𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mlm Don Allah sau nawa Miji ya kamata ya sadu da matar sa, kullum ne ko kuma yaya abin yake domin ina samun matsala da miji na? Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi Wa Barkatuhu;
Toh Malamai Sun Yi Saɓani Akan Wannan Maganar. Akwai Maganganun Malamai Har
Guda (4)
1. Abu Hanifa Allah Ya Kara Yarda Gare Shi Yana
Cewa Jima'i Hakkin Namiji Ne, Mace Tana da Hakkin Jima'i a Wajen Mijin ta ne a
Rayuwar ta Sau 1 tak a Shekara, Sauran Kuma duk Hakkin Namiji ne, Idan Ya Ga
Dama Ya Sadu da ita, Idan ya Ga Dama ya Bar ta a Haka. Amma Kuma Ya ce Namiji
ya yi Abin da Ya Dace, ya yi Abin da Zai Yi Domin Zaman Auren Su ya yi Ƙyau ya yi Ɗaɗi. Abin da Yake Nufi Shine Idan Mijin Ki Ya Sadu da ke
Sau Ɗaya a Shekara, toh Ya
Sauke Hakkin ki, Sauran Nashi Ne Idan Ya Ga Dama Ya Sadu da ke Idan ya ga Dama
Ya Bar ki. Amma Kuma ya yi Adalci ya yi Abin da ya ga Zai iya yin sa Domin
faranta miki Rai domin Auren ku ya Samun Zaman Lafiya mai dawwama da jin daɗi.
2. Imamul Shafi'i, Allah Ya Kara Yarda Gare Shi Ya
ce Bai Zama Wajibi a Tilastawa Miji Wai Ya Sadu da Matar sa ba, Ya ce Domin
Kamar Misalin ne Mutum Ya Gina Gidan Haya ga Ɗakuna Masu Ƙyau Idan Ya ga Dama ya Sa Masu Haya a Ɗakunan, Idan Ya ga Dama Kuma Ya Bar Ɗaukunan a Haka ba Tare
da Ya Sa kowa ba Tunda Mallakin Sa ne. Ya ce toh Haka Misalin Mace da Mijin ta
Yake Idan ya ga Dama Ya Sadu da ke idan ya ga Dama ya bar ki. Amma Kuma Shima Ya
ce Namiji ya yi Abin da ya ga Zai iya yin sa Domin Samun Zaman Lafiya mai Ɗaurewa a Zamantakewar
Auren Su tsakanin Sa da Matar shi, kenan dole ne idan Miji yana son Jin daɗi a gidan sa to fa dolen sa ya kasance cewa yana yiwa
Matar sa abun da take so.
3. Imam Malik, Allah Ya Kara Yarda Gare Shi, Yana
Cewa Namiji Yanada Hakkin Ya Sadu da Matar Sa a Kowanne Bayan Ƙwana (4) Sau 1 Tak, ya
ce Domin Allah Ya ce Ayi Mata 4 ne, Saboda haka Hakki ne Akan Namiji Duk Bayan Ƙwana 4 ya yi Jima'i da
Matar Sa. Idan Matan Shi Uku ne, toh Duk Bayan Ƙwana Uku ya Sadu da Mace 1. Sa'annan Shima Yana
Cewa Abin da Ya Dace Shine Namiji ya yi Abin da Ya ga Zai Iya Yin sa Domin
Auren Su ya Ɗaure a Samu
Zaman Lafiya. Kin ga wannan Mazahbin Imam Malik Ya gama bayanin komai duk yadda
ta Kai ga cewa Mace tana da bukatun ta na son Jima'i indai za ta rika samu a
duk waɗannan kwanakin tare da kulawar Mijin ta toh ya yi ba za
ta daga Hankalin ta har abun ya dame ta ba, amma idan sabanin haka ne dole ne
ake Samun matsaloli sosai.
4. A Mazahbin Hanabila, Allah Ya kara Yarda Gare
Su, Suka Ce Mace Tanada Hakkin Saduwa akan Mijin ta Sau 1 Tak a Duk Bayan Wata
4, su ma dai irin na Imam Malik ne. Kenan Kowanne Bayan Wata 4 ne Zai Kusanci
Matar Shi da Jima'i. Shima dai Abin da Yake Faɗi da ya Gama Bayanin Ya ce Namiji ya yi Abin da ya ga Zai
Iya Yin sa Domin Kada a Samu Matsala a Zamantakewar Auren Su, Ya Sadu da ita
daidai Yadda Zai iya.
Saboda Haka Ba Dole Ba ne Cewa a Dukkan Dare ko
Rana Sai Mijin Ki Ya Sadu dake Ba, masana ma sun ce Yawan saduwa da Mace a
kullum Karfin sa na raguwa duk wasu gabobin jikin sa suna samun matsala sosai
ba zai yi lasting ba. Sabida haka Idan Har Mijin ki Yana Iya Kokarin Sa Wajen Sauke
Hakkin Ki na Jima'i Yadda Ya Kamata, Shikenan Sai Ki Dage da Addu'a Allah ya
kara Muku Zaman Lafiya. Amma Ki Sani Cewa ba Dole Ba ne Cewa Kullum Sai Ya Neme
Ki da Jima'i Kamar Yadda Waɗannan Maluman
Suka Ce. Amma Shi Kuma ya yi Adalci akan ki Kada Ya Cutar da ke ya yi Yawa
Sosai, Ace Misali Ya Daina Kusantar Ki Ƙwata-ƙwata, toh Bai Ƙyauta ba Bai Yi Amfani
da Maganar Maluman Nan ba idan Bai Sani ba Auren Sa Zai iya Mutuwa akan Haka.
Sa'annan Mata Kuke Yiwa Mazajen Ku Adalci, Adalcin
Shine Kada Ku Rika Sa Su Cewa Lallai Dukkan Dare Ko Rana Sai ya yi Jima'i dake,
a Zahirin Gaskiya Hakan Yana Cutar da Lafiyar Namji Sosai Likito Sun Tabbatar
da Hakan. Rashin Karfin Jiki, Rashin Kuzari, Rashin Karfin Gaɓoɓin Jiki Sa'annan
Rashin Biya Miki Ɓuƙatar ki a Lokacin
Jima'in. Saboda Haka Idan Har Yana Yin Jima'i da ke daidai Biyan Ɓuƙatar ki Kina Gamsuwa da hakan Shima Haka, Shikenan
Sai a Ɗan Rage a Wasu Ƙwanakin Hakan Zai Sa
Shima Ya Kara Lafiya Sosai.
Sa'annan Maza dayawa suna kuntatawa rayuwar mãtan
su wadda hakan ne yake sa a yanzu wallahi ko kaffara babu matan Aure da suke
fita suyi Zina ko Madigo Allah ne kaɗai ya san iya
Yawan su, sabida kai Namiji wai Ka tafi yin kasuwancinka ka fi wata nawa ba ka
gida? Kana can ma babu irin kalaman Soyayya ko text na Farin ciki ko Jin daɗi gare ta sai ka fi sati ba ka kira Matar ka ba, wani ma
da ya kira ta Ina kwana lafiya ya Yara? Shikenan sai ya kashe wayar sa, bai
dawo gida akan lokaci ba yafi wata 6, babu kalaman Soyayya babu nuna kulawar sa
damuwar mãtan sa ba nashi ba ne kasuwancin sa shi ne a gaban sa Matar sa ba
komai ba ne a gurin sa.
Wai ka ji mutum yana haɗa Matar sa ta Sunnah ta matan kudu waɗanda su suna da Auren fita suke zuwa suyi duk abun da
suke so na rayuwar su a neme su da Zina ayi komai da su Mazãjen su ko a jikin
su, wai sai mutum ya ce shiyasa mãtan kudu suka fi ku! Wallahi mãtan Aure
dayawa a yanzu Zinar da suke aikatawa da Madigo Allah ne kaɗai ya San iya Yawan su dalilin kawai irin yadda Mazãjen
su suke kuntatawa rayuwar su. Maza wallahi a ji tsoron Allah za ka je gaban
Allah a ɗaure abun da zai kwance ka fa shi ne ayi Bincike a samu
kayi Adalci akan iyalan ka ka kyautata musu toh ka tsira wallahi, saɓanin haka a dalilin ka Matar ka ta fada halaka na Zina da
Madigo wallahi za ka je kayiwa Allah bayani. Allah ya shirya ya tsare. Fatan
Kin Gane Ko???
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.