Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Zan Iya Ciyarwa Amadadin Azumin Kaffara?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum! Allah ya karama malam lafiya da nisan kwana. Allah gafarta malam tambaya gareni. Ina tafiya da mota akan Kaduna-Kano high way ina tuku ata hannu ciki wato speed lane sai kawai kwatsam wani tsoho dan shekara tamanin yazo ya bugi motata ata gefen passenger.  Anan Allah ya karɓi ransa. Tambayan shine, zanyi mashi azumin kaffara ko zan iya ciyarwa? Nagode sosai.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Wannan irin kisan shi ake cewa 'KISA BISA KUSKURE' Kuma lallai za ka biya diyyah ga dangin wannan dattijon, domin biyansu hakkinsu na ɗan'uwansu ko mahaifinsu da ya mutu ta sanadiyyarka. Sannan zakayi kaffarah domin tuba ga Allah (SWT) dangane da bawansa wanda ransa ya salwanta ta dalilinka. Kuma kaffarar ana yinta ne ta hanyoyi biyu kaɗai. Kodai ka 'yantar da bawa ko baiwa, ko ka kayi azumin watanni biyu ajere (wato kwana 60 kenan).

Babu Zaɓin ciyarwa game da kaffarar rai kamar yadda bayanin yazo acikin Alƙur'ani Mai girma.

WALLAHU A'ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments