cikin rubutattun ayyukan adabin Hausa. Alal misali, a cikina jaridar Daily Comet an samu wani bayani a kan abin da ya shafi yunƙurin maguɗi a zaɓen yan majalisar wakilai da aka gudanar a shekarar 1961. Ga bayanin kamar haka:

Ranar Juma’a da ta wuce majalisar Jihar Arewa ta zartar da cewa a zabe mai zuwa na majalisar wakilai, Hakimai ne za su nada wakilan akwatunan zabe har da na abokan hamayya, mai makon shi mai shiga zaben ya bada wakilinsa, amintaccensa. Kuma gwamnati ta ƙara da cewa wai Hakimai su ne za a bai wa ikon takardun kuria... Wannan ya tabbatar mana cewa gwamnatin NPC ta tsorata da yan hamayya, don haka ta shirya yadda ta ga yafi yi mata daidai in an duba siyasar kasannan za a ga Hakimai ne suke shiga zabe da sunan NPC ashe kuwa hauka ne a ce za a baiwa abokin gaba kayan fada. Kuma zai zama abin dariya idan aka ce abokin gabarka shi ne wakilin ka, wajen duba akwatunan zabe. (Hakimai Ne Za Su Nada, 1961).

Idan aka yi la’akari da wannan bayanin, za a fahimci cewa ba hakimai dama cikin gudanar da ayyukan zaɓe wata dama ce da za su tafka maguɗi cikin zaɓen da za a gudanar. Hakimai da sarakuna a wancan lokaci a ƙarƙashin gwamnati suke, wadda jamiyyar NPC ta kafa.

Ayyana hakimai a matsayin waɗanda za su naɗa wakilan akwatunan zaɓe na duk jamiyyun siyasa na wancan lokacin (1961), ya tabbatar da cewa, ana samun sa hannun jami’an gwamnati a cikin maguɗin zaɓe. Ba yadda za a yi wani cikin hakiman ya yarda a faɗi akwatinsa domin ya san bakin rawaninsa ke nan. Don haka ko ta halin ƙaƙa sai ya tabbatar jamiyyar gwamnati ta yi nasara a mazaɓarsa, domin ya tsira da rawaninsa.

A cikin misalin da yake sama idan aka lura za a ga cewa, ‘yan hamayya sun riga sun nuna cewa idan har ya kasance hakiman ne za a danƙa wa kula da alamuran zaɓen to sun tabbatar jamiyya mai mulki ta ƙulla wani abu na rashin gaskiya ne. Don haka take neman hanyar da za ta shirya abin da zai yi mata daɗi kawai. Bai wa hakiman kula da al’umaran zaɓen tamkar bai wa abokin gaba ne kayan faɗa. A cikin misalin an nuna cewa, zai iya zama abin dariya a ce abokin hamayya kuma shi ne wakilin da za a sanya ya tsaya a madadin abokin hamayyarsa, wanda kuma ake sa rai shi ne zai tabbatar da an yi wa wannan abokin hamayyar tasa adalci a akwatin zaɓe.

Idan aka dubi wannan batun da aka kawo za a gane cewa, maguɗin zaɓe ne aka shirya domin a tabbatar jam’iyya mai mulki ta wancan lokacin wato NPC ta samu rinjaye a zaɓen yan majalisar, domin in ba maguɗi ba ne, ya kamata a bai wa kowane ɓangare damar kawo wanda zai sanya ido a kan akwatinsa domin kada a samu matsala. Maimakon haka sai aka sanya waɗanda da su za a shirya yadda za a kayar da jamiyyar hamayya.

Dangane da wannan batu da aka kawo misali da shi a sama, jaridar Daily Comet ta yi kira ga ‘yan hamayya na jam’iyyun NEPU da Action Group da NCNC, a kan su fito su mayar da martani ta hanyar nuna rashin jin daɗinsu a kan yunƙurin da gwamnati ta yi, wanda a ganin jaridar wannan tsarin da gangan aka kitsa shi domin tafka maguɗin zaɓe. Dubi abin da jaridar ta ce:

Ya zama wajibi ‘yan hamayya musamman na NEPU, NCNC da Action Group su san sabuwar dabara. Mu baza muce ga yadda zasu yi ba, hausawa suna cewa mai kai shi yasan makafar zanko. Amma kuma tilas ne wannan jarida ta la’anci kuma ta tsine dukan mutanen da suke nufin zaluntar na bayansu ko da wane irin zalunci ne. Lalle ne Talakawa da jam’iyoyin siyasa su gane wannan kullin da ake yi masu na nufin a zambace su. (Hakimai Ne Za Su Nada, 1961).

Jaridar ta bayyana cewa, wannan tsari da jam’iyya mai mulki ta fito da shi na miƙa ikon kula da akwatunan zaɓe da takardun jefa ƙuria a hannun hakimai, dole jam’iyyun hamayya su tashi tsaye wajen ganin hakan bai tabbata ba. Jaridar ta ce, an shirya bai wa hakiman kula da akwatunan zaɓen ne domin a zambaci sauran jam’iyyu masu hamayya. Zamba a nan yana nufin maguɗin zaɓe ne aka shirya. Duk da cewa jaridar ta yarda cewa gwamnati tana da ikon tsara abubuwanta yadda ta so domin ta san abin da ya kamata ta yi, amma kuma ya kamata ta yi adalci.

5.2.1 Ma’aikatan Zaɓe

Ma’aiakatan zaɓe sukan kasance na wucin gadi waɗanda akan ɗauka domin aikin zaɓen wannan kakar zaɓen kaɗai. Akwai kuma waɗanda suke maaikatan hukumar ne na dindindin, waɗanda suke aiki da hukumar kodayaushe. Duk waɗannan nauoin maaikatan hukumar akan yi amfani da su domin gudanar da maguɗin zaɓe. Hanyar da ake bi domin yin irin wannan maguɗin zaɓen ita ce, ma’aikatan hukumar zaɓe sukan miƙa wuya bayan an saye su da kuɗi da wasu manyan kyaututtuka da sauransu. Irin wannan misali ya bayyana a cikin littafin Da Bazarku inda aka nuna wasu manyan ‘yan siyasa wato Sanata Bolton da Lauya Uba da kuma Cif Kolade suke tattauna hanyoyin gudanar da maguɗin zaɓe cikin ruwan sanyi. Ga abin da suka ce:

...sannan kuma bugu da ƙari tuni mun riga mun saye wasu daga cikin manyan maaikatan hukumar zaɓe ta ƙasa, da kuɗi da kuma kyaututtuka na gidaje tare da yi masu alƙawarin ɗasawa da su idan mun kama ragamar mulki... Murɗiyar zaɓe ba yau muka fara ba, don haka kuwa a yau ba za mu ji kunya ba. (Surajo, 2006: 17).

A nan Sanata Bolton ne yake bayyana tsare-tsaren da suka riga suka yi na aiwatar da maguɗin zaɓe. Sanata Bolton ƙwararre ne kan harkar zaɓe wanda aka ɗauko hayarsa daga ƙasar Amurka, don ya tsara hanyoyin da za a shirya maguɗin zaɓe. A cikin bayaninsa ya nuna cewa, daga cikin hanyoyin maguɗin zaɓe akwai saye maaikatan hukumar zaɓe ta yadda za su ba da ƙofar da za a yi murɗiya ba tare da an samu wata matsala ba. Akan ba su toshiyar baki na kuɗi da gidaje da wasu manyan kyaututtuka har ma da alƙawarin gudanar da gwamnati tare da su. A ƙarshe ma har wani iƙirari ya yi cewa ba su suka fara murɗiyar zaɓe ba wato an saba tun a baya ana yi, don haka za su tabbatar shirin maguɗin da suka yi ya yi nasara.

A wani misalin dangane da yadda ma’aikatan zaɓe suke gudanar da maguɗin zaɓe, a cikin littafin Dambarwar Siyasa an nuna yadda wata budurwa mai suna Nabila ta naɗo wa ɗan takarar jamiyyar hamayya hujjar bai wa jamian zaɓe cin hanci domin su murɗe zaɓensa, a bai wa wani daban wanda ba shi ne ya yi nasara ba. Dubi wannan misalin:

A cikin wannan Memory card ɗin akwai bidiyoyi da dama da suke nuna lokacin da ake ba jamian zaɓe cin hanci domin murɗe zaɓen yau. (Aminiya-Trust, 2020: 109).

Nabila ‘yar Alhaji Maikwabo ce, wato ɗantakara a jamiyyar RPC mai mulki, sai dai ta kasance tana goyon bayan ɗan takaran jamiyyar hamayya ta NCC, wato Abubakar Mai-Allah wanda ya kasance malaminta na darasin government lokacin tana sakandire. Wata rana, yayin da ake tsaka da shirya maƙarƙashiyar yadda za a yi wa jamiyyar NCC maguɗi ta yi amfani da kyamara ta yi rikodin bidiyo na duk maƙarƙashiyar da aka shirya wa jamiyyar hamayya. Daga cikin maƙarƙashiyar da aka shirya har da bai wa jamian zaɓe cin hanci domin a murɗe zaɓen. A cikin misalin da yake sama an nuna cewa daga cikin hanyar maguɗin zaɓe akan yi amfani da jamian zaɓe domin a murɗe zaɓe, ta hanyar ba su cin hanci domin samun sakamako na ƙarya ga wanda bai cancanta ba.

5.2.3 Jami’an Tsaro

Aikin jami’an tsaro ne shi ne tabbatar da zamna lafiyar ƙasa ta hanyar kula da tsaron lafiya da dukiyoyin alumma. Wannan ya sa a lokacin gudanar zaɓuɓɓuka akakn tura su domin su tabbatar alamuran zaɓe ya tafi bisa tsarin doka. An bayyana cewa an tafka maguɗin zaɓe mai yawa jamhuriya ta biyu, inda aka nuna cewa babu jam’iyyar da ba ta yi amfani da wata hanyar maguɗi ba sai dai wadda ba ta samu dama ba[1]. A wannan kakar zaɓen na jamhuriya ta biyu sojoji ba su sanya hannu wajen tabbatar da doka da oda a wajen gudanar da zaɓuɓɓukan ba, wanda hakan ya haifar da matsaloli da dama, kuma yan siyasa suka ci karensu babu babbaka. Waɗanda ma ba su tsoma hannu cikin maguɗin zaɓe a zaɓen 1979 ba sun shiga a zango na biyu. Hakan ne ma ya haifar da juyin mulkin da ya kawo ƙarshen wannan jamhuriyar.[2]

 An riƙa samun zarge-zarge da suke nuna cewa jamian tsaro suna da hannu dumu-dumu a cikin ayyukan maguɗin zaɓe. Alal misali, a jamhuriya ta huɗu an samu irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen na cewa, jam’iyyar PDP tana yin amfani da jami’an tsaro wajen tafka maguɗi a zaɓuɓɓuka. Dubi abin da jaridar Aminiya ta ruwaito:

Hukumar zaɓe ta zargi hukumomin tsaro wato yan sanda da jamian fararen kaya na S.S.S da laifin taimakawa game da maguɗin da aka tafka a zaɓen gwamnoni da na yan majalisu da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata. (Mijinyawa, 2007).

Hukumar zaɓe hukuma ce mai zaman kanta, wadda take da alhakin shirya zaɓuɓɓuka a dukkan matakai. Ita ce take da alhakin tura maaikatanta kowane lungu da saƙo domin gudanar da zaɓuɓɓukan da aka shirya. A wannan misalin da yake sama an nuna cewa hukumar zaɓen ce ta zargi hukumomin tsaro na yan sanda da na S.S.S. da laifin taimakawa wajen aikata maguɗi a zaɓe na shekarar 2007 da aka gudanar. Jami’an tsaro aikinsu shi ne tabbatar da doka da oda a ƙasa. Aikinsu ne su tabbatar lokacin gudanar zaɓuɓɓuka an yi lafiya ba tare da samun rikici ko wasu abubuwan da suka saɓa wa doka ba, amma hukumar ta yi zargin an haɗa kai da su an yi maguɗi a zaɓen gwamnoni da na yan majalisu da aka gudanar a wannan lokacin. Wannan zargin da hukumar zaɓe ta yi ya ƙara tabbatar da samuwar maguɗin zaɓe a jamhuriya ta huɗu.

Wani misalin da yake nuna yadda maguɗin zaɓe ya ginu a cikin tarihin siyasar Nijeriya shi ne, yadda aka riƙa kama shugabannin jamiyyar hamayya ana kullewa ta hanyar amfani da jamian tsaro, a matsayin wata hanya ta gudanar da maguɗin zaɓe, kuma ba a sakinsu sai bayan an kammala zaɓe. Dubi abin da jaridar Aminiya ta ranar 26 ga Disamba 2014 ta wallafa:

...kuma muna sane da cewa babu abin da PDP ta iya illa maguɗin zaɓe, ta tura ma’aikatan tsaro marasa gaskiya, waɗanda suke kama shugabannin jamiyyun hamayya suna kullewa, su sake su bayan an kammala zaɓe. (Baba-Aminu da wasu, 2014).

A cikin misalin an nuna cewa ana amfani da jami’an tsaro wajen kama ‘yan hamayya da kuma tsare su har bayan kammala zaɓe, wanda hakan zai ba damar gudanar da dukkan wani nauin maguɗi tun da babu masu faɗa a ji ko kuma manyan masu sanya ido na jamiyyun hamayya. Irin waɗannan mutanen da jami’an tsaro sukan kama, a tsare har sai bayan zaɓe a sako su, akan lura da irin rawar da za su taka ne a cikin zaɓuɓɓukan, kasancewar su masu faɗa a ji a cikin jamiyyar. Wani lokaci kuma akan kama su ne domin sun san sirrin yadda ake yin maguɗin, don haka barin su ba tare da an kama su an tsare ba zai iya kawo wa abokan hamayya tarnaƙi.

6.0 Sakamakon Bincike

Idan aka dubi bayanan da aka kawo a sama za a fahimci cewa, maguɗin zaɓe yana cikin abubuwan da suke hana samun cigaba a siyasa domin kuwa, hanya ce da ake tauye wa al’umma haƙƙinsu da kuma hana su kai ga muradinsu. Duk wanda ya san ba zaɓen sa aka yi ba, ko kuma alumma ba shi suke so ba, to bai cika tsayawa ya yi abin da alumma suke buƙata ba. Wannan yakan sa alummar ƙasa su yi ƙasa a guiwa wajen jajircewa don tabbatar da adalcin shugabanni, domin kuwa shugabannin sun san cewa ba zaɓensu aka yi ba, kuma ko da ba su yi wa alumma abin a-zo-a-gani ba za su sa rai da za su iya ɗorewa a kan mulki ta hanyar da suka hau.

Kasancewar wannan binciken na tarihi ne, an fahimci cewa maguɗin zaɓe daɗaɗɗen alamari ne a cikin siyasar Arewacin Nijeriya, domin kuwa an samu bayanansa tun daga farkon siyasar jam’iyyu wato a jamhuriya ta farko. An ci gaba da amfani da wannan hanyar ta maguɗi a cikin zamunnan siyasar da aka samar wato na ɗaya zuwa na huɗu har zuwa yau.

Haka kuma, binciken ya gano waɗansu hanyoyi da ake amfani da su wajen aiwatar da maguɗin zaɓe. Akan yi amfani da wata hanya idan wata ba ta ɓulle ba, ko kuma a yi amfani da su lokaci guda domin a tabbatar jamiyyar da ake wa wannan fafutukar ta samu rinjaye. Hanyoyin sun haɗa da satar akwatin zaɓe, da tanadar kayan zaɓe na bogi da kuma amfani da ‘yan bangar siyasa.

Bugu da ƙari, binciken ya gano waɗansu da akan haɗa baki da su wajen yin maguɗin zaɓe ta fuskoki mabambanta kamar su jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati, da ma’aikatan zaɓe da sauransu.

Binciken ya gano cewa, samuwar maguɗin zaɓe a cikin tsarin siyasar Arewacin Nijeriya yana cikin abubuwan da sukan kashe wa wasu yan siyasa jiki wajen dagewa domin fafutukar neman matsayi, kasancewar akasarin waɗanda suke yin maguɗi masu riƙe da madafun iko ne, domin neman tabbata a kan mulki ta kowane hali. Wannan ya sa wasu suke ganin hamayya da gwamnati tamkar ɓata lokaci ne, domin sukan yi amfani da ƙarfin mulki wajen yin duk wani nauin maguɗi domin samun nasara.

7.0 Naɗewa

Wannan takarda ta tattauna a kan maguɗin zaɓe a cikin tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya. Tun da farko a cikin gabatarwa an kawo taƙaitacciyar shimfiɗa a kan maguɗin zaɓe. Daga nan sai aka kawo ma’anonin kalmomin bincike domin ya ba da damar fahimtar inda maƙalar ta fuskanta. Daga bisani sai aka tsunduma cikin nazarin maguɗin zaɓe a cikin tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriy. An kasa bayanan zuwa gida biyu manya, wato hanyoyin gudanar da maguɗin zaɓe da kuma waɗanda suke gudanar da maguɗin zaɓe, inda aka riƙa kawo misalai daga rubutaccen zube na Hausa.

Manazarta

Ali, B. Y. (2020) Cuɗanyar Adabi da Al’ada: Nazarin Tarihi a Cikin Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa. A cikin Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies. Vol.2 no.3, December 2020. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Shafi na 291-300.

Aminiya-Trust (2020) Dambarwar Siyasa. Kaduna: Tast and Print Ventures.

Awopeju, A. (2024) From Election Rigging to Vote Buying: Evolving Decay of a Dysfuntional Electoral Process in Nigeria. https://www.researchgate.net/publication/383438553_

Baba-Aminu, A., Ahemba, T., Salifu, U. F., Bivan N., Malumfashi, B. Y. (2014, Disamba 26) Za Mu Tabbatar Da A Kasa A Tsare A Zaɓe. Jaridar Aminiya, shafi na 2.

Barry, P. (1995) Beginning Theory: An Introduction to Literary and Cultural Theory. London: Manchester University Press.

Ba Za Mu Yi Maguɗi a Zaɓe Mai Zuwa Ba. (2007, Fabrairu 2). Jaridar Aminiya, shafi na 5.

Blackburn, S. (1994) Oxford Dictionary of Philosophy. New York: Oxford University Press.

Bunza, U. A. (2018). Auratayyar Zube da Tarihi a Littafin Ganɗoki na Bello Kagara. A Cikin Ife Journal of Languages and Literature. Vol. 4 no.1, December 2018. Department of Linguistics and African Languages, Obafemi Awolowo University, Ile-Ife. Shafi na 174-183.

Bunza, D. B. (2018) Tarihi A Rubutaccen Adabi: Nazari A Kan Rayuwar Kyaftin Umaru Da Suru Daga Waƙoƙinsa. Kundin digiri na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

CNHN (2006) Ƙamusun Hausa na Jamiar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Carr, E. H. (1961) What is History? England: Penguin Books Ltd.

Micheal, E., da Ogunrotimi, O., da Roland, U. A. (2023) Electoral Rigging and Violence in Nigeria in Historical Perspective: A Case Study of 1959, 1964, 1965 and 1983. A cikin International Journal of Multidisciplinary Research and Analysis, Volume 06 Issue 01 January 2023.

Ejituwu, C. N. (1997). Election Process and Governance: Election Rigging in the USA And Nigeria. In: Oyin Ogunba (ed.), Governance and the Electoral Process: Nigeria and the United States of America, Lagos: American Studies Association of Nigeria.

Gowon Ya Yi Tir Da Zaɓen Da Aka Yi. (2007, Mayu 4-10). Jaridar Aminiya, shafi na 1.

Greenblatt, S. (1980) Renaissance Self-Fashioning: From More to Shakespeare: Chicago: University of Chicago Press.

Habib, M.A.R. (2008) Modern Literary Criticism and Theory: A History. UK: Blackwell Publishing.

Hakimai Ne Za Su Nada Wakilan Akwatunan Zaben 1961. (1961, Maris 11). Jaridar Daily Comet, B.sh.

Ibn Manzur (B. Sh) Lisan Al-Arab. Vol. vi. Lebanon: Dar Sar Publishers Lebanon.

Idris, Y. (2016). Bijirewa A Waƙoƙin Siyasa: Bincike Kan Waƙoƙin 1903-2015. Kundin Digiri na Uku. Sashen Harsuna da Aladun Afirka. Zaria: Jamiar Ahmadu Bello.

Kabara, A. M. C. (2005). Siyasarmu a Yau. Kano: Government Printers.

Lawal, N. (2018). Adabi da Tarihanci: Nazarin Wasu Wasanni na Rudolf Prietze. Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Maƙera, S. da Agbese, A. da Jimoh, A. (2013, Maris 1) PDP Ta Yi Shirin Ci Gaba Da Mulki Ko Ta Halin Ƙaƙa. Jaridar Aminiya, shafi na 26.

Mashi, M. B. (1986). Waƙoƙin Baka na Siyasa, Dalilansu da Sababinsu ga Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero.

Mijinyawa, I. (2007, Afrilu 20). Jami’an Tsaro Sun Taimaka Wajen Maguɗi. Jaridar Aminiya, shafi na 7.

Micheal, E., Ogunrotimi, O., Roland, U. A. (2023). Election Rigging and Violence in Historical Perspective: A Case Study of 1959, 1964, 1965 and 1983 Elections. International Journal of Multidisciplinary Research and Anlysis. Shafi na 28-36. DOI: 10.47191/ijmra/v6-i1-04.

Mohammed, K. (2013). The Role of History, Historiography and Historian in Nation Building. A cikin International Journal of Humanities and Social Science Invention, Volume 2, Issue 7. https://www.ijhssi.org/papers/v2(7)/Version-2/J0272050057.pdf

NPN za ta ba da Haske kan Maguɗin UPN. (1980, Yuni 9). Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, shafi na 11.

Newman, R. M. (1997) An English-Hausa Dictionary. Lagos: Longman Nigeria PLC.

Oni, M. A. (2016). Election and electoral process. In Yagboyaju, D., Ojukwu, C., Salawu, M., &Oni, E. (eds.). fundamentals of politics and governance. Lagos; concept publications.

Surajo, B. I. (2006). Da Bazarku. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Ujo, A. A. (2000). Understanding the 1998-99 election in Nigeria. klamidas: Indiana University

Usman, M. Y. (2016). Waƙa: Tubalin Gina Tarihin Ƙasar Hausa. Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Yusuf, J. (2018). Tarihin Jam’iyyar PDP A Bakin Marubuta Waƙa. Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo.

Zukogi, A. A. (1994). Siyasa Waina Ce. Ba Maɗaba’a.



[1] Bayanin yana cikin takardar Awopeju, A. (2024) From Election rigging to Vote Buying: Evolving Decay of a Dysfunctional Process in Nigeria. A cikin Innovations, Number 76 March 2024. www. Journal-innovetions.com.

Post a Comment

0 Comments