𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam mene ne hukuncin girka
abinci akan mace, naji wasu suna cewa wajibine matan mutum tayi masa girki wasu
kuma suna cewa ba wajibini, idan taga dama baza tayi ba.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu:
Ko shakka babu wannan tambaya ce mai matukar
muhimmanci, Hakika Malamai sun yi saɓani dangane da
cewa shin wajibi ne Mace tayiwa Mijinta Hidimar gida kamar girka abinci da
sauran su? ko kuma ihsani ne kawai sai idan ta ga dama ne sannan za ta yi?
Mafi yawa daga cikin Malaman da ke Mazhabobin
shafi'iyya, malikiyya, da kuma hanabila, suna ganin cewa ba wajibi ba ne, toh
amma wasu daga cikin Malamai kamar Mazhabin hanafiyya sun tafi ne akan cewa
wajibi ne Mace tayiwa Mijin ta hidimar gida, Hujjar su anan kuwa ita ce, suka
ce Manzon Allah ( Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya raba ayyuka a tsakanin Sayyadi
Aliyyu da kuma Matar sa Fatima, lokacin da ita Fatima ta je gida tana so a
taimaka mata da baiwa wadda za ta rika tayata ayyukan cikin gidan ta, domin hannun
ta har ya yi kanta suna duran ruwa, daga nan sai Manzon Allah ( Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya rabawa kowa aikin da zai keyi, sai Ya ɗorawa 'Yar sa Fatima nauyin kula da ayyukan da suka shafi
cikin gida, shi kuma Aliyyu aka ɗora masa nauyin
kula da ayyukan da suka shafi waje ne.
Wani sashe daga cikin Malaman Mazhabin malikiyya
sun kafa Hujja da wannan ƙissa (ta Aliyu da Fatima) akan cewa wajibi ne akan Mace tayiwa Mijinta
hidimar da ta shafi cikin gida abisa ga al'ada irin ta su, kamar irin su,
shara, wanke-wanke, girka abinci, gyara shimfida, wankan yara, dadai sauran su.
shi Kuma Miji wajibi ne a kansa ya yi ayyukan da
suka shafi waje abisa ga yadda al'adun su yake, kamar irin su, kawo kayan
kwalliya, kawo cefane, nemo abin da za'a ci a sha, dinka musu tufafin sawa,
dadai sauran su. Wato shi Miji ana so ya zama shine yake rike da matsayin
Ministan harkokin wajen gida, ita kuma matar ta zama Ministar harkokin cikin
gida.
Wannan ya sa dayawa daga cikin Malamai suka ce
wajibi ne mace tayiwa Mijin ta hidima gwargwadon irin yanayin yadda al'adar su
take, domin al'adar Mutane takan sha bam-bam daga wani garin zuwa wani garin,
sa'annan yanayin irin nau'in ayyukan su ma sukan sha bam-bam, domin irin
hidimar da Mace 'yar birni zatayiwa Mijin ta, ya sha bam-bam da irin hidimar da
Mace 'yar kauye zatayiwa Mijin ta, hakanan abin da Mace mai karfi za ta iya yi
ba zai zama iri ɗaya da na Mace
me rauni ba, dan haka kenan gwargwadon al'adun kowanne ɓangare da kuma yanayin zamantakewar su.
Nana Aisha Allah ya Kara Yarda gare ta ita ma mun
Sha yin Bayanin cewa tana yiwa Mijin ta Hidima sosai, ga Matar Sayyidina
Abubakar Nana Asma'u ita ma Hidima sosai take yiwa Mijin ta har kula da
dabbobin sa tana yi, kenan wajibi ne kina Mace kiyiwa Mijin ki Hidima ku nema
darasin mu da muka yi akan wannan bayanin za ku ga Cikakken Bayani.
Don haka anan maganar da tafi inganci kuma tafi
dalilai masu karfi ita ce cewa wajibi ne mace tayiwa Mijin ta hidimar gida,
domin lokacin da Fatima ta zo tana neman a taimaka mata da baiwa, Manzon Allah
( Sallallahu Alaihi Wasallam) bai ce da ita cewa ai ke ba wajibi ba ne a kanki
kiyiwa Mijin ki hidima ba, karshe ma dai ya kara tabbatar mata da cewa ita ne
za ta yi wato akan ta ci gaba da yi masa hidima, kuma ace Mace mai matsayi
kamar Fatima 'yar Manzon Allah ( Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma shugabar Matan
Aljanna ga shi an ce sai tayiwa Mijin ta hidima, amma wai wata take ganin cewa
ai ba dole ba ne, wai girki ma sai taga dama zatayi? Lallai, toh wacce Mata ce
anan duniya wadda ta ke da matsayin Nana Fatima a cikin Matan duniya?
Sannan Malamai suka ce Allah ( ﷻ ) ya ce:
ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻗﻮﺍﻣﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
(Maza sune masu karfin iko akan Mata).
Kuma idan aka ce wai Mace ba za ta yiwa Mijin ta
hidima ba to kenan ya zama wajibi sai dai shi Mijin yake yin komai da kansa ita
kuma tana kwance tana kallon sa kenan, toh kuma idan har haka ta kasance, kenan
ya zama Matar ita ce ta ke da iko akan Mijin bawai shi Mijin ba ne yake da
karfin iko akan ta ba, sa'annan kuma da wanne zai ji? Da hidimar cikin gidan
zai ji ko kuma da fita neman abinci? Don haka dai Mata sai dai kuyi hakuri amma
Wajibi ne ku yiwa Mazãjen ku hidima sosai ma kuwa matukar kina son shiga
Aljanna.
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα.
ﺍﻹﺧﺘﻴﺎﺭﺍﺕ ( ﺹ 352)
ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ ( 5/186 )
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.