Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Macen Da Ta Yi Zina, Ta Yi Aure Ba Tare Da Ta Yi Istibra'i Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam Barka da yau dafatan kana cikin koshin lafiya, Allah ya sakawa malam da Alkhairi, dan Allah malam tambaya na zo da ita ina neman Amsa, ga tambayar kamar haka; Mace ce yaranta huɗu amman kafin aurensu ita da mijinta suna Zina so batayi istibra'i ba ankayi auren har Yara huɗu to yanzu auren nasu valid ne ko invalid?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu;

Wannan auren nata bai yiwu ba dole a warwareshi ta je tayi Istibra'i sa'annan a sake daura shi.

MA'ANAR ISTIBRA'I: Istibra'i shine neman sanin kububtar mahaifa daga ɗaukar ciki. ko kuma zaman jiran a haife cikin da mace ke ɗauke da shi bayan tabbatar da samuwar sa.

Idan namiji ya sadu da mace wadda bata hanyar aure ba, ta hanyar zina ne ko kuma fyaɗe toh wajibi ne sai ta yi itibra'i kafin mijin ta ya kusance ta in tana da aure ko kuma kafin ta yi auren Akwai fuskoki biyu da suka nuna rashin halaccin auren:

1. FUSKA TA FARKO: A karkashin Addinin Musulunci bai halatta a Ɗaura ma mace aure da wani sabon Miji ba, har sai ta tabbatar da cewar babu komai a cikin mahaifarta. a Bisa wannan dalilin shi ya sa Mata suke yin iddah bayan sun fita daga hannun Mijin su kafin su sake aurar wani Mijin daban.

Hakanan duk Matar da ta yi Zina, ko budurwa ce ko bazawara, toh bai halatta a Ɗaura Mata aure ba har sai tayi Istibra'i. Wato tayi Jini uku, ko kuma a Ƙalla jini guda (a fa'dar wasu Maluman).

Toh idan har Mace ta yi Aure ba tare da yin Istibra'in nan ba, Malamai sun ce auren bai yiwu ba. Ba za'a kira irin wannan zaman da sunan "AURE" ba. Har sai an warwareshi ta je ta yi Istibra'i sannan a sake ɗaura sabon aure da sabon sadaki Allah ya shirya Zina masifa ce da Bala'i Yan Mata ku Ji tsoron Allah wallahi.

2. FUSKA TA BIYU: Duk Matar da ta zamanto ita Mazinaciya ce, toh bai halatta a Ɗaura mata aure da cikakken Mumini wanda ba ya Zina ba.

Hakanan duk Namijin da ya zamanto shi ba Mazinaci ba ne, bai halatta ya auri Matar da bata yin Zina ba. Sai dai idan sun tuba Sahihin tuba irin tubar da ba za'a sake koma Ruwa ba, Ita Mazinaciyar sai ta yi istibra'i. Sannan zai halatta Mumini ya aure ta. Allah ne ya fada a cikin ayah ta Uku a cikin Suratun Nuur.

الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ

Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai. (Suratul Nur Ayata 3).

Al Imam Ahmad bn Hanbal ya ruwaito hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-Aas (R.A) ya ce, "Wani Mutum Mumini ya nemi izinin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) akan yana so zai auri wata Mata mai suna UMMU MAHZOUL wacce ta kasance kowa ya san tana yin Zina. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya karanto masa wannan ayar ta cikin Suratun Nuur cewa; "MAZINACI BA ZAI AURA BA SAI DAI MAZINACIYA KO MUSHRIKA. KUMA MAZINACIYA BABU MAI AURENTA SAI MAZINACI KO MUSHRIKI. KUMA AN HARAMTA WANNAN BISA MUMINAI". (A duba Hadisi na 11359 a cikin Sunanul Kubrah ta Imamun Nisa'iy).

Hakanan akwai wani Sahabi mai Suna MARTHAD IBNU ABI MARTHAD (R.A) ya taɓa neman izini a wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) cewa yana so zai auri wata Mata mai suna 'UNAAƘ" ta kasance Mazinaciya ce a garin Makkah. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi shuru bai ba shi amsa ba, har sai da wannan ayar ta cikin Suratun Nuur ta sauka. (A duba Sunanu Abi Dawud hadisi na 2051. Da kuma Sunanun Nisa'iy juzu'i na 6 shafi na 66 a cikin kitabun Nikahi).

Duk da cewa akwai Malaman da suke ganin cewa wannan ayar Mansukhiyah ce, toh amma Bisa waɗannan hujjojin ne Malamai irin su Imamu Ahmad suka dogara. Sun ce bai halatta a auri duk Matar da tayi zina ba, har sai bayan ta tuba. Don Haka auren nata bai ɗauru ba.

Matsayin shi Saurayin shine sunan sa Mazinaci Kuma lallai laifin zinar yana nan a kansa. Idan bai tuba ba, yadda ya yi haka shima za'ayi masa. Kafin kuma ya koma ga Allah ya karɓi sakamakon abin da ya aikata.

Yan Mata Zina Bala'i ce, Zina masifa ce, wallahi akan ki Yarda da saurayin ki ya yi Zina da ke gara kin Mutu yafi miki, Saurayin ki ko ya kawo a kanki Indai ya ce miki toh me ya rage ai kin zama nashi ki ba shi kanki, wallahi ki ja masa layi ya hakura har sai an ɗaura Auren ku tukuna kin zama nashi kafin ya yi duk abun da yake so da ke.

Amma a yanzu wai ke kin sake bakin cewa wai Saurayin ki Yana Mutuwar Son ki ai kuna son junan ku kamar yaya ai Auren ki zai yi, don haka ya yi ta bin ki ya ce ki ba shi kanki tunda shi zai Aure ki, wallahi idan kin yarda kin ba shi kanki kin yi Asara mafi girman asara a rayuwar ki, sa'annan ke ba ki San waye yake son ki ba, Kai wallahi ba ki San mene ne ake kira Soyayya ba, da ace kin san me ake kira Soyayya toh ba za ki taɓa Kiran wadda zai yi Zina da ke ya bata rayuwar ki gaba ɗayan sa ki ce wai shi ne yake matukar son ki ba.

Duk wadda yake son ki tsakanin sa da Allah, yake son ki zama Matar sa wallahi Hannun ki wannan tsoron tabawa zai ji, duk wadda zai ce ki ba shi kanki ya yi Zina da ke ai shi ne zai gane cewa lallai kina son sa, ko kuma ai Auren ki zai yi toh idan kina neman Makiyin ki Wadda zai iya kashe ki, sa'annan dãman jikin ki yake so bawai ke yake so ba, kuma yana samun jikin naki shikenan ko ya kawo duniya ne a kanki haka zai bar ki da su tunda ke mai kwaɗayin ce ku ji tsoron Allah Yan Mata da Matan Aure.

Zina masifa ce da Bala'i, ba za ki gane hakan sai ranar da kika aikata shi ki dawo kina yin nadamar da ba zai amfane ki ba, rayuwar ki gaba ɗayan sa ya tashi a iska an miki tabon da har ki koma ga Allah ba za ki taɓa mantawa, an miki illar da ke kanki kin tuba amma kullum zargin kanki da kanki kike yi, an miki tabon da ke kanki za ki dawo tamkar mahaukaci duk wannan illar Zina ce Wallahi ku ji tsoron Allah duk Karfin Sha'awar ki indai Saurayi da Zina ya zo miki ki rabuwa da shi ko da kuwa Karfin Sha'awar ki zai sa ki mutu gara ki mutu ba ki aikata Zina ba akan ki biyewa zuciyar ki da na saurayin ki kiyi Zina. Allah ya tsare.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments