Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ke Leken Tsaraicin Mutane

Hukuncin Wanda Ke Leƙen Tsaraicin Mutane

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaykum malam tambaya ta shi ne mene ne hukuncin wanda yake leqa mutane (musamman ma 'yan mata)  yayin da suka shiga bayan gida domin wanka ko kama ruwa? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Babu shakka wannan haramun ne. Kuma duk wanda ya aikata haka tabbas ya cika azzalumi kuma fasiqi ta hanyoyi kamar haka :

1. Yin haka, leken tsaraicin jama'a, Qetare iyakokin Allah ne kuma Allah ya ce : "Wanda ya saɓa wa Allah da ManzonSa kuma ya Qetare iyakokinsa, Zamu shigar dashi cikin wata wuta wacce zai dawwama acikinta, kuma azaba mai wulakantarwa ta tabbata gareshi". Awani wajen kuma Allah ya ce "Wanda ya qetare iyakokin Allah, hakika ya zalunci kansa".

2. Yin haka yana daga keta alfarmar musulmi da kuma mutuncinsa. Gashi kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce : "Dukkan musulmi akan musulmi, haramun jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa.

3. Wannan laifin ya shafi kallon al'aura da tsiraicin mutane. Kuma Imamuz Zahaby acikin kitabul Kaba'ir ya kawo hadisin dake nuna Allah ya tsine wa mai kallo da wanda ake kallon (Wato Allah ya tsine wa mai kallon tsaraici, da kuma wanda ke bayyanar da tsaraicinsa domin arika kallo). To kaga anan su waɗanda ake kallo ɗin, ba da son ransu ake kallon nasu ba. Hasali ma basu bayyanar da tsaraicin ba. Don haka tsinuwar ta tattaru ne akan wannan dake kallon nasu aɓoye.

4. Leqen tsaraicin Muminai cutarwa ce garesu kuma Allah ya ce : "wadannan dake cutar da muminai maza da muminai mata sannan basu tuba ba, to azabar jahannama ta tabbata garesu, kuma azabar quna ta tabbata garesu".

Amma idan ya zamanto akwai makobtaka atsakaninsu, to anan ne laifin kuma yafi girma domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce : "Duk wanda Makobcinsa bai tsira daga sharrinsa ba, bazai samu shiga Aljannah ba" (imamu muslim ne ya ruwaitoshi).

Sannan daga karshe idan an kama irin Waɗannan mutane wajibi ne akaisu ga hukuma mafi kusa domin ɗaukar matakin da ya dace akansu.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments