Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayi Ya Yi Wa Budurwarsa Kayan Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah

Don Allah ina da tambaya. Wai haramun ne saurayi ya yi wa budurwarsa kayan sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam Wa Rahmatullahi Wa Barkatuhu:

Shi Ɗinkin Sallah, Haƙƙin Iyayen ki ne su Ɗinka miki kayan Sallarki da duk wasu hidimar da yakamata ace an yiwa Mace toh haƙƙin iyayenki ne su yi miki komai matukar suna da halin su yi, toh haƙƙin su ne suyi miki dolen su ne wannan.

Sabida haka Ɗinki Sallah ba haƙƙin Saurayin ki ba ne, ace ya Ɗinka miki kayan sallah ko ya yi miki Hidimar Sallah koda kuwa shi ne ya kawo kuɗin Auren ki Sadakin sa na hannun ki, toh ba haƙƙin sa ba ne ya yi hidima da duk wasu abubuwan da yakamata ayiwa Mace, wannan Haƙƙin Iyayen ki ne domin har yanzu ke ba za ki zama Matar sa ba tukuna bai da iko a kanki kamar yadda iyayen ki suke da shi a yanzu, don haka haƙƙin iyayen ki ne suyi miki komai na rayuwa wadda Mace ta ke Bukata a rayuwar ta, amma bawai Saurayin ki ba.

Yi Miki Ɗinki, bayar da Kuɗin kitso, kuɗin kwalliya, kuɗin Lalle Gyaran gashi da sauran su duk waɗannan Haƙƙoƙin iyayen ki ne suyi miki su idan suna da Halin yi, amma bawai haƙƙin Saurayin ki ba ne.

Idan an Ɗaura Auren ki da shi kin zama Matar sa, misalin ace kin zo gidan ku hutu, toh nan ne yake zama wajibi ne a kansa ya yi miki indai yana da shi, nan Kuma babu Ruwan iyayen ki da ke, ko da kuwa suna da shi ba suyi ba sai sun ga dama su yi miki, domin ba haƙƙin su ba ne a yanzu suyi miki, sabida kin zama Matar wani haƙƙin ya fita daga kansu haƙƙin sa ne ya yi miki. Sabida a yanzu da kika zama Matar sa ke kin fita daga haƙƙin iyayenki Kin koma haƙƙin sa ne ya yi miki komai na rayuwar ki dole ne ya yi idan yana da shi.

Don haka idan Saurayin da ya kawo kuɗin Auren ki, toh idan bai yi miki Hidimar Sallah, ya yi miki Ɗinki, ya ba ki Kuɗin da za ki gyara jikin ki a gyara gashin Kai ayi kitso kwalliya, ayi Lalle, da Kuɗin da za ki yi girki ko wasu hidimar Sallah ba, toh kada kiyi fushi kar ki ɓata Rai akan wannan, ko kuma ki ce wai ah haka zai iya rike ki? Ko kuɗin sabulu wannan Bai taɓa ba ki ba a Sallah balle kuɗin barka da Sallah, kiyi fushi ki tayar da jijiyar wuya kina cewa ai ba zai iya rike ki ba ko ya Aure ki, wannan Kuskure ne domin har yanzu ba ki zama Matar sa da zai iya miki Hidima irin wannan ba, Haƙƙin Iyayen ki ne suyi miki komai bawai Saurayin ki ba.

Shi kyautatawa a rayuwa yana dakyau Kuma duk Mace tana son Miji me kula da rayuwar ta gurin kyautatawa rayuwar ta komin kankantar Abu ya siyo ya ba ta, ta hanya Siya mata abubuwan da ta ke so a irin wannan lokacin, Amma ki Sani cewa fa bawai Haƙƙin sa ba ne haƙƙin iyayen ki ne suyi miki komai na rayuwar ki domin kina gaban su ne, ke ba za ki zama Matar sa ba tukuna wadda haƙƙin ki zai rataya a kansa ace dolen sa sai ya yi miki.

Kin ga daga ranar da kika zama Matar sa an Ɗaura Auren ku ko ba ki tare zuwa gidan sa ba, toh yanzu wajibi ne a kansa ya yi miki komai haƙƙin sa ne a yanzu ya yi miki domin kin fita daga haƙƙin iyayen ki kin koma haƙƙin Mijin ki.

Amma idan shi ne ya yi Ra'ayin kansa ya Ɗinka ya kawo miki bawai kene kika tambaye shi ba, sai ya Ɗinka Kayan Sallah da Kuɗin kwalliyar ki, Gyaran jikin ki komai ya haɗa ya kawo miki,  shikenan sai ki sa hannunki ki karɓa ba Haramun ba ne, ki karɓa tare da sanyawa rayuwar sa Albarka sosai koda kuwa abun da ya yi miki bai burge ki ba, wato misalin ya siyo irin masu araha ya kawo miki kin Raina abun da ya miki, toh kada ki zage shi ko ki kuce kyautar da ya yi miki ko rika gayawa ƙawayen ki wannan matsaya shi ne ku duba dan abun da ya yi min har yana Alfahari ya miki abu, kawai kin Sanya Albarka tare da nuna Godiyar ki da wadatuwar ki da jinjina masa.

Sa'annan a matsayin ki na Mace Budurwa wadda kike son Namijin da idan ya Aure ki kina son ya kyautatawa rayuwar ki ya rike ki tsakanin sa da Allah da gaskiya da Amana, wadda zai kula da rayuwar ki sosai yadda kike so, toh abun da za ki duba anan shi ne, shin da ya yi miki kayan Sallah ya kashe miki kuɗi sosai a Sallah, don Allah ki tambaye shi yayiwa Mahaifiyar sa haka? Ki sani cewa idan kin yarda saurayin ki yana miki Hidima a gidan ku, toh ko ya Aure ki ba zai iya kula da rayuwar ki irin yadda yake miki a gidan ku ba.

Sa'annan ki Sani cewa fa kema Nan gaba Uwa ce shin za ki yarda ace yau Ɗan ki bai yi miki komai ba a ranar Sallah, Amma ga shi kuɗin da zai kashewa Budurwar sa a kalla sai yafi dubu hamsin (50k) don Allah idan kin ji haka cewa Ɗan ki yayiwa budurwarsa irin wannan ke bai yi miki ba ya za ki ji a ranki? Sa'annan duk wadda zai yiwa Budurwar sa irin wannan amma ga Mahaifiyar sa 2k tak ta tambaye shi zatayi siya Lalle ko Sabulu ko man gashi ta gyara kanta ya ce mata babu, don Allah wadda yayiwa Mahaifiyar sa irin wannan ke kuma ya faranta miki ya kashe miki kuɗi Sama da 50k ko 20k kina Jin daɗi ya yi miki abun da kike so, kina ganin idan ya Aure ki zai iya rike ki ne? Wallahi karya ne idan ma ke kin ɗauka ai tunda yana Mutuwar son ki Yana kaunar ki, yana da zuciyar ya yi miki komai duk abun da kike so a rayuwar ki ai idan ya Aure ki ma hakane, wallahi kin Yaudari kanki kin cuci kanki kin Zalunci kanki. Yadda kika ga bai yiwa Mahaifiyar sa ba ya zo yana miki, toh haka idan ya Aure ki ya samu abun da yake so a jikin ki Bukatar sa ta biya, shikenan ba zai taɓa kyautatawa rayuwar ki sosai kamar irin yadda yake miki a lokacin da kike gidan ku ba.

Saurayi yayiwa Budurwar sa kayan Sallah ba Haramun ba ne abu ne me kyau kamar yadda nace a sama, Amma haƙƙin iyayen ki ne ki san da wannan, kin ga idan misalin an ba shi ke zai Aure ki, sa'annan kuma kin tabbatar da cewa yayiwa Mahaifiyar sa ɗinkin Sallah ɗin da wasu hidimar,  toh babu laifi idan ya yi miki kema ki sa Hannu ki karɓa kiyi masa fatan Alkhairi a rayuwar sa, duk da dai shi ma bawai wajibi ne yayiwa Mahaifiyar sa ba domin itama haƙƙin Mahaifin sa ne ya yi mata, toh amma ai tunda sun haihu, ai yakamata itama ta samu ace Ɗan ta ya yi mata.

Amma idan har ba'a ba shi ke ba, Ma'ana ba'a ma San sa a gidan ku ba kawai kuna chatting ne da shi ko kuma Kuna Haɗuwa akan Hanya ne kuyi Hirar ku ba wadda ya sani, sa'annan bai yiwa Mahaifiyar sa ɗinki ba, toh ke kanki Budurwa idan kin San me kike yi Idan an kawo miki irin wannan kayan ba za ki taɓa karɓa ba, matukar kin san wacece ke a rayuwar ki.

Sa'annan Ko da ma ace shi zai Aure ki, ba zai miki kayan Sallah ba domin har yanzu kina gaban iyayen ki ne haƙƙin iyayen ki suyi miki komai, toh idan ko ya yi ya kawo miki kina iya tambayar sa ka yiwa Mahaifiyar ka? idan ya ce eh shikenan kina iya karɓa idan ya ce a'a ki ce ba ki so ko zai mutu ki bar sa da kayan sa ya Koma ya je ya fara yiwa Mahaifiyar sa tukuna, domin sune suka fi Cancanta da ya yi su a yanzu bawai ke ba.

Yayiwa Mace kayan Sallah ba shi yake nuna cewa saurayin ki na matukar son ki yana kaunar ki yana ji da ke, damuwar ki ko matsalolin ki kab yana kawar ki da su, ko hakan na nuna zai iya kula da ke a rayuwar ki, hasalima wannan shi yake nuna cewa ya mayar da ke Mai kwaɗayi ce, kamata ya yi ace kin ƙi karɓa, amma ya je yayiwa Mahaifiyar sa yafi akan ya yi Miki.

Idan shi Saurayin ya San me yake yi wallahi daga lokacin da kika ce masa ba ki son abun hannun sa dalilin cewa kin ce dole sai yayiwa iyayen sa idan ma yana son ya yi miki sai ya miki sai ya yi daga baya, toh zai ji kin Kara shiga zuciyar sa ya gane cewa ai ke ɗin ta musamman ce kina son sa da Rahmar Allah tunda har kina nuna masa hanyar da yafi dacewa tun yanzu, amma idan ke kawai matsalar ki ayi miki ne babu Ruwan ki da sanin cewa yayiwa Mahaifiyar sa ne ko bai yi ba, ke ba damuwar ki ba ne tunda Yana son ki yana kaunar ki yana kula da ke ai shikenan, toh Wallahi kin yi asara, abu na farko Saurayi ba zai taɓa ganin Ƙimar ki ko Mutuncin ki ba, kullum a Yar kwaɗayi zai ɗauke ki, sa'annan idan ya samu Labarin ba shi zai Aure ki ba kin ga ba zai kashe Kuɗin sa a banza su tafi a iska ba, me tausayin ki ne zai ce ya bar ki da Allah ya domin kin Yaudare shi, Kuma ko kin yi Aure sai kin gagara samun zaman lafiya a gidan Mijin ki dalilin wannan, wadda baya Tausayin ki shine zai neme ki ta kowane hanyar ne dole sai ya yi Zina da ke domin ya fance Kuɗin sa da yake kashe miki kullum ya ce ai ba zai yi aikin Banza ba, shiyasa wasu Yan Mata idan za suyi Aure kafin a Kai su gidan Miji sai sun je gurin tsohon saurayin su ya yi duk abun da yake so da su tukuna wai sun sallami juna yanzu ayi Zina da ke.

Abu na biyu shi ne indai Namiji yana ba ki Abu kina karɓa toh Mutuncin ki Ƙimar ki da Martaban ki kab suna zubewa a idon sa, sa'annan idan mutumin Banza ne dalilin kayan sa da kike karɓa ya samu hanyar da zai yi Zina da ke a sawwake kenan, domin duk lokacin da ya ce zai rabu da ke idan ba ki ba shi kanki ba ke gani za ki yi duk irin nuna kulawar sa a kanki duk wahalar da yake Sha a kanki ai idan kin yi masa haka ba kiyi masa Adalci ba, sa'annan ya ce ai Auren ki zai yi mene ne a gurin don kin ba shi kanki? shikenan kina sake jikin ki ya yi Zina da ke ya yi tafiyar sa kuɗin sa da ya kashe miki ya fitar da su domin ya lalata Budurcin ki, ba zai Aure ki ba ya tafi ya bar ki har abada, idan ma ya dawo toh sai dai idan zai ce ki sake cewa ki ba shi kanki ya yi Zina da ke.

Sabida haka Yan Mata a ji tsoron Allah ku Rika cire kwaɗayin ku akan komai na hannun saurayin ki komai ma, idan ya Aure ki wannan dole ne ya yi miki, haka iyayen Yan Mata ku dena cewa wai idan Saurayin Yar ki bai yi mata Hidima ba, ku Rika Zagin Yar ku kuna Zagin wadda yake neman ta ai bai da zuciya bai damu da ke ba a haka zai Aure ki ya rike ki, ki Rika cewa Yar ke ba ki ga yadda Samarin ƙawayen ki suke kashewa ƙawayen ki kuɗi ba? amma wannan matsaya shi ne bai da zuciyar yi, suyi ta Zagin sa ana kutse shi Iyaye wannan Kuskure ne wallahi, yana ɗaya daga cikin abun da ya sa ake yin Zina da Yar ki ke ba ki Sani ba, don haka ko Yar ki an kawo mata irin wannan kamata ya yi ace kin hana ta karɓa, kin yi mata fada sosai ki nuna Ɓacin ran ki over, kada ta sake aikata irin wannan Kuskuren na karɓan Abu a hannun Namiji, amma bawai kene za ki ce wai ki ce ayi miki, ko kuma meyasa bai yi miki ba ke ba za ki yi masa magana ba wannan Kuskure ne Iyaye. Dafatan Kin gane ko???? Allah ya tsare mu ya kare mu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments