𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Wata ce tayi aure, Koda tayi aure tanada shekara 17 yanzu haka yaran ta 3 daman mijin Yana da ciwon sugar, ciwon ya taɓa mishi gaba, yanzu haka shekaran su uku baya kwanciya da Matan shi dukan su, amman ita uwar gidan yaranta 7. To yanzu ita gudan abun yana damunta, Kuma tanajin kunya ta ce ya saketa saboda wannan dalili, yanzu haka ko iyayenta bata gayama ba, amman sunada labarin halinda take ciki. shine take tambaya ko za ta iya biyama kanta bukata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam:
Toh Yar Uwa Yin Haka Haramun ne, Haramun ne
Haramun, Haramun ne, Kuma matukar kina yin Haka wato kina Biyawa kanki bukata
fushin Allah na Kanki, Sa'annan Zai Taɓa Lafiyar ki
domin Za ki dawo Mai Yoyon Fitsari, akwai illa sosai da yake haifarwa, Sha'awar
ki zai zo ya ɗauke, infection zai kama
ki, lafiyar jikin ki zai samu matsala sosai, sa'annan Kuma Makomar ki ba zai taɓa Yi Miki Daɗi ba, Kuma Akwai
Azaba Mai Tsanani da Allah ya yi miki tanadi matukar za ki koma Yin Haka. Allah
ya tsare Ameen.
Ai Jin kunyar ta bai Mata Amfani ba matukar za ta Fara
Saɓawa Allah ta wannan, toh Babu wani amfanin Jin kunyar ta,
tana jin Kunyar gayawa Mijin su Cewa a rabu ba amma ba za ji Kunyar Ɓiyawa kanka Bukata ba ai
akwai matsala.
Mata Kuna bani mamaki wallahi, Wai Mace tana
Cutuwa ana cutar da ita, Amma Wai ba zai iya Buɗe bakin ta tayi abun da Addinin ta ya ce ba, Amma za ta iya
aikata Saɓon Allah kuma, ba ki ji
kunyar Ubangijin ki gurin Aikata Saɓon Allah ba, toh
kunyar waye kuma za ki ji? Idan ma kina ganin Kamar ba Wadda yake ganin ki ai
Ubangijin ki Kam Yana ganin ki, kuma shi ne yafi Cancanta da ki ji kunyar sa,
bawai Kunyar Iyayen ki gurin Gaya musu abun da Shari'a ya ce a faɗa ba, bawai Ya Saɓawa Addinin
Allah ba ne.
Ai Gurin Gyaran Aure Babu kunyar da ake ji a
gurin, Shari'a ta ce a Furta duk matsala domin a gyara, don ko a gaban Manzon
Allah Sallallahu Alaihin Wasallam ne, ai Mata Suna zuwa da irin wannan Matsalar
su gayawa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam irin wannan Matsalar Kuma ya
warware musu shi, inda ace za su ji kunya Yaya Za'a samu Hadisan da suke Magana
akan wata Mata ta zo gaban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ta ce Mijina Bai
da Komai Sai Abu kamar Haka? ta kama Karshe bakin zanin ta ta nunawa Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam, toh a gaban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ma an Yi kuma an
warware wannan Matsalar, ballatana a gaban Iyayen ki Wai ba za ki iya Gaya musu
ba? Su Kuma su waye kenan? ai ga Wadda yakamata a ji kunyar sa Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ne, Amma tunda abun da ya shafi Addini ne ba'a
maganar Jin kunyar a gurin.
Amma Wai sai ku tsaya Wai Kuna Jin kunyar Iyayen
ku ba za ki Gaya musu abun da yake damun ku domin a samu hanyar da Za'a yi
gyara komai ba, wannan ai ba hujja ba ce, ai tunda ba za ji kunyar aikata Saɓon ba, toh Bai kamata ki ji kunyar Cewa ba za ki gayawa
Iyayen ki matsalar domin su magance Miki shi ba.
Kuma matukar kin ci gaba da zama a Haka, toh fah
za ki aikata Saɓon Allahn da
yafi wannan ko kina so ko ba ki so sai kin yi abun da kike son, domin Babu
Macen da za ta iya gure irin wannan Zaman Shekara 3 ba Jima'i Kuma kin San
Jima'i bawai ba ki sani ba.
Sa'annan Shi ma Mijin naki, Bai Muku Adalci ba,
wannan ba Adalci ba ne tunda ya San Cewa ga Halin da yake ciki, tunda hakane!
ai Addinin sa ya ce ya Tara Matan nashi dukka sai ya baku Zaɓi, Zaɓin da zai ba ku
Shine, Zai ce muku tunda a yanzu ga Halin da yake Ciki na Ciwon Sugar da yake
fama da shi yana jinya kuma ya San cewa yana cutar da ku, kuma shi a yanzu ba
zai iya yin Jima'i da ku ba, sai ya fi Shekara ko watanni Bai Kusance ku ba,
toh sai ya ce muku duk Wadda take Son ta zauna da shi Shikenan Sai ta Zauna da
shi a hakan🤷🏾♂️.
Idan kuma akwai Wadda ba ta son Zama da shi a
hakan domin kada hakan ya takura ta ko cutar da rayuwar ta na rashin Jima'i,
toh Sai ya ce Zai Rubuta Takardan Saki ya Sake ta, sai ta je ta Auri Wadda zai
rike ta ya Rika biya Mata bukatar ta na
Jima'i da Sauran su.
haka Shari'ar Musulunci ya ce ya yi a lokacin da
ya fadi haka shikenan dabara ta rage ma mai shiga rijiya, idan kin zaɓi ki zauna da shi a hakan shikenan sai ki zauna da shi
amma kuma dole ne ki kiyaye dokokin Allah gurin kada ki Saɓawa Allah ta hanyar kallon Batsa ko ki Biyawa kanki
Bukata gurin wasa da Farjin ki ko Nonon ki ko kallon Batsa duk Haramun ne
wajibi ne ki kiyaye.
Amma ya sani Cewa Bai da lafiya Kuma Baya iya
Jima'i yanzu, sannan Bai Muku hakan ba, Wannan zalunci ne da Cutarwa Kuma Babu
Adalci ga yin hakan, Bai kamata ya yi muku hakan ba. Sabida Haka ki ji Tsoron
Allah ki Sani Cewa Za ki mutu, Akwai Kwanciyar Ƙabari, Akwai Hisabi, Akwai Tsallake Siradi, Akwai
Azabar Cikin Ƙabari, Idan ba
ki ji tsoron Allah kin tsare kanki ba Kika ce tunda Mijin ku baya Jima'i da ku
Bari ki Fara Biyawa Kanki bukata, Toh Abun da na lissafa miki kab Sai Sun same
ki, Kuma matukar za ki Fara hakan Rayuwar ki ma Sai a Hankali kuma hakan zai taɓa Lafiyar jikin ki.
Don Haka ki ji tsoron Allah idan ma ba ki Fara ba,
toh ki ji tsoron Allah kada ki Fara yi, idan Kuma kin Fara yin Hakan, toh ki ji
tsoron Allah kiyi gaggawan Tuba tun kina da Sauran Numfashi a tare da ke.
Sa'annan kuma kiyi gaggawan Sanarwar Waliyyan ku abun da yake tafiya, domin
Gyaran Aure ne wani Kunya za ki ji? ai kunyar Aikata Saɓon Allah shine yakamata ki ji, bawai Kunyar Gyara
Shari'ar Allah ne za ki ji Kunya ba, Don Haka ki Gaya musu ke kin gaji Idan ba
za iya ba kawai ya sake ki Ki je ki Gama iddar ki Kiyi Auren ki.
Amma Zaman ki a Haka Wai ki ce kina Jin Kunya ba
za ki iya Gayawa kowa ba domin a samu Hanyar Ceto ki, wannan ba hujja ba ce
Kuma idan ba ki Gaya musu an gyara ba, toh Shakka Babu duk Tsare kanki wata
Rana sai kin aikata Saɓon Allah, domin
Shekara 3 a gurin Wadda ta San Jima'i Abu ne Mai matukar wahala ta iya jure
kanta har Haka, don Haka mafita shine ki Gaya musu ke kin ga ji ya Sawwake Miki
ki je kiyi iddar ki Gama kiyi Auren ki, shine yafi dacewa. Allah ya tsare ya
Shirya. Dafatan kin gane Koh??
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.