Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Sanda Mijina Yake Dakina Sai Ya Dauko Katifa Na Amaryarsa Ya Kwanta A Falona

DUK SANDA MIJINA YAKE ƊAKINA SAI YA ƊAUKO KATIFA NA AMARYARSA YA KWANTA A FALONA:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum don Allah wacce shawara za'a bani, mun kasance mu biyu, ni ce uwargida ina da yara uku, ina da kwalliya gayu tsafta amma duk sanda mijina yake ɗakina sai ya ɗauko katifa da bargo na amaryarsa ya kwanta a falona, da Safe yana tashi sai yakoma can ya yi wanka ya karya ya ɗauki matarsa ya kaita inda take koyarwa, baya ɗaukata machine sai ita, komai nasa yana can,bnayi masa nasiha ya ce haka yaga dama, kuma ba laifi yayiba, idan zan zauna ahaka idan ba zan iyaba ya sakeni, nazamar masa bala'i baya zama aɗakina bare ya yi hira dani kullum yana can, shin da gaskene bani da hakki ko kuwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:-

Toh a Zahirin Gaskiya dai shine ɗayan Biyu ne, ko akwai wani abun da kike masa ya ƙi ya sanar da ke laifin ki domin ki gyara, ko kuma akwai wani abu da Kika taɓa Yi Masa ya ɓoye ya Ƙi ya Gaya Miki domin ki gyara kuskuren ki, Domin na San Cewa a Lokacin da kike Amarya ai ba Haka yake Miki ba.

Kuma shi zaman ya kamata idan kin Kuskura Miji ya fito ya gaya miki cewa abun da kika yi Rana kaza bai yi masa daɗi ba amma don Allah ki gyara, shikenan sai ki gyara idan ba ki gyara ba ne toh wannan laifin ki ne idan ya yi abu domin ya hore ki, ki gane Kuskuren ki da kanki ki gyara shikenan yayi, sa'annan ke kanki zai iya Yi miki Abu ki ce abban wane ka min abu kuma ban ji daɗin sa ba Shima sai ya ce in Sha Allah zai gyara shikenan haka rayuwar Auren yake, amma indai dai ba abun da kika yi masa kawai don ya samu Amarya Yana ganin komai Sabo ne a gurin sa komai masu Kamshi ne sa'annan domin a kuntatawa rayuwar ki har Amaryar ta Raina ki, toh wannan bai yiwa kansa Adalci ba kuma shi da kansa yake son ya kawo fitina da Masifa a cikin gidan sa.

Don Haka kenan wata kila akwai wani Abun da dai da Kika Masa Bai Gaya Miki ba ya ɓoye miki. Ko Kuma ita Abokiyar Zaman ki, ta shirya Masa magana kissa irin naku na Mata, shi Kuma ya hau Kai ya zauna ba tare da ya yi binciken Shin Haka  bayanin yake ko bahaka ba? wata kila shiyasa ya ɗauki Matakin Cutar da ke da Rashin Adalci. Ko Kuma ita Abokiyar Zaman naki tayi masa Asiri ta yadda a yanzu zai Dena kula ki ko yin Mu'alamar Aure da ke, da Sauran su don Haka duk wannan Al'amarin zai iya faruwa domin ku mata Sai Allah kawai.

A Gefen Sihiri da Gefen haɗa guri da iya Gulma cin zarafin ɗayanku Duk wasu Matan Suna aikatawa a gurin Mazan su domin biyan bukatan su. amma idan babu Ruwan ta kawai dai ra'ayin sa ne hakan toh gaskiya wannan Zalunci ne babu Adalci anan, Bai yi Amfani da abun da Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam suka ce ba cewa ku zauna da su da kyautatawa tare da yin Adalci a tsakanin su.

Sabida Haka ki sani Cewa abun da yake Miki a Shari'ar Musulunci wato a Shari'ar Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Suka Hukunta, abun da yake miki Zalunci ne da Rashin Adalci da Cutarwa da Sanya bakin Ciki a Cikin Zuciyar ki wannan Babu Adalci a Lamarin sa. Ko da wani laifin Kika masa yakamata ya Gaya Miki domin ki gyara Amma bawai ya yi ta miki horo da irin nashi tunanin ba in ma zai Miki horon yakamata ya yi sa ba tare da kayan Amaryar sa ba ko zuwa gurin ta ya yi wanka ba domin irin haka shi ne yake sa ita Amarya ta raina uwar gidan sa ita Uwar gidan Kuma ta gagara hakuri tayi abun da hankalin ta ya bata karshe shi kansa sai zaman gidan sa ya gagare shi.

Sa'annan shi Addinin Musulunci Babu inda ya ce a Cutar da wani, Haka zalika Addinin Musulunci Babu inda ya ce a Zalunci wani, Sa'annan Addinin Musulunci Babu inda ya ce a Fifita Amaryar a bar Uwar gida ko oho ko Kuma a Fifita, Uwargida a bar Amaryar, wannan laifi ne Babba domin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce duk Namijin da bai yin Adalci a tsakanin Matayen sa 2 ko 3 ko 4 ba, Miji Yana Cutar da 1 Matar sa, Yana Tauye Haƙƙin ɗayan Yana zaluntar ta Yana cin zarafin ta Bai Sauke duk wani Haƙƙin Allah da ya ɗaura masa a kanta, toh a Ranar Alkiyama Lallai Yana tare da Azabar Allah Mai tsanani da radadi, matukar ita wannan Matar Bata yafe masa ba, wallahi a Filin Hisabi Dalilin hakan zai shiga Wutar Jahamnama.

Sa'annan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Mana a Ranar Alkiyama zai tashi ɓarin Jikin sa gefe ɗaya a Sanye, a Haka zai Yi ta ja har Zuwa Filin Hisabi, wannan Sanyewar jikin itama Azaba ce.

Kuma a Ranar Alkiyama Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shine Lauyan Mata, Kin ga Kenan idan ma Yana ganin hakan ba laifi ba ne shi ya isa da gidan sa haka ya ga damar yi, toh ga Hukuncin Allah sai ki duba ki gani hakan da yake miki Zalunci ne ko Kuma ke ba ki da Haƙƙi a kansa ne a Matsayin ki na Matar sa? Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce shine Lauyan Mata a ranar Alkiyama kin ga kenan Babu wadda zai tsira indai ba ya yin Adalci ga matan sa biyu Kai ko guda 1 ne, don Haka ya koma yin Adalci a tsakanin ku ya chanja Halin sa ya koma yin Adalci a tsakanin ku, idan ko ba zai iya ba toh akan ya rika Tarawa kansa Zunubi da Bala'i Wadda zai sa shi ya Shiga Wuta, toh wallahi gara ya Sake ki ya zauna da Mata 1 yin hakan yafi Alkhairy gare shi akan ya ci gaba da Zama da ke Yana Cutar da ke, domin ai Allah ma ya ce idan zaku yi Adalci toh Ku Auri 2 zuwa 3, ko 4, ya ce idan ba zakuyi Adalci ba toh ku tsaya 1.

Shin Adalci yake Miki a hakan? Abu na Farko idan kin Yi Masa Nasiha ya Ƙi ya Chanja Halin sa ki gayawa Waliyyan ku ki je ki samu Waliyyin sa ki sanar da shi, idan sun Yi sun gagara toh idan kina son sa a hakan sai ki ci gaba da Zama da shi idan koh ba ki son Zama da shi domin kada aje aje ki koma Saɓawa Allah, toh kina da zaɓi Sai ya sake ki kowa ya je Allah ya haɗa shi da Rabon sa, idan Kuma za ki iya jurewa sai kiyi hakuri ki danne zuciyar ki ki bar sa da halin Allah yana ganin ku Allah ya San me gaskiya a tsakanin ku kuma Allah yana tare da masu hakuri kenan ba za ki taɓa tabewa ba In Sha Allah.

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam kafin ya bar duniya kafin Allah ya ɗauki rayuwar sa wasiyar da yake bayarwa ga Al'umman duniya masu Mata shi ne, ya ce ku tausayawa Matayen ku, ku zauna da su cikin aminci da amana, ku kyautatawa rayuwar su kada ku kuntata musu, Wasiya fa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya bayar Kuma yanzu sai Namiji ya rude Ido ya ce ai gidan sa ne ganin damar sa ya yi duk abun yake so kuma wai a hakan yana son ya mutu ya shiga Aljannah bayan ya Saɓawa abun da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, Maza a ji tsoron Allah wallahi, sa'annan kema ki zauna ki bincika kanki me kika yi masa? idan babu ki tambaye sa ko akwai Kuskuren da kika yi masa ke ba ki Sani ba don Allah ya gaya miki sai ki gyara, idan ya gaya miki sai ki gyara halin idan ya ƙi sai ki sanarwa Waliyyin sa a haɗa ku a ji meyasa yake miki Hakan? Allah ya tsare ya Shirya. Dafatan kin gane Koh?

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments