Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Maganin Kara Girman Mazakuta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam Wallahi ni ne ranan muna tare da iyali na, sai ta ce min nasha maganin da zai kara min girman azzakari na da kuma tsayin ta, hakan yasa ni na washe ta kuma har nace mata wannan zai iya saka na zargeta, amma ta yaya tasan wannan maganan? sai ta ce wai taji ana fada akwai maganin ne a radio. Gaskiya yanzu Malam na rasa yaya zanyi shiyasa nace don Allah indai akwai yadda za'ayi azzakari na ta kara tsayi da girma ka taimaka min, domin ni bani da matsalan rashin karfin azzakari sai dai gaskiya azzakari na bai wuce 9 centimeter ko kuma ince tsayin ruler karami na cikin math-set. Saboda haka don Allah Malam akwai hanyan da zanyi azzakarina ta karu? Malam kuma wanne shawara za ka bani akan wannan maganan da ta gaya min domin har yanzu banajin sha'awanta kaman da, thank you very much for your contribution. Malam don Allah ina bukatan amsar ka, domin nafi jin aminci tattare da maganganun ka da hujjoji da kake bujirowa da su. Nagode. Allah ya kara maka Imani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Gaskiya ɗan'uwa Ya kamata ka godewa Allah tunda ya baka cikakkiyar lafiya da ikon yin aure, sannan ya baka matar da ka aura, harma kuka samu daman biyan bukatunku na sha'awa.

Idan ka duba za ka ga wasu da dama suna da lafiyar jiki, amma kuma mazakutarsu batta da

cikakkiyar lafiya. Wasu kuma suna da cikakkiyar lafiyar amma Allah bai basu ikon yin auren ba, har ranar mutuwarsu. Bai kamata ka ji haushin matarka saboda ta baka wannan shawarar ba. Watakila akwai dalilin da yasa ta baka shawarar. Watakila kana da WUƘA MAI KAIFI ne, amma baka san yadda za ka yi aiki da ita ba. Don haka ya kamata kayi tunani akan wasu halattattun hanyoyin da za ka bi domin gamsar da ita ayayin da kuke Jima'i. MISALI: Kamar gabatar da wasanni, da kalamai na soyayya, da chanja position alokacin Jima'i. Duk waɗannan suna sanya Ma'aurata su samu Gamsuwa da Junansu. Kabi waɗannan shawarwarin. Kar ka wahalar da kanka wajen neman maganin Ƙarin Girman Mazakuta. Tsawon da kake dashi ayanzu ma ya isheka.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments