𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Na ga Sunana a Group ɗin NYSC Amma Mahaifiyata ta ce ba zan je wani gariba ba tare da Muharramiba har senayi aure tukun Mlm Ina son aban shawara ina tsoran Allah, inatsoran shahadar karya da Saɓawa Mahaifiyata, Inasan Mallam yaman bayani da shawara inajiran ansa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Waalaikis Salaam:- Ina Miki Nasiha da Ki Ji Tsoron
Allahu Subhanallah Wata'ala, da Yiwa Mahaifiyar Ki Biyayya, Saboda Shi Biyayya
ga Mahaifiya Wajibi Ne Kamar Yadda Allah Subhanallah Wata'ala Ya Faɗi Haka ( Kuma Ubangijin Ku Ya Hukunta Kada Ku Bauta ma
Kowa Face Shi, Kuma Game da Mahaifa Biyu Ku Kyautata Musu, Kyautatawa Ko da Ɗayan Su Ya kai ga Tsufa
a Wurin Ka Ko Dukkan Su Biyu Kada Ka Ce Musu Tir Kuma Kada Ka Tsawace Su Kuma
Ka Faɗa Musu Magana Mai Karanci).
A Bisa ga Wannan Ayar, Ya Wajaba Gare Ki Kiyiwa
Mahaifiyar Ki Biyayya. Ya Tabbata a Cikin ( Sahihul Bukhari Da Muslim da
Abu-Hurairah Allah Ya Kara Mishi Yarda) Ya ce Annabi Muhammad Mai Tsira Da
Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Ya ce Wanene Yafi Cancanta in yi masa
Kyakkyawan Mu'amala da Biyayya Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasalam Ya
ce Mahaifiyar Ka! Ya ce Sai Wa? Ya ce
Mahaifiyar Ka, Sau 3 Uku Yana Cewa Mahaifiyar ka Sannan Ya ce Mahaifin Ka.
Sa'annan Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin
Allah Su Tabbata Agare shi, Ya Hana Mace Ta yi Tafiya ba Tare da Muharramin ta ba, Musamman a
Wuraren da Ake NYSC, ko Kuma Zuwa Karatun Jami'a kai ko malamar Addinin
Musulunci ce an gayya ce ta yin Wa'azi bai halatta gare ta, balle Yan Boko a
inda Babu wani Ɗan Uwan ki Na Jini a gurin da za ki je Karatun, Wadda zai kasance Tana
Kwana a Gidan Sa bawai a Hostel ba, Kuma Mafi Yawanci Fasadin da Ake Aikatawa a
Cikin Jami'a ko NYSC yana da Yawa, Daga Jami'a Har zuwa NYSC.
Musamman ga Daliban Matan Jami'a, ko da a Gidan Su
Salihar Mace ce ita, toh wallahi idan ta je Jami'a na Wasu Kwanaki Sai Rayuwar
ta ya Chanja daga inda aka San ta, Yan Mata Daya-daya ne Suke Tsare Kansu da
Farjin Su a Jami'a, Amma Wallahi Kaso 80% cikin 100% 20 ne kaɗai suke tsare Kansu, sai Wadda Allah ya tsare duk Sun
Lalata Rayuwar su a Jami'ar, Wadda ba'a Tsammani ta Lalace Amma idan an Bincika
sai a ga ai ba tayar Baya ba ce ita.
Yau ko da ace Jami'ar a Cikin Garin ku yake,
Iyayen ta za su Rika kula da ita, Wallahi Yan Mata dayawa Sun Lalata Rayuwar su
a Garin nasu, Ballatana Ace ai Ɗiyar ka ta tafi wani Jihar yin Karatun Jami'a babu wani Dangin ka a gurin,
ai Sai yadda Allah yayi da ita. An San Cewa Wasu ko da a gaban Iyayen su ne
Suna Lalacewa hakane, Amma Rayuwar Jami'ar Yanzu yafi Karfin Tunanin mu, duk
Macen da zata je Jami'a ita kaɗai tana Kwana a
Hostel da wasu matan a rika yin wanka a Toilet ɗaya kowa na ganin Tsiraicin Yar uwar ta, ba ta da Wadda
zai Rika Yi mata tsawa da Razanata ba ta ganin wani Dangin ta a kusa da ita zai
Rika kafa Mata doka kar kiyi kaza kiyi kaza shi ne daidai.
Toh Wallahi Yan Mata Daya-daya ne waɗanda ba'a lalata da su, ko Kuma da suke Shiga Harkan
Iskaci Na Madigo Ko Luwaɗi, Wata ba zata
Yi Karatu ba, Domin tana da jikin ta maza Suna Neman ta, Idan Lecturer nata Ya
neme ta Zata bada Kanta Yayi Zina da ita, Domin ya ba ta Marking ta ci Exams
nata. Wata Kuma ga Dalibai Yan Uwan ta ne, zata Sake musu jikin ta su yi Zina
da ita, Domin tana Ganin Qawayen ta Suna Yi da Samarin su, Kuma sun gaya mata
Cewa idan ba ta yin wannan Harkan zina ai Bata Waye ba ko kuma ba zata samu Kuɗin Kashewa ko na Siyan Handout ba.
Iyaye Mata da maza Ina ne zaku Kai Karatun Ɗiyar naku? Akwai Yan
Matan da ba su aikata hakan a Jami'a ko wanin sa amma gaskiya ba su da Yawa,
toh ka Tura Ɗiyar ka ta je
Jami'a ko NYSC an je ana ta Zina da ita, ta je tana ta Yin Madigo, Kai ba ka
San Komai ba, Kai Damuwar ka kawai a nemo maka Duniya ta kowacce kawai results
na Degree kake so ko Master's ta kawo ma, haba Jama'a iyaye Mata da maza? Don
Allah Wacce irin Rayuwar ce wannan?
Shugaban Maluman Da'awa Na Africa wata Rana Wani
Malamin mu ya Kai Masa Ziyara Gidan sa a Kano, sai ya Tarar da Yaran sa Sun
dawo daga Karatun Jami'a nasu, Sai 1 yaron ya zo ya Nunawa Wannan Shugaban
Maluman Da'awa Na Africa Wato Baban Shi Results nashi, ya Samu First Class
Offer, Ɗayan Kuma ya Samu Second
Class Lower, Wannan Malamin Wallahi da ya Ga Results ɗin Su Sai Malamin Nan ya Haɗa Fuska ko nuna Farin Cikin Sa Bai Yi ba.
Malamin mu yana ta mamakin sa, Suna zaune Sai ga Ɗayan Yaron Sa ya Dawo
Shima ya Samu Second Class Lower Sannan ga Certificate Nashi Na MSSN, Wannan
Malamin da ya ga Certificate na MSSN da results na wannan yaron Sai ya Dafa
Kafadar Yaron Sa, ya ce Allah ya Sanyawa Karatun ka Albarka Malamin Nan ya nuna
Farin Cikin Sa da Jin daɗin sa Fiye da Waɗanda Suka kawo Masa Results na Jami'a kuma Sun ci.
Shugaban Maluman Da'awa Na Africa Sai yake gayawa
Malamin Mu Cewa, Shi wallahi Yana Bakin Ciki ace Wai Ɗan Musulmi Jikan musulmi zai Shiga School Amma har
ya bar Wannan Makarantar ba tare da ya Shiga Kungiyar Musulunci ba, har ya dawo
gida, Ya ce Wannan abun Takaici ne abun bakin Ciki ne babba, ya ce shi bawai
Bai ji daɗin Results ɗin Sauran bane, Amma na Wannan Yaron da ya Shiga Kungiyar
Musulunci shi ne yafi Burge Sa yafi Jin daɗin Sakamakon sa, Kuma Wallahi Wannan Malamin Yana gaya
Mana Cewa waɗancan da Results nasu
yayi kyau, ba su Zo Suka Rike Uban Su Kamar yadda Wannan Wadda ya samu
Certificate na MSSN ɗin ba.
Shugaban Maluman Da'awa Na Africa ya ce komai
Wannan Yaron ya dawo ya ce Baba Ka Huta Kawai, Duk Sati duk Shekara Sai Ya je
Umura Da Aikin Hajji, Waɗancan kuma ko a
Jikin Su. Ina Karatun su ya je? Wasu ma Su je inda MSSN ɗin yake Suna ganin ai Kauyanci ne wannan, wani Uban ko
Uwar Har Yaransu Su Gama Karatun Jami'a su dawo wallahi su tambaye su komai
Amma ba zai su Tambaye su Cewa Shin Wani MSSN kike Ciki a Jami'a? Inna illahi
Wa'inna illahin Rajee'um Haba Yan Uwa Musulmai.
Toh Wallahi Iyaye Maza da Mata Ku Ji tsoron Allah,
kowacce Uwa ko Uba Wallahi Sai Allah ya Tayar da ku ya Tambaye Ku Ko kuna So ko
ba ku So Sai Allah ya muku Tambaya ku Fara tanada Amsar da za ku bayar.
Idan Ɗiyar ka, ba za ka iya Aurar da ita ta tafi Jami'a Tana gidan Mijin ta ba,
Ko kuma a Garin da zata je Babu wani Ɗan Uwan ka ko Wani Muharramin ta, Wadda suka San ta a Gurin zata Rika kwana
a gidansu Su Rika kafa Mata doka Suna Mata Barazana da matsa Mata ba, toh Zaman
ta a gida ku yi mata Addu'ar Allah ya sanyawa Karatun da ta yi na Secondary
School Albarka.
Sa'annan ku yi Mata Addu'ar Allah ya kawo Mata
Miji Nagari ta yi Aure ta bar gidan ku, Wallahi yin Haka Shi ne Zama mafi
Alkhairi ga Rayuwar ku daga duniya Har zuwa Lahirar ku, Iyaye Mata da maza
Rashin Yin Haka Wallahi Shi ne Zai sa daga Nan Duniya Rayuwa ta yi muku tsada, Ɗiyar ku ba Karatun ko
kuma ga Karatun Amma ta Lalace, ko ga Karatun duniyar ta samu amma Mijin Aure
ya gagare ta, Ku je Lahirarku ku tarar da Azabar Allah Mai Tsanani.
Hadisi Ya Tabbata a Cikin ( Sahihul Bukhari da
Muslim Daga Ibnu Abbas Allah Ya Kara Mishi Yarda) Annabi Muhammad Mai Tsira Da
Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, ya ce Kada Ɗaya Daga Cikin Ku Ya Keɓanta da Wata Mace Sai dai Tare da Muharramin ta, Kuma
Kada Ta yi Tafiya ba Tare da Muharramin ta ba. A Wani Riwayar Kuma a Cikin (
Sahihul Bukhari Da Muslim Daga Abdullahi Bn Umar da Abu Sa'idil Khudri) Annabi
Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Ya ce Kada Wata Mace ta
yi Tafiyar Ƙwana (3) Uku ba Tare da Muharramin ta ba. A Wani
Riwayar har Yanzu a Cikin ( Sahihul Bukhari da Muslim Ya ce kada Mace ta yi
Tafiyar Yini Ɗaya da Dare Ɗaya ba Tare da
Muharramin ta ba.
Shin Jami'a Ko NYSC Wuni ake Yi a gurin ko Shekara
ne? Amma Haka Budurwa zata Kama hanya ta tafi ba kowa nata a gurin Tana Kwana a
Hostel ko a waje, ba Uban ta ko wani nata a kusa Wadda zai Rika Zuwa duk Sati,
Shin me kuke tunanin zai faru iyaye? Duniya fah ba ta da Tabbas Wallahi Lahirar
ku Shi ne Tabbas kun Samu Duniyar, amma Kun bar Lahirar me kuka Yi Kenan iyaye?
Saboda Haka Abin da Yafi Cancanta shi ne Ki Yiwa
Mahaifiyar Ki Biyayya, Bayan Kin yi Aure Sai Ki Tafi da Muharramin Ki Wato
Mijin ki, Yin Hakan shi ne yafi Alkhairi Gare Ki, Rashin yin Haka a tafi Babu
Muharramin ki wallahi Shi ne Idan kin je Jami'a ko NYSC Babu wadda zai Miki
magana ki ji, babu Wadda za ki ji tsoron sa don ganin idon sa, toh shi ne zai
Sa ki haɗu da Qawayen Banza da Friends ɗin banza, Duk Kamewar ki Sai Kin Chanja Rayuwar Ki,
Kuma ki zo kina yin abun da ya Saɓawa Allah na Aikita Zina Ko Madigo ko kuma kina harka da
Maza ke a naki tunanin ai friends naki ne Allah ya Shirya, Amma idan Mace zata
tafi da Muharramin ta ko akwai wani Dangin ta yana nan a gurin, toh In sha
Allahu Za'a Ɗan samu Sauki
Duniya da Lahiran Ki. Allah ya Shiryar da mu da Son Zuciya. Dafatan Kin Gane
Koh???
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.