Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sana'ar Ture-Turen Odiyo Ko Bidiyo

HUKUNCIN SANA'AR TURE-TUREN AUDIO KO VIDEO

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Na'am malam dan Allah ina tambaya : Shin ya hukuncin kasuwanci da laptop kamar ta hanyar ture-ture irin su wa'azi karatuttuka da finafinai da sauran su ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah.

Wannan Sana'ar da kake tambaya akanta, tana daga cikin sana'o'in da matasa ke yinsu sosai awannan zamanin musamman ma ayankinmu na arewacin Najeriya.

Kamar dai kowacce hulda wacce Ɗan Adam zai gudanar arayuwarsa, itama wannan sana'ar tana da hukunce-hukuncen da suka kebanceta. Ga misali :

Duk abinda kallonsa ko sauraronsa haramun ne ga Musulmi, misali kamar fina-finai batsa, kade-kade, wake-waken disko da sauransu, to haramun ne Musulmi ya rika turawa mutane haramtattun abubuwa amatsayin sana'a ko hanyar neman kuɗi.

Amma halastattun abubuwa kamar wa'azi da nasihohi da tarihohi da darussa na ilimai masu amfani, babu laifi ga musulmi cikin kallo ko sauraronsu, to ya halatta musulmi ya turo ma wani ko wasu, kuma ya halatta ya karɓi wani abu na kuɗi amatsayin ladan turawar da yayi. Saboda ayar nan ta Suratul Ma'idah inda Allah yake cewa :

...وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ

"KUYI TAIMAKEKENIYA DA JUNA WAJEN BIN ALLAH DA KIYAYE DOKOKINSA, KADA KUYI TAIMAKEKENIYA BISA SAƁON ALLAH DA KETARE DOKOKI" (Suratul Ma'idah Aya ta 2).

Don haka duk wata sana'ar da acikinta akwai taimakawa ga masu Saɓon Allah da ketare dokokinsa, misali kamar sayar da miyagun kwayoyi, ko bayar da rance da kuɗin ruwa, ko tuka motar giya, ko aiki a kampanin giya, ko yin aikin gadi ko tsaro (security) a gidajen karuwai ko gidan rawa da sauransu bai halatta ba, saboda yin hakan tamkar taimaka wa ayyukan saɓo ne.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments