Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Sakin Aure Yana Yin Expire?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaikum malam Dan Allah gawani post suna bukatar Karin bayani sosai kan su biyewa San zuciyar su Allah kasa mudace ameen. " Sister Dan Allah ki6oye I'D na, Munrabu da mijina har saki uku yau kusan shekara 4 ya hanani aure ya hanani kula kowa " shi burinsa inkoma gidansa Kuma duk iyayenmu sunsan saki ukune Kuma gsky munasan junanmu Sosae " sannan ya ce bazan auri wani ya kwanta daniba! Shine wai yakecemin wai wani abokinsa ya ce tunda mundade da rabuwa sakin yanayin expire"" Dan Allah Wai da gaskene a addini saki yana expire " Ngd duk wacce tazageni itada mahalicci🙏

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:-

Toh Subhanallah Wal'izu billah Inna illahi Wa'inna illahin Rajee'um, Lallah duniyar ta zo karshe Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi Gaskiya Cewa Nan gaba Za'a Rika Halatta yin Zina a matsayin Aure, yanzu ga alama Wal'izu billah😭.

Wallahi Ki gaya mata ta ji tsoron Allah ta sani Cewa za ta mutu, Sa'annan ta sani Cewa akwai Azabar Ƙabari, Akwai Ranar tsayuwa a Ranar Hisabi, Akwai Tsallake Siradi. Don Haka wallahi su ji tsoron Allah da Kuma Azabar Allah, Koda a ce Mijin ya zo mata da irin wannan Maganar Cewa su sake yin Aure ai yanzu sakin ya yi Expired, kada ta taɓa Amincewa da Bukatar sa, Matukar ta biyewa son Zuciya ta koma gidan sa wai sakin ya Mutu, toh Zaman Zina kaɗai za suyi bawai Zaman Aure ba ne.

Babu wani hadisi ko da a ce Hadisin karya ce, Babu inda aka taɓa Cewa Wai ai idan an sake Mace Sakin Saki uku idan ya yi Shekara ko ya jima ai sakin Yana yin Expire, ai Hukuncin Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ba irin Hukuncin Yan Boko ba ne, ai Hukuncin Allah bawai Hukuncin Mutane Yan Boko ba ne, Hukuncin Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Babu Expire a cikin sa, kuma Babu wadda ya isa ya Chanja wannan Hukuncin daga inda Allah ya ɗaura shi.

Sabida Haka Kafin ta koma gidan Sa, sai ta Auri wani Namijin daban, idan tayi Sahihin Aure Wannan Mijin da ya Aure ta ya yi Jima'i da ita sun ji daɗin Junan su ta dandani zumar sa Shima ya dandani nata, sai wani Sausayi ya shiga a tsakanin su Mijin ya ce ya sake ta, toh Nan ne za ta dawo tayi iddar ta na Jini uku, kafin tsohon Mijin ya sake Auren ta.

Amma Wai Cewa ai sakin Aure Yana yin Expire wannan Karya Ce da kuma Jahilci, ko Shekara 1000 zakuyi Ba zai mutu ba Sakin, Ni ban taɓa jin Haka ba sai Yau Inna illahi Wa'inna illahin Rajee'um Subhanallah, Hasalima shi Wadda ya Gaya musu hakan Yana son ne ya sa Rayuwar su Cikin Hallaka na Zina, wato ya rudesu su bi maganar sa a mayar da Auren, toh idan sun Komar da wannan Auren Zaman Zina kaɗai suke Yi bawai Zaman Aure ba. A yanzun ma waye ya San iya abun da suke Aikatawa da Mijin domin komai za su iya Yi indai Suna Haɗuwa, sa'annan ta ce wai suna son junan su kin ga kenan akwai yiyuwa cewa suna Haɗuwa, toh yin chatting ko Hira ma a hukuncin Saki uku Haramun ne Haramun ne Namiji ya tsaya yana yi da wannan matar, kuma Daman dole ne Allah ya jarbe su da son junan su sosai fiye da tunanin su.

Sa'annan Ina ga ita wannan Matar ma Bata son yin Auren ne kawai, domin hujjar tsohon Mijin ta ai ba hujja ba ne, Cewar Wai idan ta Auri wani Namijin daban ba zai kwanta da ita ba, ai yanzu komai Kai a waye ake yin Sa, tunda ya furta hakan Kuma Yanzu Shekarun su 4 ba tayi Aure ba, toh indai tana son yin Auren ne, ai sai ta fitar da Mijin Auren, idan tana son yin Auren kenan, ta fitar da Miji a Gama komai su tafi gaban Alkali Masanin Shari'ar Musulunci a Kira tsohon Mijin ya zo ayi komai a Rubuce, don Haka idan sun je Wannan Sabon Miji ya gagara Saduwa da ita, toh Daman kun Yi komai a gaban Alkali Sai Mijin naki ya koma gurin Alkali ya yi Masa bayani Alkali ya San wanne Hukunci ne ya dace da shi.

Amma Wai ki biye Masa kina zaune ba Aure don ya ce idan wani ya Aure ki ba zai kwanta da ke ba, sai dai idan wata kila kin biye Masa kina biya masa bukatar sa wato Kuna Zina, toh Nan Kan ai ba za ki so Yin Auren ba, Amma muddin kina son Auren toh Maganar sa Babu inda za ta je a Zuciyar ki tun tuni Kika manta da yin sa.

Haka zalika ai duk Lokacin da akayi saki 3, toh a Lokacin Dukkan ku Allah yana Karawa kowa Son Junan ku, don Haka ko kin ce za ku iya hadiye Junan ku ne saban Son Junan ku, toh fah babu Aure a tsakanin ku har Abada har sai dai wani Mijin ya Aure ki, Kuma Sahihin Aure Nan ma Sai ya yi Jima'i da ke idan sausayi ya shiga ya ce ya Sake ki, Shikenan Sai ki dawo tsohon Mijin ki ya Aure ki, idan kin yi Sabon Aure wannan Mijin bai yi Jima'i da ke ba sai ya Sake ki toh fa har yanzu bai Halatta tsohon mijin ki ya Aure ki ba dole ne wadda ya Aure ki sai ya yi Jima'i da ke idan ya Sake ki shikenan idan Auren ya masa Daɗi ya ƙi sakin ki shikenan Auren sa yana kanki shi Sabon Mijin ki.

Amma a yanzu wallahi ko Shekara 1000 za kiyi ba za ki taɓa koma gidan sa ba Matukar ba ki Auri wani Namijin daban ba. sa'annan ki sani cewa Hira da shi ko zuwa gurin sa ko shi ya zo gurin ki ko kina chatting da shi a waya, duk waɗannan Haramun ne Haramun ne, kai wasu malaman ma suka ce ko tafiya zakuyi zuwa wani gari toh Bai halatta ku haɗa moto guda kina ciki shi ma yana Ciki ba dole ne ya chanja moto kowa ya yi tafiyar sa daban, amma yanzu sai a samu saki uku ne sai ka ga kullum ga su kuna Hira kullum suna call a waya kullum suna chatting kullum suna Zina karshe idan sun ga ba yadda Za'a yi sai kawai su daurawa kansu Aure wai ai an halatta musu ai an mayar da saki ya zama saki 1 ayi ta haihuwa Yaran Zina kawai don Allah Ina za ku sa kanku?

Ke ban da rashin hankali da tunani ma inda ace Yana son ki yana tausayawa rayuwar ki da na Yaran ki yana kaunar ki yana ganin girman Darajar ki da Mutuncin ki da na iyayen ki, don Allah zai Sake ki har saki 3? ai dole ne idan yana son ki Yana tausayawa rayuwar ki da na Yaran ki halin da za ku shiga wallahi dolen sa ya jure ba zai taɓa cika sakin har su zama uku ya rabu da ke ba, amma mutum baya kaunar ki baya Tausayin halin da za ki shiga ya ce ya cika sakin sun zama uku, sa'annan yanzu ki dawo kina cewa wai duk duniya babu wadda kike so sai shi, shin halayyen sa da dabi'un sa da yake nuna miki har saki ukun ya shiga kina tsammanin wai ya chanja su ne? ya chanja ne a yanzu dalilin yafi wata 4 Bai yi Jima'i da ke ba, amma kina dawowa gidan sa da ya yi Jima'i da ke wani Sabon salon rashin cin Mutunci ne zai dawo. haka masu yin Auren kisan Wuta 🔥 karshe idan sun yi sun koma gidan tsohon wallahi nadamar da suke yi yafi na Farkon da aka yi sakin ukkun.

Ki ji tsoron Allah ki rabu da shi ki yi Addu'ar Allah ya kawo Miki wani Namijin ki Aure shi, ki yi Sahihin Aure bawai Auren kisan Wuta ba, wata kila ma idan wani Aure ki shine Wadda zai rike ki tsananin sa da Allah riko na Amana da gaskiya da tsoron Allah Sama da shi tsohon Mijin naki, domin ai duk Wadda zai Yi ta Sakin Mace har Saki 3 toh ai hankali ma Bai ise shi ba da Sauran sa wallahi, Kuma har ya dawo Yana furta mata Cewa Wai ko kin Auri wani ba zai kwanta da ke ba Ina Mai Hankali yake anan bayan Allah ne ya ce ki sake yin wani Auren sa'annan a Sadu da ke shi Kuma ya ce a'a shin yana da hankali? Sa'annan kema Wai sai Kika biye masa ki ka ƙi yin Auren kina zaune, kin yarda ne kawai, Haka zalika Babu wani mu'alama a tsakanin ki da shi matukar bawai gurin Yaran sa yake zuwa ba Yana duba Lafiyar su ko kawo musu Abinci ko magani ba, ba wani mu'alama a tsakanin ku na Jin Daɗi.

Kin ga Kenan wata kila Kuna Saɓawa Allah, Saɓawa Allah da kuke Yi Kullum wata kila Sai Kun haɗu a wani gurin Kun yi abun da kuke so Bukatar ku ta biya, Kuma Bai halatta ku Rika Haɗuwa a wani guri ku kebewa da shi ba, in ba dai Ya zo gurin Yaran sa ba, ko Kuma ki Rika Chatting na Soyayya da shi Haramun ne Haramun ne, wallahi ku ji tsoron Allah Akwai Azabar Allah Sosai matukar ba ki tuba kin Dena ba. Allah ya tsare ya Shirya. Dafatan kin gane Koh?

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments