Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Alhaji Sa'idu Muhammad Bako

ALLAH YA JIƘAN "TARA GARI ƊAN MAMMAN ", AMIN.

An haifi Alh. Sa'idu Muhammad Baƙo a garin Kwantagora ta Jihar Neja a shekarar 1934.

Mahaifinsa shi ne Malam Muhammadu Sarkin Zagin Kwantagora.

Ya yi karatun addinin musulunci mai zurfi ya kuma yi karatun zamani a matakin firamare. Tun ya na ƙaraminsa ya ke da ƙwazon neman nakai ta hanyar sarrafa taro sisin dake shigo shi. Wannan ne silar azama da nasibinsa a fuskar kasuwanci.

Ya yi sana'o'i daban daban ciki kuwa har da siye da siyar da kayan abinci irin su Hatsi da Wake da sauransu kafin daga baya ya tsunduma a cikin sha'anin kwangilar ciyar da Sojoji a Barikinsu daban daban.

Irin wannan zirga-zirga ce ta sanya shi barin Kwantagora zuwa yankin kudu maso gabascin Nijeriya kamar su Inugu da Aba da Umma'ahiya inda ya haɗu da sojoji 'yan asalin Jihar Arewa tun suna ƙananan hafsoshi kamar su Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Aliyu Muhammad Gusau suka ƙulla abotar da bata yanke ba har bayan wafatinsa.

Kamar yadda muka ambata a sama ya samu shiga sosai a sha'anin kwangilar gidan Soja dalilin waɗannan aminai da yayi musamman a lokacin yaƙin basasa na Nijeriya (1967-1970).

Bayan kammala wannan yaƙi Alhaji Sa'idu Baƙo Muhammad ya ci gaba da kasuwancinsa da kuma ayyukan kwangila a matakin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatotan wasu Jihohi cikin iyawar Allah SWT ya zama hamshaƙin mai kuɗi ba wai a Jihar Neja ba kawai har ma a Nijeriya gaba ɗaya.

Bahaushe ya na cewa "A bayar a rasa ta hanawa raggo suna". Allah ya yi Alhaji Sa'idu Baƙo Muhammad jarumi kuma karimin dattijo. Nan take alherinsa ya game kowane sashe na arewacin Nijeriya.

Tun daga Adamawa da Taraba zuwa Borno Gombe da Yobe da Bauchi da Jigawa da Kano da Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Plateau da Nasarawa da Kogi da Kwara da Benue babu Jihar da wannan bawan Allah bai ƙulla zumunci da muhimman mutanensu ba.

Alheri da aikin tawali'unsa musamman wajen ci gaban addinin Musulunci da fitar da al'umma daga cikin ƙangin fatara ya sanya sunansa ya yi amo sosai musamman a lokacin siyasar Jamhuriya ta biyu.

Ya zama jigon Jam'iyyar NPN da ta kafa Gwamnatin farar hula ta farko a Jihar Neja da kuma samun nasararta a zaɓen 1979 da kuma zaɓen 1983 a matakin Tarayyar Nijeriya.

A matsayin godiya da tukuici akan irin kyawawan ayyukansa, Masarautar Kwantagora a ƙarƙashin jagorancin Marigayi Mai Martaba Sarkin Sudan na Kwantagora, Alhaji Sa'idu Namaska Allah ya jaddada masa rahama ta naɗa shi GARKUWAN KWANTAGORA a ranar Asabar 22 ga watan Maris na shekarar 1980 inda aka gudanar da ƙasaitaccen bikin da ya tara jinsin al'umma a garin Kwantagora. ALLAHU AKBAR! WANI AIKI SAI TARA GARI ƊAN MAMMAN.

Allah SWT ya karɓi rayuwar Alhaji Sa'idu Baƙo Muhammad Garkuwan Kwantagora a ranar 21/8/1989.Ya bar iyali (matan aure da 'ya'ya).

Daga cikin ya'yansa akwai Alhaji Ibrahim Baƙo dake zaune a Kaduna da Alhaji Aminu Baƙo dake Abuja da Alhaji Falalu Baƙo wanda a halin yanzu Kwamishina ne a Gwamnatin Jihar Neja da kuma Hajiya Hauwa'u Baƙo, Dakrata - Janar a Gwamnatin Jihar Neja.

Allah ya jaddada masa rahama shi da sauran magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji,
Jihar Zamfara, Nijeriya.
Litinin 26/05/2025.

Post a Comment

0 Comments