Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Sunnah Ta Koyar Game Da Mai Fama Da Jinnu, Da Yadda Za A Kare Kai Kafin Fitinuwa Da Su

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Tambayata Ita ce: Yaya Sunnah ta koyar ga wanda jinnu ke damu, da kuma kariya daga su ko da ba suna jikin Ɗan Adam ba ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, ƴar uwa game da wanda ke fama da jinnu, ya tabbata za a iya yi masa ruƙ'ya wadda ba ta saɓa wa Shari'a ba, saboda hadisin Aufu bin Malik Al'ashja'iy da ya ce: Mun kasance muna yin ruƙa a zamanin jahiliyya, sai muka ce; ya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam mene kake gani game da hakan? Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: " Ku nuna min ruƙan naku, babu laifi ga ruƙa matuƙar babu shirka a cikinta". (Sahihu Muslim 2200).

Wannan ya zama dalili a kan yin ruƙ'ya matuƙar an kaucewa shirka a cikinsa. Ibn Hajar ya ce: "Haƙiƙa malamai sun yi ijma'i a kan halascin yin ruƙ'ya idan an kiyaye sharuɗɗa guda uku, ya zama da maganar Allah SWT za a yi, ko da sunayensa da siffofinsa, ya zama da harshen Larabci za a yi, ko kuma wani harshen da aka san ma'anarsa, ya zama an ƙudurce a zuci cewa ita ruƙ'ya ba ita ce take tasiri da kanta ba, tana yin tasiri ne da nufin Allah SWT. (Duba FAT'HUL BÁRIY (10/227).

Shi ma Shaikhul Islam Ibn Taimiyya ya faɗa cewa: "Malaman Musulunci sun hana yin ruƙ'yar da ba a fahimtar ma'anarta, saboda ita ce matattarar shirka, ko da kuwa mai yin ruƙ'ya ɗin bai san ita shirka ba ce". (Duba littafin AKHBÁRUL JINNI WASSHAYAƊEEN shafi na 21, na Ibn Taimiyya).

Wato dai dole mai son yin ruƙ'ya ya yi ta da maganganun Allah, da sunayensa da siffofinsa, kuma ba a so a yi ruƙ'ya da kalmomin da ba a san ma'anarsu ba, haka kuma ba a son mutum ya riƙa tunanin cewa ita ruƙ'yar ce za ta samar da waraka da kanta, wato a ƙudurce cewa Allah ne zai ba da lafiya.

Yana daga cikin hanyar samun kariya daga jinnu: kiyaye farillai da wajibai, da nisantar haramtattun al'amura, da yawan tuba daga dukkan munanan ayyuka, da yawan kyautata yin zikirori da addu'o'i, da isti'azozi da shari'a ta yarda da su.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments