Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Cin Bashin Waya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum. Malam ina fata kana chikin koshin lpy , Allah yasa haka Amin. Malam ya matsayin chin bashi da akeyi na Sim, kuma za ka ga wasu idan sunchi ya yi yawa saisu jefar da Sim ɗin ,sannan idan mutum ya mutu da wannan bashin a wayan sa ya matsayin sa yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam. Ameen Ya Yayyu Ya Ƙayyum 🤲🏽:-

Misalin masu Cin Bashi Su biya, Wannan Babu Laifi, duk da dai Akwai Maluman da Suka ganin Cin sa Riba Ce shima, Amma a zance mafi inganci ba Riba ba ce, Misali Koda kuwa Idan kin nemi naira 100, sai su cire naira 1, wato sai su ba ki naira 99, Alhalin Kuma ke Naira 100 Cikakken sa Kika Nema, Kuma idan kin tashi biya Hakan za ki Biya Cikakken Naira 100 ne, toh Wannan Babu Laifi.

Domin su ma, waɗanda suke bayar da Bashin da kuke karɓa a gurin su, Suna Cire Naira Ɗayan ne a dalilin massage ɗin da za su tura miki ta wayarki na wannan Bashin Naira 100 da Kika Nema a gurin su, shine suke cire naira 1 ko 5 daga Cikin Bashin da Kika karɓa sai su ba ki naira 99 ko 95, wani Kuma ba su Cire ko sisi daga Bashin da suke ba shi.

Yanzu kamar misalin ne ke idan Za ki turawa wani massege ai Ana cire naira 4 ko 6 Komin kantantar Sakon da za ki tura, toh Suma haka ne masu bayar da Bashin. Ko Kuma ai yanzu a wani gurin Idan kin je Siyan Katin Waya, Sai an Kara Miki Naira 10, idan na 100 za ki Siya Sai kin bayar da 110 ko 120, toh irin wannan misalin shine Suma Suke Cire Naira 1 idan kin nema Bashin a gurin su, Sabida Haka Suma Kasuwanci suke Yi ba laifi karɓar bashin su, Amma sai idan Babu wani Hanya sai Dole kin karɓa. Domin wasu Maluman Kai Tsaye Suna ganin Cewa Haramun ne. Wallahu A'alamu.

Toh waɗanda Kuma suke karɓar Bashi a SIM nasu Idan ya yi Yawa su Ƙi biyan Bashin, daga karshe ma sai su Cire SIM ɗin su Yar da shi, toh Su Sani Cewa Bashin Layin su na Kansu, idan ba su biya su anan Duniya ba, toh za su Lahira su biya da Ladan ayyukan su, Koda kuwa naira 1 ne Suka karɓa ba su biya ba, toh idan ba su biya anan Duniya ba a Ranar Alkiyama za su je su biya su ko ba ka so.

Sa'annan Biyan da za su yi Bawai Kuɗin ne za su Cire su biya ba da shi ba, A'a ladan ki, da Shi Za'a ɗauka a biya su, idan Kuma Arne ne Toh Za'a Debo Zunuban sa a zuba miki, idan kuma Musulmi ne Mai kuɗin Za'a Debo Ladan ki a Zuba masa, a Debo Zunuban sa a zuba miki, Wannan Shine Sakamakon da Za'a Yi a Ranar Alkiyama. Cin Bashi hatsari ne Yar Uwar.

Sannan Bashi Ko na sisin Kobo ne, Yana Hana mutum Jin daɗin Kwanciyar Ƙabarin sa, mutum Bai taɓa Samun Natsuwa da Kwanciyar hankali a Cikin Ƙabarin sa, Har sai ranar da aka biya Masa wannan Bashin da ake bin sa, idan ba'a biya Miki ba har Ranar Alkiyama, toh kina Cikin masifa da Tashin hankali daga Ƙabarin ki, Misalin Kin karɓar Bashin naira 100, sai Kika mutu ba ki biya ba. Toh idan Kina da Yara Sai Suka duba Suka gani ai ga shi ana bin ki Bashi, Suka Biya Miki wannan Bashin, toh a Ranar da Suka Biya Miki wannan Bashin a Ranar ne za ki Fara Samun Sawaba daga Azabar Allah a Cikin Ƙabarin ki ta dalilin cin Bashin Nan MTN ko wanin sa da kika yi.

Amma matukar ba'a biya Miki wannan Bashin ba, toh kina Cikin tashin hankali da masifa a Cikin Ƙabarin ki har Ranar Alkiyama, a tafi Hisabi a je a ɗauki Ladan ki a biya su da Shi. Allah ya Shiryar da mu da Cin Bashi kowanne iri ne ma, Cin Bashi kowanne iri ne matukar mutum ba biya zai Yi ba, Wai mutum Yana ganin ya ci Banza ko ya fi Karfin Wannan Mai bashin, toh ba'a ci banza ba, an ci Banza anan Duniya Kam, Amma idan An Je Barzakiyya daga Cikin Ƙabarin ki za ki gane Cewa Lallai da kin sani da Kin biya Bayin Allah Bashin su ko da kuwa Kobo 1 ne.

Wannan fa Bashin naira 100 kenan, idan kuma Bashin kuɗin Yana dayawa fah? Inna illahi Wa'inna illahin Rajee'um, Mu ji tsoron Allah Yan Uwa Akwai Hisabi da Kwanciyar Ƙabari a gaban mu sisi 1 Tak wallahi zai hana ki Kwanciyar Ƙabarin ki. indai na wani ne Kika karɓa Bashi Kika Ƙi Biyan su, kina ganin kin fi Karfin Su ko Kuma Kika Zalunce su, Kwanciyar Ƙabarin ki na zuwa, Azabar Allah da Za ki tarar kaɗai a cikin ƙabarin ki kafin a tashi Alkiyama idan an bar ki a Haka ya ishe ki ballatana ace Za'a tafi Hisabi Allah ya tsare mu Ameen.

Bashi Masifa ce, Bashi Bala'i ne, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam Ya ce idan mutum ya Mutu an gayyaci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya zo yayiwa wannan Gawar Sallah, kafin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi masa Sallah sai ya tambayi masu Gawar Shin akwai masu bin sa Bashi ne? idan an ce Eh Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam zai ce a biya masa ko a yafe masa kafin ayi masa Sallah, idan wadda yake bin Bashi ya ce ba zai yafe ba Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam zai ce toh kuyiwa Gawar ku Sallah, idan kuma an biya masa Bashin sa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam sai ya wuce gaba yayiwa wannan Gawar Sallah a je a Binne sa, indai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam zai ƙi yiwa wani Sallah a dalilin Bashi kenan akwai hatsari cin Bashi wajibi ne a kiyaye dokokin Allah sai a zauna lafiya, idan kunne ya ji, jiki ya tsira Allah ya shirya. Dafatan kin gane Koh??

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments