𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa Barkatuhu, Malam ranar mun ga kayi bayani akan zuwan mata Jami'a da yin savis na NYSC muna son a taimake mu da numbern Hadisan da kuma Karin bayani da janyo Hankalin iyaye da Yan Mata akan wannan mun gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis salaam wa rahmatullahi wa Barkatuhu;
Dole ne a yi bayanin da suke kiyayewa mace Martaban ta, kuma Suke Tsare
mata Mutuncin ta sabida haka bai halatta Mace Budurwa ko Matar Aure ce ta ɗauki kafar ta zuwa wani a gari da sunan karatu alhalin
babu kowa nata a gurin wadda yake Muharramin ta ne shi ba wannan ya Saɓawa koyarwan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam.
Har wa yau yana daga cikin matakan da suke
taimakawa ga tsare Farji, hana mace ta yi tafiya in ba da muharramin ta wanda
zai tsareta ya kare ta daga kwadaice kwadaicen lalatattu da fasikai, rashin yin
haka ne shi ya sa a yanzu wallahi mata dayawa sun fada cikin halaka na
Zinace-Zinace da harkan Madigo ba tare da sanin Mijin ta ba ko iyayen ta ba
kawai an sake Baki cewa ai ita mutumiyar Kirki ce.
Toh Haramun ne mace ta yi tafiya ba tare da
muharramin ta ba kamar yadda muka yi bayani ranar, Ingantattun Hadisai sun zo
waɗanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da muharrami ba.
Daga cikin su akwai Hadisin da Abdullahi Ibn Umar yardar Allah ta tabbata a
gare shi ya ruwaito ya ce: Manzon Allah tsira da amicin Allah su tabbata a gare
shi ya ce: " kada mace ta yi tafiyar kwana uku sai da muharrami tare da
ita". Bukhari da Muslim suka
ruwaito shi. Kuma daga Abu Sa'id Al-Khudry Yardar Allah ta tabbata a gare shi ya
ce: Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana mace ta yi tafiyar kwana biyu, ko dare biyu sai da Mijin
ta ko muharramin ta ." Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Daga Abu Hurairah yardar Allah ta tabbata agare
shi ya ce, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Bai
hallata ba ga mace ta yi tafiyar kwana ɗaya da wuni ɗaya sai tare da muharrami a gare ta". Bukhari da
Muslim he suka ruwaito shi. Kaddarawar da aka yi da kwana uku, kwana biyu, da
kuma kwana ɗaya da wuni ɗaya, abin da ake nufi da shi shi ne tsawon tafiyar
gwargwadon irin abin hawan da ake da shi a wancan zamanin, na tafiya a kafa, ko
kan taguwa.
Malamai suka ce saɓanin gwargwadon kwanakin da ya zo a cikin Hadisan kwana
uku, ko biyu, ko ɗaya ko ma abin
da bai kai haka ba, ba ana nufin zahirin sa bane, abin da ake nufi dukkan abin
da ake kira bulaguro toh mace an hanata ta yi shi (sai dai idan cika wannan
sharadin) tukuna. Imam Al-Nawawiy ya ce a cikin sharhin sahih Muslim (9/103).
Ah shin a wannan zamanin wata nawa mace zata je karatun Jami'a ko zuwa Service
babu kowa nata a gurin? Sa'annan ku Sani cewa fa har da Malaman da ta ke koyar
da Addinin Musulunci ita Kanta Shari'ar Musulunci ya hana ta zuwa wani gari yin
Wa'azi, toh ina ga ke kuma?
Dukkan abin da ake kiran sa tafiya, toh an hana
mace ta yi ba tare da Mijin ta, ko muharramin ta har ta yi kwana uku, ko ta yi
kwana biyu, ko kwana daya, ko ta baridi daya (watau mil goma sha biyu ), ko
wanin haka. Dalili kuwa shi ne riwayar Ibnu Abbas wadda ba ta kayyade ba, kuma
ita ce karshen riwayoyin da Muslim ya kawo, wadda ta ce: "kada mace ta yi
tafiya sai tare da muharramin ta". wannan ya haɗa dukkan abin da ake kiran sa tafiya ne. Allah ne Mafi
sani.
Malaman da su ka yi fatawa da halarcin tafiyar
mace zuwa aikin hajjin Farillah cikin kungiyar mata, wannan sabanin Sunnah ne.
A duba cikin Al-Imam Al-Khaddabi ya ce a cikin Ma'alimus-Sunan (2/276-277):
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana mace ta yi tafiya
sai da muharrami a gare ta.
Don haka ba a halattawa Mace yin tafiya domin
aikin hajji ba sai tare da cika sharadin da Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya tabbatar da shi ba
sabawa Sunnah bane. Saboda haka idan dai fitar ba tare da muharrami bane
toh sabo ne, bai halatta a lazimta mata yin hajji ba, domin a lokacin ya zamo
yin aikin biyayya ga Allah amma da abin da zai kai ga saba masa. Karin bayani
kuma shi ne cewa su malaman ba su halattawa mace tafiya ba tare da muharrami ba
a kowane irin hali; sun halatta mata ne kawai a cikin tafiya domin yin aikin
hajji na Farillah kadai.
Imamun Nawawi ya ce cikin majmu '(8/249): Bai
halatta Mace ta yi tafiya domin aikin hajjin tadawwa'i, ko tafiya domin
kasuwanci, ko ziyara, ko makamancin su sai da muharramin ta. Don haka waɗanda suke yin sassauci a wannan zamani wajen halattawa
mace ta yi kowace irin tafiya ba tare da muharrami ba babu Wanda yayi muwafaka
da su a cikin malaman da ake dogaro da maganar su a cikin Addini. Abin da kuma
suke fada wai cewa: Ai muharramin nata shi ne zai dora ta a kan jirgin sama,
sannan kuma wani muharramin ya tareta idan ta isa garin da za ta je, domin
jirgin saman amintacce ne a riyawar su kenan, saboda yawan waɗanda suka hau shi waɗanda suka haɗa da mata da
maza; toh mu dai sai mu ce musu, Sam-sam ba haka bane.
Hadarin da ake cikin jirgin sama yafi na wanin sa,
domin matafiya a cikin sa suna cakuduwa da juna, wata kila ma ta zauna kusa da
namiji, ko kuma wani abu ya faru da zai sa jirgin ya je ya sauka a wata tasha
ta daban, in da babu wanda zai tarbe ta, ta kasance ta shiga hali mai hadari.
Toh idan kuwa irin haka ya faru, mene ne zai kasance halin mace da ta sauka a
kasar wadda ba ta san kowa ba, kuma babu wani Muharrami na ta a kasar?
Yarinya Budurwa sai ya kama hanya ita kadai wai
tafi yin karatu a Jami'a, ai ta tafi wani state yin Camping, bayan an gama wata
ana iya dawo da ita garin su wata kuma a sake tura ta can state din da babu
kowa nata a gurin, me muke daukar rayuwar ne Yan Uwa Musulmai? Manya da fa za
ka ga Mahaifiyar ka idan za su je yin Barka ko gaisuwa toh da dare suke tafiya,
nan ma idan za su tafi sai Mahaifin ka ya ce wane tashi Kara su, wani gari
Mahaifiyar ka zata je Mahaifin ka ne zai je da ita sai ya bar ta a gurin idan
ta gama iya kwanakin da zata yi sai ya je ya dauko ta, ga shi babau aya ba
Hadisi a gurin waɗanda suke yin
hakan amma sun zauna lafiya da iyalan su.
Amma sai ga shi mu da muke cewa Kai ya waye, amma
Hankalin ya Bata Matar ka ce ta tafi aikin Service babu kowa nata a gurin wani
ko a jikin sa, Yar ka ne ta tafi aikin Service ko Karatun Jami'a a wani garin
amma wani Uban ko Mahaifiyar ko Yan Uwan ta babu wadda ya taba taka kafar sa da
sunan bari ya je ya ga Yar uwar sa ko Yar sa yaya take rayuwar ta a Jami'a?
Wani babu kowa nashi a State din zai tura Yar sa wai yana son ta zama Likita ko
Law, ga abun da Addinin Musulunci ya ce daga Bakin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Sallam da Ayar Al Qur'ani guda, amma sai kowa ya ce a'a ai Yar sa ko
Matar sa tana da kulawar da babu wadda ya isa ya lalata rayuwar ta ko yayi Zina
da ita, shin ka fi sanin Manzon Allah sanin haka ne? Ka fi Ubangijin ka Sanin
hakane da ya ce dole ne ta je da muharramin ta ko Mijin ta? Wajibi ne ku ji
tsoron Allah domin babu wadda zai tafi da Boko ko abun da ya mallaka anan
duniya komai anan za'a bar shi, abun da za ki tafi da shi shi ne Likafanin ki
Shima iya cikin qabarin ki zai yi, abun da za ki tafi da shi Lahirar ki shi ne
wannan rayuwar da kika dauko me kyau ne ko marar kyau kowa zai je gaban Allah
yayi bayani Allah ya shiryar da mu ya tsare mu da sabawa Allah da Manzon Allah
domin Neman duniya.
Madogaran rubutu, Littafin Fadakarwa a kan hukunce
hukuncen da suka kebanci mata muminai wallafar: Dr. Saleh bin Fauzan Al-Fauzan_
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.