Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijin Mahaifiyata Ya Yi Zina Da Ni

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam ygd ya kokari. Malam dan Allah ina neman shawara akan wannan matsalar. Mahaifina ne Allah ya baiwa mahaifiyata miji ta yi aure mu biyu ta haifa da babanmu nida ƙanena malam sati ɗaya kenan da mijinta yazomin cikin dare ya bani wasu ruwa nasha daganan na kasa ko magana sai kawai ya fara amfani dani (Zina) nakasa yadda zanyi in faɗawa mahaifiyana don bansan ta ina zan fara bayani ba toh malam abjn bai tsaya ba don ya sake dawo min, nidai bawai na yanke Shawarar komawa inda kakata amma mahaifiyata na nunamin ra'ayin zama damu kusa da ita, na mata uzurin saurarenta don batasan abunda ya faru dani ba, malam banason in kashe mata aure shin zan iya bijirewa ince sai inda kakata zan zauna koda rayuwarta za ta ɓaci karin tashin hankalin shine watan 12 zanyi aure narasa ya zanyi ko zan faɗawa wanda zan aura idan zai iya aurena ahaka?  Shawara don Allah malam ina neman mafita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam: Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'uun Subhalallah toh Abin da ya Dace Za Kiyi Shine, Kada Ki Gayawa ita Mahaifiyar Ki, Kuma Kada Ki Gayawa Shi Wadda Zai Aure Ki.

Dalilin Haka Shine, Ba Ki da Wani Shaida idan Kin Gayawa ita Mahaifiyar Ki Wannan Labarin da ya Faru da ke a yanzu. Sa'annan Shi ma Mijin Mahaifiyar ki ɗin ma Zai iya Karyatawa Cewa Shi bai Aikata Hakan da ke ba. Ɗan Adam Sai Allah. Sabida haka Ke Ce Za Ki Ƙwana a Ciki kenan.

Sa'annan Idan Kin Gayawa Wanda Zai Aure Ki, Shi ma dai ba Maslaha ba Ce Gaya Masa, Domin Zai iya Fasa Auren Ki Kuma Yake Yawo da Sunan Ki Cewa ga Abun da Kika Aikata. Sabida haka Kawai Shawara Anan Shine Ki Haɗa Yanaki-danaki Ki Koma Can Gidan Kakar Ki Ɗin, Koda Kuwa ita Mahaifiyar Ki ta ce Wani Abu akan Komawar ki can Ɗin. Ki Nuna mata Cewar Hakan da Za Kiyi Shine Abun da Zai Sa Ki Samu Natsuwa da ita kanta. Indai Kika Gaya mata Haka In sha Allahu Na Sani za ta Ce da ke, Ko Akwai Wani Abu Ne?? Sai Ki Ce da ita babu Komai. Idan Kika yi mata Haka, In sha Allahu za ta Bar Ki Ki Koma Can Gidan Kakar Ki.

Domin tunanin ta Zai bata Cewar Lallai Akwai Wani Abun da yake Damun ki, Sai dai Kuma ba za ta Matsa Miki Akan Sai ta San Mene ne ba. In sha Allahu za ta Barwa Allah ne Kawai. Duk da Cewar Na san itama tana Son Zama da ke a Kusa da ita kema haka, Sabida Tarbiyyan ki da Sauran Su. Allah ya tsare ki da Faɗawa Halaka da Kuma Sauran Matan Musulmai Akan Mugayen Mutanen Banza.

Sai dai idan kina da Hujjojin ki toh ko domin ceton rayuwar Mahaifiyar ki toh gara ki fito Fili ki sanar da ita ta hanyar hujjojin ki da kike da su, domin za ta yiyu wannan aikin sa ne Yin Zina kin ga kenan aje aje zai iya ɗauko Ciwo ya sawa Mahaifiyar ki, kin ga kenan ga Auren su ya mutu akan ta ci gaba da zama da Mazinaci ma ci yin Amana wadda bai San me yake yi ba a rayuwar sa.

Sa'annan yanzu kin ga kada Ciki ya shige ki Mahaifiyar ki da mutane da wadda zai Aure ki su fara Zargin ke Yar Iska ce Zina kike yi da Maza alhalin wannan banzan ne ya lalata rayuwar ki, kin ga koda ace gayawa Mahaifiyar ki zai sa Auren ya mutu toh gara kin gaya mata in ya so Auren ya mutu, wannan wacce irin rayuwa ce don Allah? sabida haka abun da za ki yi kenan Mazinaci sai Yar uwar sa Mazinaciya, sa'annan babu wani zaman Aure ma ga irin wannan Mijin da zai yi Zina da Yar Matar sa.

NASIHA Zuwa Gare Ku Maza Waɗanda Suke Tare da Agwalolin Matayen Su a Cikin Gidajen Su, Wallahi Wallahi Wallahi Ku Ji Tsoron Allah, Ku Ji Tsoron Haɗuwa da Azabar Ubangijin Ku a Ranan Alkiyama ko Kuma daga anan Duniyar, ranar da Allah zai bayyana duk wasu abubuwan da ka aikata Al'umman duniya da Mala'ikun Allah da Jinnu duk suna ganin ka shi ne ranar Alƙimaya, Ku Dena Yin Zina da Ɗiyar Matayen Ku Agwala, Ka Sani Cewa Zina Kayi, Sa'annan Hukuncin Zina ne a Kanka ko ba ka so, Shi ne a Jefa ka har Sai Ka Mutu. Shin Yanzu Idan Ɗiyar Ka Ce, sai Ka Saki Mahaifiyar ta Wani Namijin ya Aure ta, Sai ta Tafi da ita Gidan Mijin ta, Sai Ɗiyar naka ta Girma ta Dawo Budurwa a gaban wannan Mijin, Sai Mijin Wannan tsohuwar Matar naka ya Rika Yin Zina da ita, don Allah yaya Za ka Ji a Rayuwar ka?

Maza Mene ne Kuke nema a Duniyar nan ne da Babu Kunya, babu Tsoron Allah, babu Tunawa da Mutuwa, wai Har za ka iya Saduwa da Mahaifiyar Yarinya, Sa'annan ko kunya babu kuma Ka Juya Kayi Zina da Ɗiyar ta? Wannan Wacce irin Rayuwar Ce haka na Zalunci da cin Amana? Wannan Wacce Irin Masifa Ce? Ka Sani Cewa Kamar Yadda Ɗiyar Ka Mace Budurwa Wanda Ka Haifa na Jinin ka yadda ta ke a Wajen ka, Wadda Kai Kana Ganin ba Za ka Iya Zina da Ɗiyar ka ba, haka nan itama Wannan agwalan naka ta ke a Wajen ka, Domin ka Auri Mahaifiyar ta Kuma kana tare da ita Babu Aure ma a tsakanin ku tunda ka Auri Mahaifiyar ta har kayi Jima'i da ita, kenan babu wani alaka da zai shiga tsakanin ka da Yar ta domin Yar ka ce yanzu.

Allah ya haramta yin Aure tsakanin ka da ita amma sai kuma ga shi Kai Zina ma kayi da ita Inna lillahi Wa inna Ilaihi Rajee'un wannan wacce irin rayuwa ce ta dabbanci?, Shin ka Lalata Budurcin ta, ka Lalata Rayuwar ta, Ka Watsar da duk Tunanin ta Farin cikin ki komai nata ka wargaza shi, Shin kana Ganin Cewa Allah Zai bar Ka Ne? Shin kana Ganin Cewa kaima idan Kana da Ɗiya Mace Allah ba Zai yi Sakamako a Kanta ba ne?

Maza mene ne wanne daɗi za ka ji a zuciyar ka? ko min daɗin da za ka ji fa wallahi Azabar ƙabarin ka kaɗai masifa ce wadda ba za ka iya ɗaukar sa ba, Yar ka kayi Zina da ita sabida son zuciya da mugunta da Zalunci, wallahi Allah ba zai bar ka ba. Wajibi ne gare ku Maza Masu Irin Waɗannan mummunar Ɗabi'ar Wallahi ku Ji Tsoron Allha, Ku Ji Tsoron Haɗuwa da Azabar Ubangijin ku, Ku yi Gaggawan tuba daga Wannan Mummunar Aikin na Zina da Ɗiyar ku.

Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi yana Cewa, Shin Idan Kayi Zina da Matar Wani Kai Kana Son ayi da Naka Matar ne? Ka Sani Cewa ita Wanda kayi Zina da ita, ai Matar Wani ne nan Gaba, Ya ce Shin Za ka Iya Zina da Mahaifiyar Wani? ya ce Ka Sani Cewa ita Wanda Kayi Zina da Ita fa, Nan gaba itama Mahaifiyar Wani ne, Ya ce Shin Za ka Iya yin Zina da Ɗiyar Ka Yar ka Wadda ka Haifa kayi Zina da ita ta cire ma Tsiraicin Jikin ta kayi Zina da ita shin za ka iya yin hakan? Ya ce Ka Sani Cewa ita Wanda Kake yin Zina da ita Ɗiyar Wani ne, Shin idan Kaine akayiwa Haka za ka Ji Ɗaɗin Haka? idar yar uwar ka ce zai ka za ka iya yin Zina da ita ta zauna a gaban ka ta Buɗe ma Tsiraicin ta kayi Zina da ita? haba maza Ina zamu sa kan mu?

Ku ji Tsoron Allah, Ku tuɓa Ku ɗena Lalata Rayuwar ƴan Mata idan Sun taso, yin Haka Ba Karamin Zunubi ba ne da Azaba ba ne wadda kuke ɗaukar kanku, daga yin Shirka zuwa ga Allah, toh babu Wani Bala'i da Masifa da ya kai na Yin Zina, Zinar ma wai da Yar ka haba don Allah, duk Wani Abun da ba ka Son ayiwa Naka, toh wajibi ne ka Kiyaye yin sa ga wasu Sai ka Zauna Lafiya. Allah muke roka ya Shiyi Masu Lalata Rayuwar ƴan Mata da Matan Aure da Kananan Yara Ameen.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments