LALACEWAR AL'AMURA TA SANADIYYAR SHAFAR ALJANIN SOYAYYA (JINNUL ASHIƘ)
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Ina fama da laluran Jinnul ashiƙ kuma a yadda nake tunawa ni tun ina yarinya abun ya kamani sanadiyyar lalata da wasu maza sukai tayi dani, Wlh har tunanin in kashe Kaina nakanyi, Saurayi fa yazo Se Abu yaki yiwuwa sai ya gudu, aljanin yana samin bakin jiki, ga fargaba da damuwa Mara dalili ko kuma Abu kaɗan na Mayar dashi babba, kawayena nakusa da nake son su a sanadiyan aljanin nan da matsalolinshi duk mun rabu, Ina cikin damuwa wlh.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.
Da farko dai abin da nake so ki fahimta shine ita
larurar shafar bakin aljani wanda ake kira da JINNUL ASHIƘ ana samun waraka daga gareta, itama tana da
magani kamar dai kowacce irin chutar dake damun Dan Adam.
Kuma hanyar samun waraka daga gareta ita ce
lazimtar ayyukan bin Allah ako yaushe, musamman ma yawaita karatun Alƙur'ani da zikirai,
Musamman azkar ɗin safiya da
maraice da sauran zikirai da mutum zai rika yi ko yaushe.
Sannan ki kaurace wa saurarar kade-kade da
wake-wake, ki nisanci yin tabarruji wato ina nufin kamar sanya tufafi matsattsu
ko masu bayyanar da siffar jikinki, ko fesa turare alokacin da za ki fita waje,
ko yayin shiga cikin jama'a.
Daga cikin addu'o'i ko magunguna masu karfi wajen
magance shafar jinnul Ashiƙ akwai :
1. Yawaita La haula wala Ƙuwwata illa bil Lah (1,111 kullum) da niyyar neman waraka daga Allah da neman
kariyarsa daga sharri da makircin wannan shaiɗanin.
2. Ki samu
ciyawar Za'afaran da kanumfari da dusar si'itir, (idan ba'a sameshi ba, ayi amfani da busashen ganyen tumfafiya) ki
haɗasu waje guda ki dakasu (ba sai sunyi laushi ba) sai ki
samo jan Almiski (red musk) ki narkashi sannan ki zubashi akan haɗin wannan maganin sannan a gaurayashi baki ɗaya. za ki rika damkarsa kadan-kadan kina yin hayaki
dashi safe da yamma kuma kina tsugunawa bisa hayakin kina turara gabanki. In
sha Allahu wannan shaiɗanin bazai Ƙara zuwa ya sadu dake
cikin mafarki ba. Kuma da dolensa zai tattara kayansa ya fita daga jikinki.
Bayan waɗannan akwai wasu
fa'idodin domin magance shafar aljanu ko sihiri. Amma dai ki fara jarraba
wannan ɗin tukunna. Idan kina bukatar Ƙarin bayani ko Ƙarin wasu fa'idodin za ki iya tuntubar ZAUREN FIƘHU akan wannan lambar
07064212990.
Wadancan abubuwan da suka faru dake lokacin
kuruciya, ki daukeshi amatsayin jarrabawa ce daga Allah. Don haka kici gaba da
kulawa da shawarwarin da aka baki tare da yawaita sallolin dare da addu'a domin
samun mafita cikin taimakon Allah.
WALLAHU A'ALAM.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.