SAMARI SUNA YAWAN SON TAƁA JIKINA:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam. Shawara nake nema game da wani abin dake yawan faruwa ga wata kawata. Wato tana da farin jinin samari amma mafi yawan dalilin dake rabata da saurayi abu guda ne. Shi ne yawancinsu suna son ta'ba jikinta ne. Ita kuma da zarar taga saurayi ya nuna mata ga bukatarsa sai ta sallameshi ta koreshi. Shi ne muke neman shawara. Don Allah malam wacce addu'ar zata rikayi domin neman kariya daga sharrin irin wadannan samarin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.
Da farko dai babbar shawarar da zan baku ke da
kawar taki ita ce ki isar mata da sakona
kamar haka :
Baiwar Allah kiji tsoron Allah ki kiyaye dokokinsa
afili da boye. Duk yadda akayi ba za'a rasa wani dalikin dake janyo miki
shaidanun samari ba. Kodai kina yawan sanya sutura masu bayyanar da tsaraici ko
masu bayyanar da siffar jikinki, ko kuma kina yin wasu abubuwan da zasu motsa
sha'awar namiji alokacin da kuka zauna hira dasu.
Misali kamar yin zantukan batsa ko fesa turare, ko
kuma zama awani kebantaccen waje inda babu mutane sosai, alhali duk wadannan
haramtattun abubuwa ne bisa karantarwar addinin Islama.
Zantukan batsa haramcinsu ba boyayyen abu bane.
Hakanan kebancewa da wani namijin da ba mijinki ko muharraminki ba. Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "BABU WANI NAMIJIN DA ZAI KEBANCE
DA WATA MACE WACCE BA MUHARRAMARSA BA, FACHE SAI SHAIDAN YA KASANCE SHI NE NA
UKUNSU". Zai zo yana sanya muku sha'awar junanku yana siffanta muku
tsaraicin junanku har sai ya afkar daku cikin fasikanci.
Shi kuwa turare yana daga cikin abubuwan dake
saurin motsa zukatan mutane zuwa ga sha'awar jima'i (musamman ma maza) don haka
haramun ne ki fesa turare domon wani wanda ba mijinki ba.
To yawancin abin dake faruwa kenan ga matasa
awannan zamanin.mummunan dressing, Kebancewa daga ke sai saurayi, fesa turare,
zantukan batsa, daga nan sai shafa jikkunan juna, sai kuma zina (Allah shi
kiyayemu baki daya).
Don haka mutukar ba zaki bi dokar addini ba acikin
al'amuranki, kina sanya gyale, kina yin shiga mai bayyanar da tsaraici, kina
fesa turaruka masu motsa sha'awa, to
dole duk wani shaidanin saurayi da zarar ya ganki sai yaji tamkar kiransa
kikeyi. Don gaka da zarar yazo zance wurinki ba zai ta'ba boye miki manufarsa
ba.
Amma idan da zaki kiyaye dokokin Allah wajen
yanayin suturarki da lokutan fitarki waje, da irin mutanen da zaki rika kulawa
awaje, da kuma yanayin shigar da zakiyi idan saurayi yazo wajenki, In shaAllahu babu shaidanin saurayin da zai
ji sha'awarki ballantana yazo wajenki ko yai kokarin ta'ba miki jiki. Babu
wanda zaizo wajenki sai mutanen kirki masu mutunci wadanda keda kyawawan
manufofi in sha Allahu.
Hadisi ya tabbata wanda manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam Ya ce: Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe akan ɗayanku shi yafi masa alkhairi akan ya shafi jikin macen
da bata hallata agareshi ba. Albany ya ce hadisine ingantacce acikin sahihul
jami’ul kabeer (5045).
Lallai duk macen da ta bada kanta wa wani ɗan iska mayaudari wanda baya sonta baya son rayuwarta da
tarihinta da sunan wai yana sonki ko kuma kunyi alkawarin aure wallahi duk
yaudara ce kuma wallahi koda ya aure ki sai yaci mutuncinki ya sake ki, duk
wanda zaki masa haka kina tunanin zai aminta cewa idan wani yazo gunki ba zaki
bashi irin damar da kika bashi ba? Kiyi tunani da kyau yake ‘yar uwa!
Wannan hadisan kaɗai ya isa ya zama tsawa da firgitarwa ga samari da kuma
‘yan matan da ake yaudara da sunan ana sonku, ya isa kuji tsoron Allah ku tuba
tun kafin lokaci ya kure muku, ku lazumci yiwa Allah biyayya cikin abunda ya
haramta na dokokinsa, na daga abunda taɓa jikin mace
yake haifarwa wanda yake kaiwa zuwa ga fitintunu da alfasha kala-kala.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.