Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yanke Wa Barawon Hannu Da Hukuncin Kashe Barawo

HUKUNCIN YANKA WA ƁARAWON HANNU

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam, wani al'amari ne ya damemu a garinmu. Muna da ɓarayi sosai 'yan rainin hankali saboda goyon baya da suke samu daga wurin wasu mutane. Idan an kama ɓarawo an kaishi wurin hukuma wani lokacin ko kwana uku baza ayi ba, zaka ganshi sun sakeshi ya dawo gari yana cigaba da sha'aninsa. Shi yasa mu matasan unguwarmu muka yanke shawarar cewa duk ɓarawon da muka kama zamu yi masa tsinannen duka, ko kuma mu yanke masa hannu ko kafa, ko kunnuwansa ko wani waje a jikinsa. Shin idan munyi hakan babu laifi, tunda dukiyoyinmu suke sacewa kuma mukan kamasu da abun ahannunsu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Da farko dai ina yi maka nasiha tare da ni kaina da dukkan Musulmai cewa Wajibinmu ne muji tsoron Allah afili da ɓoye, kuma mu kiyaye dokokinsa koda sunci karo da son zuciyarmu.

Hakika Allah shi yayi umurni cewa ayanke hannun ɓarawo acikin Suratul Ma'idah (ayah ta 38). Allah yace :

وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُوا أَيْدِيَهُمَا جَزَاءً بِمَا كَسَبَا نَكَالًا مِّنَ اللَّهِ وَاللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

"DA ƁARAWO DA ƁARAUNIYA KU YANKE HANNAYENSU. WANNAN SAKAMAKO NE BISA ABINDA SUKA AIKATA, (KUMA) AZABA CE DAGA ALLAH. HAKIKA ALLAH MABUWAYI NE (CIKIN AYYUKANSA), MAI HIKIMA NE (CIKIN HUKUNCINSA)".

To amma fa ba'a bada damar cewa kowanne mutum idan ya kama kowanne ɓarawo ya zartar masa da hukunci shi dashi ba. A'a hukumar Musulunci kaɗai keda wannan damar. Misali kamar Alqali ko Sarkin Yanka (wanda keda matsayin Amirul Mu'uminina acikin mutanen dake karkashinsa).

Sannan kuma ba kowanne irin ɓarawo ake yanke wa hannu ba. Idan ɗan fashi ne (wato Armed robber) wannan hukuncinsa daban, idan ɗan danfara ne ko mai yankan aljihu shima hukuncinsa daban, idan kuma mai fasa gidan mutane ne ya shiga, shi ne wanda ake yanke wa hannu ɗaya, amma idan abinda ya sata ɗin yakai nisabin da shari'a ta ajiye. Misali a mazhabin Malikiyyah shi ne 'RUB'U DINAR' Wato kimar mafi karancin sadaqi kenan.

Addinin Musulunci bai bada damar mutum ya rika ɗaukar doka a hannunsa ba. Ya kamata a kula sosai kada abiye wa son rai. Duk sanda kuka kama ɓarawo ku mikashi wajen hukumar da tafi kusa daku, sannan ku tsaya akan maganar har sai kun tabbatar da anyi masa hukuncin da ya dace dashi. Idan kun tabbatar ba'a yi muku adalci ba, zaku iya ɗaukaka Qara zuwa wata kotun ko kuma ku tuntubi hukumar sauraron koke-koke ko kungiyoyinku na jama'ar gari zasu iya shiga cikin maganar domin tabbatar da adalci.

Lokaci ɗaya ne aka yarda zaka iya ɗaukar mataki akan ɓarawo. Shi ne idan ya shigo gidanka da makami kuma yana nufin kasheka ko yayi maka rauni, to zaka iya ɗaukar mataki kaima domin kare kanka ko iyalanka ko dukiyarka, kuma koda ɓarawon ya kasheka, to mutuwar shahada kayi. Idan kuma kaine ka kasheshi, to jininsa ya zuba abanza.

Mutanen dake amfani da matsayinsu ko dukiyarsa wajen goyon bayan miyagun dake aikata ɓarna acikin al'ummar musulmai, wajibi ne suji tsoron Allah su dena domin yin hakan yana Qara bunkasa ayyukan ɓarna da ta'addanci atsakanin mutane, kuma hakan babbar hanyar lalacewar zamantakewa ne.

Allah yana cewa :

...وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ

...Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.

WALLAHU A'ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

HUKUNCIN KASHE ƁARAWO:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malan barka da safiya Wai malam hukuncin kisa da ake yiwa ɓarawo idan an kama shi, ya hallata ko kuwa bai hallatta a kashe ɓarawo ba? Allah ya karawa malan sani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Bai halatta ba, saboda a Shari'a hukuncin ɓarawo shi ne a yanke masa hannu, idan ya saci nisabi daga inda ba shi da iznin shiga.

Sannan yanke hannun Ɓarawo yana hannun Hukuma, ita ce take da hakkin zartar Masa da haddi, hakan sai ya nuna abin da mutane suke Yi kuskure ne.

Idan Ɓarawo ya yi kokarin yin taaddanci aka kashe shi wajan kai ɗauki babu matsala in an kashe shi.

Allah ne Mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments