Ticker

6/recent/ticker-posts

Barkwanci a Kasar Hausa: Bitar Asalinsa Da Gurbinsa a Zamantakewar Hausawa

Citation: Gambo, H. & Mohammed, S. (2025). Barkwanci a Ƙasar Hausa: Bitar Asalinsa Da Gurbinsa a Zamantakewar Hausawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(2), 46-51. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.007.

BARKWANCI A ƘASAR HAUSA: BITAR ASALINSA DA GURBINSA A ZAMANTAKEWAR HAUSAWA

Hamza Gambo
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero Kano
Email: hgambo31@gmail.com
GSM: 08167309171

Da

Shu’aibu Mohammed
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero Kano

Da

Muhammad Isa Usman
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero Kano

Tsakure

Wannan nazari an aiwatar da shi ne a kan barkwanci a tsakanin al’ummar Hausawa. Nazarin an aiwatar da shi ne ta hanyar samo bayanai daga litattafai da kundaye da kuma kafafen sada zumunta kamar facebook da tiktok. An gudanar da wannan takarda ta bin bayanan da masani Gusau, (2003) ya kawo na aiwatar da waƙar baka da sauran matanin adabi, an kuma yi amfani da matakan da ra’in ya samar na nazarin waƙar baka da sauran dabarun jawo hankali. Manufar wannan takarda shi ne gano barkwancin da Hausawa suke yi, ta hanyar kafa hujjoji daga bayanan da aka samo daga kundaye da kafafen sadarwa. Sannan an yi sharhin dukkannin abubuwan da nazarin ya gano. A ƙarshe dai binciken ya gano barkwanci, ta hanyar fayyace yadda ake aiwata da shi daki-daki da misalai.

Fitilun Kalmomi: Barkwanci, Zamantakewa, Asalin Barkwanci

1.0 Gabatarwa

Takardar tana ɗauke da bayanai ne a kan barkwanci. Barkwanci na ɗaya daga cikin nau’o’in adon harshen na maganganun azanci. A takardar an yi, ƙoƙari wajen ganin an duba ayyukan magabata kamar: Ɗangambo (2008) da Yahaya (1992) da Gusau (2013) da Gumel (1992) da sauransu. Haka kuma, an yi tsokci kan ra’in da aka yi amfani da bayanan ciki wajen gudanar da binciken. An kawo ma’aanar barkwanci a mahangar masana, sannan an kawo masu yin barkwanci da dalilin da suke sa a yi barkwanci. Haka kuma dukkanin misalai da aka kawo a kowanne ɓangare, an kafa hujja ne daga ɗaya daga cikin barkwancin da aka nazarta, domin a tabbatar da barkwanci a ilimance. A ƙarshe an fito da saƙonnin cikin talluka da zantukan da suke a wasu kafafen sada zumunta.

1.1 Ra’in Bincike

An ɗora wannan bincike ne bisa ra’in tsarin waƙar baka Bahaushiya Wanda ya ƙirƙiro wannan ra’i shi ne Farfesa Gusau shekarar 2003 A ƙasar Nijeriya, shi wannan ra’i yana yana ƙarfafa yadda za a yi nazarin waƙar baka da hanyoyin da ake bi wajen nazartar waƙar baka da kuma adon harshe. An sami manazarta adabi waɗanda suka gabatar da ayyuka a kan wannan ra’i. Wannan dalilin ne yasa aka ɗora wannan aiki na amfanin habaici a kafafen sadarwa.

1.2 Hanyoyin Tattaro Bayanai da Sarrafa su.

A ƙoƙari gudanar da wannan bincike an yi ƙoƙarin samo bayanan da aka nazarta daga Ɗangambo (1984) da Umar (1986) da Tukur (1991) da Ingawa (1990) da CNHN (2006) da Bunza (2006) da gidajen radiyo da kuma facebook da tiktok. Haka kuma an sake samo bayanai daga littafin Ibrahim Yaro Yahaya wanda suka yi tare da wasu. An sake samo wasu bayanan daga gidajen rediyo da kumafacebook da tit-tok a inda aka samo waɗannan bayanai.

2.0 Ma’anar Barkwanci a Mahangar Masana

Ƙamusun Hausa (2006: 39) ya bayar da ma’anar barkwanci da “Raha ko wasa na fatar baki don ban dariya”. Ɗangambo (1984: 36) yana ganin barkwanci “zantuka ne na raha da wasu mutane waɗanda Allah ya hore wa iya raha da magana da ban dariya suke yi wa mutane”.

Shi kuma Umar (1980) cewa ya yi barkwanci “wani muhimmin rukuni na zube a adabin baka na Hausa wanda ya danganci irin labarun nan da Bahaushe yakan ƙirƙira don kawai ya yi dariya ya more”. Tukur (1999: 11) ya bayyana barkwanci da cewa “zantukan raha ne da ban dariya da mafi yawan al’umma suka amintu da wanzuwarsu don adana tarihinsu da yauƙaƙa zumunci”.

A bisa ga bayanan da masana suka faɗa dangane da ma’anar barkwanci. Za mu iya cewabarkwanci wata magana ce da akan shirya mai ɗauke da zantukan hikima waɗanda suke sanyawa a yi raha da annashuwa a tsakanin mutane biyu,, ko a tsakanin wasu al’umma (abokan wasa) waɗanda a duk wurin da suka haɗu da juna, sai sun yi zolaya ko kuma sun tunzura juna ba tare da an yi saurin samun wani saɓani a tsakaninsu ba.

A taƙaice dai barkwanci wani salon magana ne da Allah kan huwace shi ga ɗaiɗaikun mutane ta inda za su kasance masu fasaha a duk zancensu Hakan ya sa da zarar sun yi magana sai an yi raha; akalla a yi murmushi. Barkwanci na iya zama tsararren zance na ban dariya, musamman wanda aka shirya shi don zolaya ko tsokana. A wani ɓangaren kuma barkwanci shi ne irin wasa da ke tsakanin ƙabilu ko al’umma, ta dalilin aukuwar wani lamari mai girma a tsakaninsu. Haka kuma wasan da ake samu a tsakanin taubasai (abokan wasa na dangi) ana kiran sa da barkwanci

2.1 Masu Yin Barkwanci

Dangane da masu yin barkwanci, yawanci duk rukunin al’umma na yin barkwanci, barkwanci ba na ya-ku-bayi ba ne kaɗai, hatta saraki da ma’aikatan gwamnati na yin sa. Haka ma makaɗa da mawaƙa da maroƙa ma suna yin barkwanci, samari da ‘yanmatatsofaffi da dattijai da yara ma duk suna barkwanci. Haka ma malamai da almajirai ma suna yi barkwanci don haka ba wani rukunin mutanen da ba sa barkwanci.

2.2 Dalilan da ke sa a yi Barkwanci

Wasan barkwanci a tsakanin al’ummar Hausawa wani daɗaɗɗen al’amari ne wanda yake da wuyar a ce ga lokacin da aka fara aiwatar da shi a cikin rayuwar Hausawa. Akwai dalilai da sukan sanya a yi wasan barkwanci tsakanin al’umar Hausawa ko da wasu. Dalilan sun kasu zuwa manyan gida uku kamar haka:

2.2.1 Zumunci

Zumunci wata kyakkyawar dangantaka ce ta jin ko ta aure ko ta abota tsakanin mutum da mutum (Ƙamusun Hausa, 2006: 496). Zumunci wani babban dalili ne da yake kawo wasan barkwanci tsakanin al’umar Hausawa. Bakura da Sani (2022: 31) sun nuna cewa, zumunci yana ɗaya daga cikin dalilan da suke haifar da barkwanci a tsakanin al’umma. Haka kuma, barkwanci wata hanya ce ta ƙarfafa danƙon zumunci a tsakanin mutane.

Zumunci a zamantakewar Hausawa ya kasu gida biyu; akwai zumunta ta ‘yan uwantaka wadda ta ƙunshi dangantaka ta jini. Irin wannan dangantaka ce ta haifar da wasan barkwanci tsakanin kaka da jika da taubasi da kuma wasan ƙannen miji da mata. Sai kuma, zumunci tsakanin masu sana’o’in gargajiya. Sana’o’in Hausawa na gargajiya sana’o’i ne da suke dogara da junansu a koda yaushe. Don haka, wannan ya bayar da damar yin wasa a tsakanin masu sana’o’i biyu ko fiye da ma dangantaka wato alaƙa ta jinni. Misali, Makiyayi da Mahaucida Malami da Maharbi da Maƙeri da Buzu da sauransu.

2.2.2 Zaman Tare

Zaman tare zana wuri ɗaya ne tsakanin wasu mutane wanda hakan kan janyo shaƙuwa da junaA sakamakon zama wuri ɗaya tsakanin wasu mutane waɗanda babu alaƙa irin ta jini ga shi kuma suna zaune a muhalli ɗaya. Misali, auratayya a sanadiyyar haka sai wasa irin na barkwanci ya shiga tsakaninsu.

Ga wani ɗan misali:

Wai an ce zaman tare ya haɗa wani Bufulatani da ɗan ƙabilar Tibi. Da Bufulatanin nan zai yi tafiya sai ya ba wa Tibi ɗin nan amanar kadararsa suka yi ban-kwana. Ai kafin Bufulatanin nan ya dawo Tibi ya hau kan dukiyar nan ya cinye, bai rage komai ba. Bafulatani na dawowa ya tambayi Tibi game da ajiyarsa, sai Tibi ya ce: “Mun ci!” Wannan dalilin ne ya sa har gobe za a ji Fulani na ƙiran Tibi da suna “Mun ci” (D/Iya, 2/10/2016)

2.2.3 Yaƙi

Akwai yaƙe-yaƙe da dama da suka shiga tsakanin daulolin Ƙasar Hausa da kuma maƙabtansu tun kafin jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo. Kowace masarauta ta Ƙasar Hausa ta kan far wa wata masarauta da faɗa (yaƙi) domin ta faɗaɗa ƙasarta ta kuma mallaki tattalin arziki mafi girma. Wannan dalilin yaƙin tsakanin wata masarauta da wata shi ne ya assasa wasan barkwanci da ake tsakanin Katsinawa da Gobirawa, Katsinawa da Haɗejawa, da kuma Guddirawa da Haɗejawa. (Bunza 2015)

Ga wani ɗan misali:

Haka ma a kusa-kusan nan an samu labarin barkwancin da ya faru a fadar Sarkin Katsina. An ruwaito cewa taron aure ne ya haɗa Sarkin Katsina da wani Kwamishina da ya zo daga jihar Nja, inda Sarki ya murtuke, ya kalli wannan Kwamishinan ya ce: “ Duk jami’in da ya zo daga jihar Neja kar a bar shi ya fita, a ɗaure shi.” Mutane suka fara kallon-kallo. Da Mai martaba ya lura, sai ya saki fuska ya ce: “Saboda su bayinmu ne” Nan fa raha ta dawo sabuwa a fada, musammam ga mutanen da suka san wannan tada ta barkwanci. (Ɗan maman Alajiƙan Shata)

 3.0 Rabe-Raben Barkwanci

Ana iya karkasa barkwanci bisa la’akari da masu yinsa. Za mu iya samun rabe-rabe kamar haka:

3.1 Barkwanci Tsakanin Rukunan Hausawa

Tarihi ya nuna cewa Ƙasahen Hausawa sun sha fama da ƙananan yaƙe-yaƙe da aka sha gwabzawa, sai dai abin da aka jima, amma ba sa lissafuwa,. An fafata tsakanin Gobirawa da Katsinawa, an yi ɗauki-ba-daɗi tsakanin Kanawa da Katsinawa, an yi artabu tsakanin Zamfarawa da Kanawa da kuma gumurzu tsakanin Katsinawa da Haɗejawa da kuma yaƙi tsakanin Kanawa da Zazzagawa. Daga ƙarshe dai yaƙe-yaƙen ƙasarmu su suka fahimtar da mu cewa; dole a share jini a koma wasa. A taƙaice dai masana na ganin yaƙe-yaƙen da al’ummomin Ƙasar Hausa suka yi da wasu ƙasashe da kuma tsakaninsu, su suka haifar da wasannin da ke gudana a yau. An gama yaƙi an riga an fahimci juna kowa ya san wurin da wani ya kwana, da wanda ya yi rinjaye da wanda aka rinjaya, don haka kowa ya miƙa wa zaman lafiya wuya. Umar 1986)

 Wasu wasannin sun faru ne sakamakon yaƙin da aka gwabza, wasu kuma sakamakon auratayya da ta shiga tsakani, wasu kuma zamantakewa ta yau da kullum. Daga cikin wasannin barkwancin da ke gudana tsakanin rukunan na Husawa sun haɗa da:

3.2 Katsinawa da Gobirawa

Wasan barkwanci tsakanin Katsinawa da Gobirawa ya ƙullu ne bayan da aka kwashi ‘yan kallo musamman lokacin da Katsinawa suka rinjayi Gobirawa a wata fafatawa da aka yi har Sarkin Gobir Ibrahim Babari (1737-1764) ya ce: “A mazaya a mai da iri gida” lokacin da ya ga Katsinawa na ƙoƙarin ƙarar da mayaƙansa. Tun a wannan lokacin kowa ya miƙa wa zaman lafiya wuya sai ‘yan abn da ba a rasa ba. A kan wannan ne wasan barkwanci ya ƙullu tsakanin Gobirawa da Katsinawa, Duk in da Katsinawa suka haɗu da Gobirawa sai sun musu irin wannan wasan barkwancin suna ce musu “A mazaya a mai da iri gida”, ko su ce “Gobirawa sun ƙare har jariransu”. Su ma Gobirawa suna da wasu lafuzzan barkwanci da suke faɗa wa Katsinawa, sukan ce: “Katsinawa bayinsu ne” saboda su suka fara cin Katsina da yaƙi. (Ingawa 1990)

3.2.1 Katsinawa da Kabawa da Haɗejawa

Barkwancin da ke gudana tsakanin Katsinawa da Kabawa ba ta yaƙi ba ce, ta auratayya ce. Wato Katsinawa ne suka ba wa Kabawa aure. An ce Sarkin Katsina Tsaga-Rana 1751-1764 ya ba sarkin Kabi Kanta auren ‘yarsa wanda ta haifi ‘ya’ya da yawan gaske. Wannan dangantakar ce ta ƙara donƙon zumunci tsakaninsu da kuma ɗorewar zaman lafiya har zuwa yau. (Dano 2015)

Amma wasan barkwancin da ke tsakanin Katsinawa da Haɗejawa yaƙi ne ya haifar da shi sakamakon an samu yaƙe-yaƙe tsanin Katsina da Haɗeja.

3.3 Kanawa da Daurawa da sauran Ƙasar Hausa.

Wasu sun ce wasan barkwanci tsakanin Kanawa da Daurawa ya samu ne sakamakon gwada ƙwarin ƙashi da aka yi tsakanin ƙasashe biyu. Wasu kuma cewa suka yi alaƙar jii ta haddasa wasan, wato Kanawa ‘ya’yan Bagauda ne, Daurawa kuma ‘ya’yan Garori ne. A kan wannan dangantakar ne aka ce wasan jika da kaka ne ke tsakaninsu. Sauran wasan na barkwanci sun haɗa da tsakanin Kanawa da Ningawa wanda ita ta samu ne sakamakon fafatawar da aka yi da juna. Sai kuma tsakanin Kanawa da Zazzagawa da kuma Kanawa da Zamfarawa da sauransu. (Tukur 1991)

3.4 Barkwanci Tsakanin Hausawa da Wasu Ƙabilu

Tarihi ya nuna cewa yaƙe-yaƙen da Hausawa suka gwabza bai tsaya tsakaninsu ba kawai ba, akwai wasu artabun da aka kwasa tsakaninsu da wasu ƙabilu musamman Nufawa da Barebari da kuma Fulani. Bayan yaƙi ya lafa, zuciya ta sanyi ai aka share filin gaba ya koma filin wasa. aga cikin ƙabilun da wasan barkwanci yake gudana tsakaninsu da Hausawa sun haɗa da:

a.      Katsinawa da Nufawa

b.      Katsinawa da Barebari

c.       Hausawa da Kambari

d.     Gobirawa da Yarabawa

e.      Hausawa da Buzaye

3.4.1 Barkwanci Tsakanin Tobasai Na Jini

Da farko dai kalmar Tobasai ta samo asali ne daga kalmar Taubashi wada take nufin ɗan mace ko ɗan namiji, wato ɗan wa da ɗan ƙauwa, ko ɗan ya da ɗan ƙani (Ƙamusun Hausa 2006: 423). Akwai wasan barkwanci na musamman da yake gudana a tsakanin waɗannan mutanen a kusan duk lokacin da aka haɗu da juna. Ana irin wannan wasan sosai domin kowa yana faɗar albarka3cin bakinsa. Ana ma aka yi wasan barkwanci sosai kowa ya faɗi albarkacin bakinsa. Irin wannan wasan yana da tasiri ƙwarai wajen tabbatar da zama lafiya da ƙarfafa zumuntar ‘ya’ uwa na jini da ma sauran al’umma. (Tukur 1990)

4.0 Barkwanci Tsakanin Masu Sana’a

Akwai sana’o’in Hausawa da dama musamman ma na gargajiya waɗanda suke da alaƙa da juna ta fuskar amfani ko yanayin gudanarwarsu ko sarrafawa. Wasu sana’o’in sun dogara ne ga wasu wajen samar masu kayan gudanar da sana’ar tasu, wasu kuma kamar kishiyoyin juna ne. Irin wannan yanayi na zamantakeawar shi yake haifar da kishi da kuma gaba tsakanin juna, wanda kuma ka iya haddasa fitina a tsakanin al’umma. A maimaikon cigaba da irin wannan ƙazamin zaman, sai Hausawa suka ƙirƙiri wasan barkwanci wanda zai kawar da tunanin kishi da gaba domin a zauna lafiya. A dalilin haka, aka samu wasannin raha tsakanin masu sana’o daban-dabam da suka haɗa da: (Tukur 1990)

 4.1 Masunta da Mahauta

A duk lokacin da masunta da mahauta suka haɗu akan yi wasan barkwanci kowa ya yi nishaɗi har da mutanen da suke kusa. Daga cikin kalaman barkwanci da suke faɗa wa juna shi ne, mahauta kan cewa masunta “ga kuɗinsu a ba su fata da kayan ciki” ko kuma su ce “masunta kuna kayan gawa, ina mahautarku take?” Su kuma masunta sukan mayar da martani su ce “mahautarmu tana ga Allah, turun bashi”. (Rabi’u Abbatuwa)

4.2 Maƙera da Wanzamai

Wannan wasan barkwanci tsakanin maƙera da wanzamai ya ƙullu ne sakamakon dangantakar da take akwai a tsakanin sana’o’in biyu. Maƙera suna ganin su ne masu gidan wanzamai, domin kuwa su ne suke samar musu muhimmin kayan da suke amfani da shi a sana’ar tasu. Ba ma wanzamai kawai ba maƙera na ganin su ne iyayen gidan mahauta da manoma da kuma masassaƙa. Don haka, a duk inda aka haɗu akan taɓa wasan barkwanci kafin a rabu. Maƙera kan yi wa wanzamai su ce musu “wanzam ba ka so a jikinka“. Wanzamai kan mayar da martani su cewa maƙera “maƙeri sai ka ɗanɗana kuɗarka”. (D/Iya 2/10/2019

 Akwai wani wasan barkwanci tsakanin Maƙera da Masassaƙa, inda Maƙera kan ganin su ne masu gidan masassaƙa domin su suke samar musu ƙarfen da suke sassaƙa da shi. Idan an haɗu maƙera kan ce wa masassaƙa “sakke gwanin kashin ice ba na raya ice ba”. Su kuma massaƙa su ce wa maƙera “maƙeri abokin wuta, ko a can tare kuke”.

4.3 Mahauta da Majema

Akwai wasannin barkwanci da ke samuwa tsakanin waɗannan al’umma. Wannan wasa yana da nasaba da ƙarfafa zumuncin sana’arsu. Mahauta suna ganin su ne masu gidan majema tun da sai sun yanka dabba sun cire fatarta sa’annan majema su samu fatar da za su sarrafa. Don haka ne ma majema suke kaɓar dukiyar shara ga mahauta idan lokaci ya yi. Mahauta kan yi wa majema barkwanci suna ce musu, “A ci ƙazanta, a kwana cikin ƙazanta, ai ado da ƙazanta sai majema”. Su kuma majema sukan ce wa mahauta, “Talle ba ta yi audi gori, jikan ma ci bashi”. Haka ma duk lokacin da aka haɗu akan yi raha kafin a rabu. (Shehu 2017)

4.4 Masu Goro da Masu Gishiri

Wasannin barkwancin da yake gudana tsakanin waɗannan masu sana’a, wasa ce ta kyautata zamantakewa saboda dangantakar da suke da ita na zama kamar kishiyoyin juna. Mai sana’ar Goro a koyaushe cikin ban-ruwa goronsa yake, shi kuma mai gishiri babu abin da ya fi tsana ya taɓa sana’arsa kamar ruwa. Don haka, a duk lokacin da mai goro ya haɗu da mai gishiri sai wasan barkwanci ya kaure, mai goro na faɗin Allah ya kawo ruwan sama, shi kuma mai gishiri ya ce ba amin ba. (Lawan 2016)

 Haka kuma akwai sana’o’i da dama da wasan barkwanci ya shiga tsakanin masu yin sana’o’in kamar wasan barkwanci da yake shiga tsakanin masu raƙuma da masu jakai, Direbobin mota da masu raƙuma, masu rake da mai alewa da sauran su.

5.0 Sakamakon Bincike

Haƙiƙa babu shakka wannan bincike ya gano muhimman barkwanci da yake a tsakanin al’ummar Hausawa da makwaftansu da kuma masu sana’o’in Hausawa na gargajiya, wanda sakamakon haka ya sa aka sami wasanni tsakanin masu sana’a da kuma sauran mutane.

Haka kuma, haƙiƙa wannan bincike ya gano cewa, akwai barkwanci a tsakanin al’umma, domin kuwa an sami barkwanci a cikin waƙoƙi da maroƙa kamar ‘yangambara da ‘yankama da ‘yan’adaki bzu da ‘yandamalgo da kuma ‘yangalura da sauransu. Haka kuma, wannna bincike ya gano barkwanci a kafafen sadarwa kamar: Facebook da Tik-tok da Gidajen Rediyo da Talabijin da sauran kafafen sadarwa.

6.0 Kammalawa

Wannan bincike ya yi ƙoƙarin kawo barkwanci a tsakanin al’ummar Hausawa da yadda ya sami ɗaurin gindi a tsakanin al’ummar Hausawa, wanda ya zame musu garkuwa ga jindaɗin rayuwa. Barkwanci zantuka ne na raha da wasu mutane waɗanda Allah ya hore wa iya raha da magana da ban dariya da suke yi wa mutane. Barkwanci ya samu ne bayan Hausawa sun gama yaƙe-yaƙe a tsakaninsu. Wannan ya haifar da ƙirƙiran wasan barkwanci don kawar da tashin-tashina da rigingimun da suka dabaibaye rayuwar Hausawa. Wasan barkwanci hanya ce ta ƙulla/ƙara dnƙon zumunci da haɗin kai da ƙaunar juna da inganta zamantakewa tsakanin Hausawa ko tsakanin Hausawa da wasu maƙwaftan ƙabilu. arkwanci yakan sa raha ko nishaɗi da manta zogin abun da ya faru a baya. Zumunci da haɗin kai da manta abin da ya faru a baya na artabun da aka yi tsakanin masu wasanin barkwanci kuwa, su ne suke haɗuwa su samar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin al’umma.

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2022). Ƙabilu a tunanin Bahaushe: Duba cikin labaran barkwanci. Sarcouncil Journal of Humanities and Cultural Studies 1(1), 27-32. https://zenodo.org/record/6418660.

Bunza, A. M (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos Tiwal Nigeria Limited.

CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Ahmadu Bello University, Press

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Triumph Publishing Company.

Gusau, S. M (2008). Adabin Hausa a Sauƙaƙe. Century Research and Publishing Lt.

Gusau, S. M. (2013). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Benchmark Publishers Lt.

Ingawa, I. L. (1990). Katsina Ɗakin Kara. Katsina: Arewa Printers Limited.

Lawan, N. (2023). Barkwanci mai labari a Matakin Nazari: Cikin Journal of Contemporary Hausa Studies. Vol 5 no 1 Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Ya’aduwa.

Sanyinnawal, S. I. (2012). Cuɗeɗeniyar Sana’o’in Gargajiya a Adabin Bakan Bahaushe. [Kundin Digiri na Biyu] Sashin Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Tukur, A. (1991) Wasannin Barkwanci A Ƙasar Hausa. Rukhsa Publications.

Umar, M. B. (1986). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Yahaya, I.Y, Gusau S.M, Yar’aduwa T.M (1992) Darussan Hausa Don Manyan Makaratun Sakandire Littafi na biyu Zaria: Ahmadu  Bello Uniɓersity, Press.

Post a Comment

0 Comments