Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Yin Sallar Istikhara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam. Dan Allah ina son a yi min bayanin yanda ake Sallar istihara. Allah ya ƙara ilmi mai amfani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam. Sallar istikhara sallah ce da ake yin raka'o'i guda biyu kamar yadda ake yin sauran sallolin nafila, abin da ke bambanta su shine niyya. Ana yin sallar istihara ce don barin ma Allah zaɓi a kan wata buƙata da mutum ke da ita. Sannan kuma Sallar istikhara sunnah ce ba farilla ba. Bayan mutum ya kammala sallar, sai ya karanta wannan addu'ar:

اللّٰهُمَّ إِنِّيْ أَسْتَخِيْرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيْمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الغُيُوْبِ اللّٰهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأمْرَ (وَيُسَمِّيْ حَاجَتَهُ) خَيْرٌ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِيْ وَيَسِّرْهُ لِيْ ثُمَّ بَارِكْ لِيْ فِيْهِ وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ فَاصْرِفْهُ عَنِّيْ وَاصْرِفْنِيْ عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ، ثُمَّ أَرْضِنِيْ بِهِ

Allahumma inni astakiruka bi'ilmika, wa astaƙdiruka biƙudratika, wa as'aluka min fadlikal azhim, fa'innaka taƙdiru wa aƙdir, wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamul guyub, Allahumma inkunta ta'alamu anna hazal amra (sai ya ambaci bukatar tasa), Khairunliy fiy diniy wama'ãshiy wa ãƙibati amri faƙdurhu liy wa yassirhu liy, thumma bãrik liy fihi, wa inkunta ta'alamu anna hazal amra sharrun liy fi diniy wama'ashiy wa ãƙibati amri fãsrifhu anniy wasrifniy anhu waƙduriyal khaira haithu kana thumma raddiniy bihi

FASSARA:👇

Ya Allah ina neman zaɓinka domin ilminka, kuma ina neman ka bani iko domin ikon ka, kuma ina rokonka daga falalarka mai girma, domin kai ne mai iko, ni kuwa bani da iko, kuma Kaine masani, ni kuwa ban Sani ba, kuma Kaine masanin abubuwan fake, Ya Allah! Idan kasan cewa wannan al'amari (sai ya ambaci bukatar tasa) alheri ne gareni a cikin addinina, da rayuwa ta, da kuma karshen al'amarina, - a wata ruwayar da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - ka ƙaddara mini shi, kuma ka saukake mini shi, sannan ka albarkaceni a cikin sa, kuma idan kasan wannan al'amari sharrine a gare ni a cikin addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina - a wata ruwaya; da magaugaucin al'amarina da majinkircinsa - Ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar dani daga gare shi, kuma ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma ka sanya ni in yar da shi.

Ana karanta addu'ar ce bayan an idar da sallar an yi sallama, sai mutum ya ɗaga hannuwansa sama, ya yi yabo da jinjina ga Ubangiji, sannan ya yi salati ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. Daga nan kuma sai ya yi ita waccan addu'ar ta istikhara, bayan ya gama sai ya sauke hannayensa kawai ba sai ya shafa a fuska ba.

Kuma ya halasta ga wanda ba ya iya yin ta da Larabci ya furta ma'anoninta da Hausa, ko kuma da duk harshen da yake iyawa, amma a yi addu'a da Larabci shi ne yafi kamar yadda malaman Fiƙhu suka bayyanar.

LOKACIN YIN SALLAR ISTIKHARA:

Magana mafi inganci za ka iya yin ta a kowani lokaci. Mafi falala cikin dare. Amma banda lokacin da aka hana yin nafila a cikin sa..

Duk wanda ya nemi zaɓin Mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to bazai yi nadama ba. Insha Allah. Domin Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: "Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka ƙuduri aniya, to ka dogara ga Allah.

Ba mafarki ake yiba kamar yadda mutane dayawa suka ɗauka, ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai kaji zuciyarka taƙara nutsuwa da yarinyar, idan sana'ace kake so kafara sai kaji zuciyarka ta nutsu da sana'ar.

Wannan shi ne yadda ake yin sallah da addu'ar Istikhara, kuma kai ake so ka yi da kanka, ba wani ne zai yi maka ba, wannan ita ce Sunnah.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments