Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsayin Zuwa Wajen Mai Bugun Kasa/Duba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam don Allah ina da tambaya. Malam nine naje wajen Malamin bugun kasa nace ya dubamin acikin samarina su uku 3 waye yakesona tsakani da Allah sai Malamin ya cemin ɗaya 1 ko na Aureshi zamu rabu, biyun kuma duka akwai alkhiri a tattare dasu kuma wanda nafi so wai shine bayida alheri. To Malam wai ancemin babu kyau to Malam yaya matsayina a Musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaykumussalam

Manzon Allah ya hana zuwa wurin boka/mai duba. Ya ce: ”Duk wanda yaje wurin boka/mai duba kuma ya gaskata shi toh lallai ya kafircewa abin da aka saukar wa Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam (Alkur'ani)” Imam Ahmad ya ruwaito, an karbo daga Abu huraira. A wata ruwaya dake cikin Swahihu Muslim :.”baza'a karɓa masa sallar sa ta kwana arba'in ba.”

A cikin waɗannan hadisai da ire-irensu sun nuna girman laifin zuwa wajen boka/mai duba. Amma tunda an gaya miki babu kyau kuma kinyi nadamar zuwa toh babu komai akanki sai a cigaba da istigfari sannan a nesanci sake zuwa nan gaba..

Manzon Allah ya koyar da yadda akeyin istikhara ga duk mai neman zaɓin Allah cikin al'amurran sa. Sai a nemi littafin hisnul Muslim a samu malami/malamar sunnah don a koyi yadda ake yin istikhara a sunnance.

WALLAHU A'ALAMU.

Amsawa 🏻

MALAM NURUDDEEN MUHAMMAD MUJAHEED

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments